Image: Screenshot
Sabin tsarin kasuwanci ya bulla: Ga labaran dijital na hadin gwiwa
Tsokacin Edita: An fara wallafa wannan labarin ne a jaridar Non-Profit Quaterly (NPQ)– Jaridar da ke fita bayan kowani watanni uku a yanar gizo ranar 3 ga watan Maris 2021. Muna farin cikin sake wallafa mu ku shi a nan da izinin su. Duk da cewa labarin ya fi mayar da hankali kan kasuwannin Amirka ne akwai darussan da duniya za ta iya yin koyi da su. Hakika, kamar yadda labarin ya bayyana, dadaddu jaridun hadin gwiwar da masu karantawa ne ke jagora na na a kasashen Turai, da Mexico kuma sun fara samun tushe a kasashen Canada da Uruguay
Cikakken yunkurin jama’a ke nan: Rabon da dimokiraddiyarmu ta yi rauni haka tun lokacin yakin basasa, a yanzu ba wanda ya yadda da cibiyoyin gwamnati, kuma kafar samun labaran cikin gida mai cike da tarihi wanda ke karfafa jama’a – wato jaridun al’ummomi – suna ta fuskantar koma baya na tsawon shekaru fiye da goma. Kashi daya cikin hudu na jaridun Amirka sun rufe tun shekarar 2004 kuma annobar COVID-19 ta sake ta’azara wannan matsala.
Bacin yunkurin da ake yi na fadada matsalar mutuwar kamfanonin jaridun da sabbin shafukan dijital – wasu masu burin samun riba wasu kuma ba ruwansu da samun riba – adadinsu ba ya karuwa da sauri kamar yadda ake so, dan sum aye gurbin wadanda ke bata. Binciken jami’ar jihar North Carolina (UNC) ya rubuta yadda jaridun ke cigaba da bata daga iyaka zuwa iyaka.
Amma tsaya – Wani haske ne ake hange?
Shafin labarai na hadin gwiwa na farko a kasar ke kokarin fara wani salon samar da labaran a birnin Akron da ke jihar Ohio. The Devil Strip (ko kuma zirin shaidan) – wanda sunan mai jan hankali ya sami asali daga zirin ciyawan da ya raba tsakanin titin mota da ‘yar hanyar simintin da mutane ke tafiya kai a kan hanya – Na bukin cika shekara guda a matsayin ta na jaridar hadin gwiwa, tare da mambobi kusan dubu guda, kuma a cewar mawallafi Chris Horne, har ma sun gota yawan kudaden shigan da su ka yi kiyasin za su samu. Shin wannan zai iya kasancewa alamar cewa jaridun hadin gwiwan za su dore kuma zasu fadada; kuma al’ummomi za su sami karuwa daga jama’an da za su rika samun bayanai nagari wanda zai tabbatar da al’umma mai lafiya?
Tuni an fara yunkurin auna hakan a Northern Carolina, Maryland, Hartford, Connecticut, Pittsburgh, Pennsylvania, Boston, Massachusetts; Springfield Massachusetts; kauyukan Maine da sauransu. Shirin Bayan Project wanda na kafa, shi ne ya fara samar da samfurin labaran dijital na hadin gwiwa a al’umma. Hasali ma yanzu al’ummomi fiye da 40 sun tuntube mu. Kowani shiri na da banbanci: Alal misali, a Boston, burin shi ne samar da majiyar labarai mai nagarta wa al’ummar bakaken fatan da ke da yawan gaske a yankin metro.
Mene ne Labarain Hadin gwiwa ko kuma News Co-ops?
Masu rajin tabbatar da labaran al’umma na hadin gwiwa na ganin wannan salon samar da labaran da suke shiryawa na da babban daman samun nasara a wuraren da shafukan dijital ke fama da rashin karbuwa ko kuma su ke mutuwa, hatta wuraren da ma babu wata majiyar labarai baki daya. Duk da haka dai, har yanzu wannan tsarin bai gama haduwa ba kuma abin da ya ke alkawartawa ba’a riga an sami hujjar yiwuwarsa ba. Kamar kowani irin tsari ko salon a sana’a, wani abu na iya faruwa.
