Bayanai a aikin Jarida: Manyan Tarukan Aikin Jaridan da ke aiki da Bayanai
Read this article in
Wadannan manyan tarukan su na iya bayar da damar haduwa da kuma ma’amala da irin mutanen da ba ko da yaushe ne za’a iya haduwa da su ba, yana iya bayar da damar koyon sabbin dabaru da kuma tattauna mahimman batutuwa da sauran ‘yan uwa ‘yan jarida.
Cibiyar binicike mai zurfi a aikin jarida ko kuma Centre for Investigative Journalism a turance na da taron da ta ke yi a lokacin bazara, summer conference inda ta kan koyar da amfani da bayanai a aikin jarida a karkashin jagorancin manyan malaman da suka shahara a wannan fannin.
Data Harvest/ Girbin Bayanai – wani taro ne da ke gudanarwa daura da babban taron ‘yan jarida masu bincike mai zurfi a Turai. Za’a gudanar da mai zuwa daga ranar 19 zuwa 22 ga watan Mayun 2022, a Mechelen da ke kasar Beljiyam.
European Data and Computational Journalism Conference/Babban taron Turai kan bayanai a aikin jarida – yana kawo ma’aikata daga masana’antan da ‘yan jarida da kuma kwararru a fanin illimi
The international Journalism Festival/Bukin ‘Yan Jarida na kasa da kasa a Perugia na kasar Italy, inda a kan hada har da makarantar koyon amfani da bayanai.
Investigative Reporters and Editors/Masu daukan rahotanni da editoci a bincike mai zurfi wanda akan yi kowace shekara na mayar da hankali ne dungun kan bayanai da bincike mai zurfi a aikin jarida
NICAR, shiri na masu daukan rahotanni da editoci masu gudanar da bincike mai zurfi kan dauki nauyin bakin babban taro kowace shekarar kan bayanai a aikin jarida da kuma koyarwa. NICAR kuma ta na da wani jaddawali ko kuma NICAR-L inda take samun shawarwari daga sauran ‘yan jarida. Tana kuma da shi a harshen Spanianci.
NODA, – Wannan babban taro ne na kasashen da ke yankin Scandanavia wanda ake kira Nordic Data Journalism a turance wanda kuma ya ke bajekolin fitattun ayyukan da suka fito yankin dangane da bayanai a aikin jarida. Wannan ya hada da labarai da hotuna da kuma lambobin yabo.