A yanzu haka dai masu shirya wannan tsari na hangen shi daga fannoni daban-daban:
- Masu karatu, news co-ops cibiyoyin al’umma ne wadanda ke cike gibin bukatun al’umma na labarai da bayanai – yayin da suke kuma bayar da shafukan dijital inda al’umma za ta ga irin martanonin da jama’a ke mayarwa dangane da labarai, har su ma su hada kai a yunkurin da ake yi wajen taimaka ma al’umma. Co-ops su kan shirya duk labarai da ma sauran bayanan da ake bukata kyauta kuma da kan su domin kowa ya karanta.
- Mawallafa, wannan tsarin na samar da kudaden shiga daga sayar da wani abu mai daraja – kamar damar kasancewa mamba da kuma wani kaso da damar jefa kuri’a a cibiyar da hidima mai mahimmanci kadai ta ke yi wa al’umma ba hatta bayar da murya. Kudaden da ake biya na maye gurbin kudin da ake biya wajen sayen jaridun. Ita dai news co-op burinta shi ne ta baiwa al’umma damar baiwa kansu kyakyawan fata
- Mambobi, alfunun da za su samu shi ne wani kaso na kamfanin da kuma damar zabe, amma wannan soma tabi ne. Ginshikin shi, shi ne sanin cewa yunkurinsu zai taimaka wajen samar da cibiyar da za ta tabbatar cewa kowa a al’ummar ya san batutuwan da ke da mahimmanci. Banda haka idan aka sami dandali na dijital mambobi na da damar rubuta abubuwa, sa’annan a wasikun da za’a rubuta za’a tambaye su ra’ayoyinsu da abubuwan da suka sani dangane da batu da ma wadanda suke so a wallafa kuma ta yaya za’a wallafa. Wadanda ba mambobi ba basu da wanann damar.
- Masu abin tallatawa, ma wadanda ke biyan kudi mafi yawa suna samun karin abubuwa kamar sanya sana’ansu a takardar sana’o’i dan kowa ya gani, suna samun ragi idan suna so su yi talla. Kuma ba kaman sauran shafukan intanet ba, za su san wuraren da tallansu zai fita kuma za’a yi komai da nagarta. Za’a sanar da irin alfanun da abin da ake tallatawa ke da shi ga al’umma. Idan har al’umma ta san alfanun shi tabbas zai sami ciniki.
- Al’umma, labaran za su sanar da masu ‘yancin zabe a al’ummar da duk wani abin da ya kamata su sani, kuma zai basu damar shiga a dama da su irin wanda jaridu da sauran fasahohi ba za su iya ba.
Haka nan kuma doka ta bukaci co-ops su yi jagoranci irin na dimokiradiyya, ta yadda kowani mamba na da kuri’a yin zabe na ‘yan kwamitin zartarwa wadanda za su zaba kuma su sanya ido kan ayyukan edita da babban darekta. Ana iya samun daruruwa ko dubban mambobi ya dai danganta ne da yawan al’umma. Wannan zai raba iko tsakanin mutanen al’umma ta yadda kowa zai sami murya ko kuma karfin fada a ji.
Co-op da ke aiki da kyaua kulluyaumin zai tambayi mambobi ra’ayoyin su ya kuma gayyace su wajen tattauna abubuwan da suka shafe su ko ta hanyar yanan gizo ko kuma ido da ido. Ana kuma iya horas da mutane kan aikin jarida, karatun jarida, da sauran abubuwan da suka shafi ci-gaba. Wannan zai inganta dangantakar da ke tsakanin al’umma. A zamanin da babu aminci sosai da kuma akw samun karancin dangantaka a tsakanin ‘yan al’umma hankulan mutane na komawa ga batutuwan da suka shafi sauran kasashen duniya, rawar da news co-ops na da mahimmancin gaske.
Ga dimokradiyya, akwai dama sosai na samun alfanu musamman idan wannan salon na News co-op ya dore a wuraren da salon aikin jarida na samun riba da na wanda ba ruwan su da riba ba su dore ba. A cikin jaridu fiye da 2100 da suka mutu a 2004 wadanda ake bugawa kowane rana ba su kai 100 ba yawancin su mako-mako ake bugawa. Jaridar UNC da aka ambato a sama ya sami shafuka 525 a matakin al’umma. Wannan adadin ya karu – Cibiyar labarai wadanda ba ruwansu da riba kwanan nan ya bayar da labarin yadda yawan mambobinsu ya karu – amma a daidai lokacin da wannan ke faruwa jaridu fiye da 60 suka mutu.
Co-ops na daukar suffofi daban-daban. News co-ops sun shiga rukunnai daban-daban ke nan kuma wadanda ke cin moriyarsu ke mallakarsu. Yawancin wadanda ke karantawa ne za su mallake co-ops din kamar dai yadda kungiyoyin adashe da na abinci ke yi. Irin wadannan ba su girma sosai amma kuma ana iya daukan darussa daga wurinsu. Kungiyoyin bashi ko Credit Unions misali kanana ne kuma a matsayin masana’anta, kungiyoyin bashi 5,133 da ke kasar na da mambobi milliyan 123.7 wadanda ke da kaddarar da ke da darajar trilliyan $1.79 na dallan Amurka. Wannan ya fi Wells Fargo wanda shi ne banki mafi girma a mataki na uku a Amirka, idan har News co-op suka sami shiga haka, ba karamin riba dimokiradiyya za ta yi ba.
Alfanu da rashin alfanu
To wadanne irin alfanu ne news co-op suke da shi?
Da fatan samun tallafin masu karatu, labaran dijital da suka kafu sukan nemi hanyar hulda domin su ja hankalin masu sha’awan labaran rediyo da talbijin wadanda za su tallafa mu su da kudi. Wadanda ke rajin ganin News Co-op ya habaka suna da ra’ayin cewa kasancewa mamba a irin kungiyoyin ya fi daraja – akwai daidaito, damar zabe, da kuma damar fada a ji a mahimman batutuwan da suka shafi al’umma. Idan har news co-ops suka nuna cewa irin wadannan huldodin su na da mahimmanci za su ja hankalin mambobi kuma idan har suka iya rike su yadda ya kamata, kudaden shiga za su karu. Wanann kudaden da za su samu zai taimaka wajen gudanar da shafukansu da su kansu masu gudanarwar, ko a al’ummomin da ba su da wani arziki sosai irin wadanda suka cika rayuwa babu kafar yada labarai.
Wani karin da za’a samu daga amfani da tsarin co-op din kuma shi ne sahihancin shi. Editoci da manyan darektoci suna karkashin wadanda suka mallaki kamfanin ne dan haka alhakin wadanda suka mallaki co-op din ne su sanya ido a kan editocin da sauransu kuma tunda mambobi ne suka mallaki co-op din, ya zo da sauki ke nan, su ne za su tabbatar cewa editoci da darektoci sun yi abin da al’umma ke so.
Wannan ne abin da ya sa ake ganin tsarin na da sahihanci domin abin da aikin jarida da dimokiradiyya ke bukata ke nan – sahihanci
Mene ne kalubalen wannan tsari da wuraren da ta gaza.
- Daga farko ana bukatar aiki sosai da kuma mambobin da yawa wadanda za su bayar da kudi mai tsoka wanda za’a yi jari da shi kafin a iya kaddamarwa. Wannan ya fi wahala idan aka kwatanta wanda ya riga ya tara kudi ko. To amma ban da haka, saboda yawan mambobin da akan samu wadanda suka riga suka zuba kudi kuma suna so su ga sun yi riba, da wuya kamfanin ke durkushewa. Haka nan kuma sauya kafar yada labarai na dijital ta zama mallakar al’umma ba wuya sosai, abin da Devil Strip ke yi ke nan.
- Saboda babu co-op da yawa a sana’o’i, da wuya ake samun wanda ke da kwarewa a fannin, haka nan kuma babu wadanda ke da kwarewa wajen co-op na labarai tunda salon sabo ne. Irin co-op din da aka saba na adashe da sauransu ba su cika hulda da mambobi sosai, kuma nan ne wannan ya bambamta domin shi yana bukatar mambobi. Sai dai kuma a lokaci guda editoci na bukatar yanke shawarwari a wasu fannoni domin tafiyar da komai cikin nasara.
- Mawallafa a shafukan dijital na fannonin wadanda ke riba da wadanda baruwan su da riba nan da nan ake samun shiga sai dai news co-op yana bukatar matakai da yawa domin ya kunshi neman mambobi, duba ciniki da kuma kiyaye duka abubuwan da ake yi a shafin
Mafi mahimmanci dai shi ne ba’a riga an gama gwada tsarin ba. Akron na jagora kuma yayin da ake samun masu nuna sha’awa a wurare daban-daban, wadanda suka saba sanya kudi a kafofin yada labarai na gargajiya har yanzu ba su kai hankalinsu tsarin news co-op ba.
Tsarin na samun karbuwa
Ba da dadewa news co-ops su ka fara bulla a Amurka ba, amma tun ba yau ba ake da jaridu na kasa mallakar masu karantawa a kasashe irin su Jamus, Italia, Switzerland da Mexico abin da ke nuna ma jama’a cewa mutane za su tallafawa jarida ko kafar yada labaran da za ta biya bukatunsu. A yanzu haka dai akwai sabbin news co-op da suka fara samun tushe a kasashen Canada, Uruguay, da Birtaniya. A Amurka, the Devil Strip ne na farko amma akwai wadanda suka biyo baya:
- The Devil Strip ya fara ne a matsayin jarida na wata-wata amma sai ya fara fiskantar matsala, sai shugaban kamfanin Chris Horne ya yanke shawarar mayar da shi co-op. Wannan yunkurin ya ya yi sanadiyyar tallafi daga kamfanoni 13 abin da ya kai jimilar rabin milliyan na dallan Amurka daga gidauniyar Knight da sauransu – ya kuma ja hankalin Columbia Journalism Review.
- The Mendocino Voice wannan shafin intanet ne wanda aka fara 2016, shi ma masu shi sun amince su mayar da shi co-op. A wata hira da Kate Maxwell, mai kamfanin, ta ce an riga an kammala duk wani aikin da doka ta tanada. Shi kan shi wannan shafi ya ja hankalin kamfanoni da masu aikin jarida.
- Bloc by Block, wanda ke da mazaunin shi a Baltimore na farawa daga farko ke nan domin samar da news co-op di da za ta rika samar da labarai ga al’ummomin Maryland. Kevon Paynter mai kamfanin ya ce burin kamfanin shi ne samar da labarai ta yin amfani da manhajar waya
- Civic Mind na kokarin kaddamar da wata shafin intanet mai suna Hartford Times, dan ta kasance takwarar wata jaridar da aka rika wallafawa a Hartford na tsawon shekaru 159 kafin aka dakatar a shekarar 1976. Civic Mind ta sami ‘yancin amfani da sunan a hukumance kuma mai kamfanin Thomas Clynch yana aikin kirkiro tsarin da ya dan banbanta daga wanda aka sani – yana son na shi ya kasance wand aba ruwan shi da riba kuma mai kuri’a daya da shugabanci daya.
Shirn Banyan inda na ke aiki, ba co-op ba ne amma yana taimakawa wajen samar da co-op ba tare da yin riba ba. Yana bayar da makaman aiki, da tsari da shwarwarin da za su jagoranci kungiyoyin kauyukan da ke da sha’awan fara amfani da tsarin na co-op. Daga nan Bayan sai ya bas u shafukan da ke da irin abubuwan da suke bukata domin yin nasara. Mutane a jihohi 21 sun riga sun tuntube mu dangane da fara amfani da tsarin na Banyan a yankunansu. Banyan ya sami kyautan kudi kuma yana neman wasu karin hanyoyin samun kudin na shekaru masu yawa domin ya iya daukan ma’aikata ya fara girka ofisoshin news co-op a duk wuaren da ake bukata, inda kuma akwai wadanda za su bayar da kai wajen yin aikin kyauta dan su jagoranci wannan yunkurin. A yanzu haka Banyan na aiki da Civic Mind a Hartford.
A wannan lokacin babu news co-op biyu da ke da kama. Daya ya fara a matsayin mallakar mambobi a Canada amma da ya ke babu kudi daga mambobin sai ya durkushe. Ya yi kokarin samun mambobi daga cikin wadanda ke karantawa amma nan ba ba’a yi nasara ba. Wani kuma a Ingila mai suna Bristol’s Cable ya sauya saboda ya bunkasa har ma ya kara kujeru a kwamitin gudanarwa dan “masu bayar da gudunmawa” The Devil Strip na kwaikwayon wannan tsarin ne. Tsoffin kamfanonin co-op din da aka sani a Turai da Mexico sun fara a matsayin jaridu ne kuma salon aikin su ya banbanta. Akwai abubuwa da yawa da ya kamata a koya.
Me ya sa yunkurin amfani da sabon salon ke da amfani?
Kusan ko’ina akwai gibi wajen bayar da labaran cikin gida. Dimokiradiyya ba za ta yiwu ba idan babu al’ummar da ta ke da fahimtar al’amurar da ke faruwa kewaye da ita- dan haka wannan gibin na bukatar cikewa.
Shafukan da ke yanar gizo a yanku haka, da na kudi da wadanda ba ruwansu da riba sukan cike wadansu gibin su bar wasu, binciken UNC ya nuna cewa babu daidaito a yanayin da suke bayar da labaran a tsakanin wadanda ke da karfin tattalin arziki. Akwai wadanda za’a iya ware wa, misali, shafukan da ke karban kudi sun fi samun cigaba ne a yankunan da ke da arziki. Shafukan da ba ruwansu da riba kuma sun fi tasiri a birane inda ake yawan bayar da tallafi. Sai dai bayan kwashe shekaru fiye da 10 ana yunkurin kafa su, shafukan da ake da su har yanzu sun gaza maye gurbin jaridun da suke cigaba da durkushewa bare har su shiga yankunan da ba su ma da jaridun samsam.
Akwai shafukan da suka cancanci yabo domin yadda suke aiki a yankunansu. Akwai jaridu wadanda ba ruwansu da riba da suke kawo labaran gwamnati a jihohin Texas da Vermont kuma suna aiki fiye da yadda jaridu ma su ka yi aikin a baya. Jaridun kasa da na duniya baki daya, masu bincike kuma wadanda ba ruwansu da riba musamman ProPublica da Kungiyar hadin-kan ‘yan jarida masu bincike mai zurfi wadanda ke tasanma gwamnati su kuma samu kyauta mai yawa. Wasu shafukan sun taso suna labaran manyan brianen da suka dade ba su da kafofin yada labarai a yankunan da ke kudancin Chicago. Wadannan suna matukar taimakwa dimokiradiyya.
Haka nan kuma a bangaren labarai masu dadi, Hukumar Karbar Haraji na Cikin Gida ko kuma IRS ta fara barin jaridu su sauya daga masu karban kudi zuwa wadanda ba ruwansu da riba. Jaridar Baltimore The Sun na kan hanyar yin hakan. Wannan matakin ma zai taimaka ma jaridun da suka kusan durkushewa su mike. Akwai kuma yunkurin da ake gani na samun tallafi wa kamfanonin jarida na dijital da ake da su yanzu.
Duk da haka dai akwai wuraren da ba’a samun labaran.
“Wannan ne babban kalubalen da aikin jarida ke fiskanta yau” a cewar Martin Baron wanda ya yi ritaya kwanan nan daga mukaminsa na baban darekta a jaridar The Washington Post yayin da ya ke wata hira da PBS News Hour, inda ya kara da cewa “babban barazana ce ga dimokiradiyya kanta”
Wannan lamarin na neman sabbin dabaru. A yanzu haka ana ganin cewa news co-op za ta taka rawar gani.