Accessibility Settings

color options

monochrome muted color dark

reading tools

isolation ruler

Riyoyin

Freelancing: Dandalolin da ke samarwa marubuta da kudi

Ana ganin karuwa a yawan shafukan da ke taimakon marubuta suna samun kudi a yayin da suka wallafa labaransu da kan su. Wajibi ne ku yi bincike dan tantance ko wannan abu ne da ya dace da ku.

A wannan sashen, ba za mu duba wuraren da ke taimakawa wajen kirkiro da shafi, ki wasiku ko taskokin blog ko kuma ma duba batun Plug-ins wato fasahohin da ke taimakwa wajen saye da sayarwa ko biyan kudi ba. Ba kuma zamu mu shiga batun shafukan sochiyal mediya irin su Telegram, facebook, Reddit da WhatsApp ba.

An kwatanta irin karuwan da ake samu wajen kirkiro wasikun email masu zaman kansu a cikin wani labarin da aka wallafa a jaridar New York Times a watan Satumban 2020, wani a Axios da wani na uku kuma a Medium wanda mai bayar da shawara kan kafofin yada labarai Mark Glaser ya rubuta.

A wani sashen mun tattauna hadin gwiwa ta hanyar manyan kamfanoni a intanet irin su Labaran Apple da SmartNews wadanda ‘yan jarida masu zaman kansu ba suwa samu.

Rarraba shirye-shiryen sauraro na podcast shi ma wani batun ne. Akwai shawarwari a wannan labarin, 22 Top Networks to Submit Your Podcast in 2020/ Kafofin yada labarai 22 da ya kamata ku baiwa shirin podcast din ku a 2022 wanda kwararre kan talla a Amurka Robert Katai ya rubuta.

Adadin sabbin wuraren wallafa labarai na ninka kanshi. Wannan fanni ne da ke sauyawa kullun dan haka yana da mahimmanci a yi bincike sosai kafin a yanke shawara. Wani wajen da zai taimaka shi ne Blogging Guide/Jagorar Rubutu a Blog na Casey Botticello.

Wuraren Sayar da Labarai

Medium

Wannan dandalin da aka kaddamar a shekarar 2012 ya ce yanzu mutane akalla milliyan 120 na ziyartar shafin kowani wata kuma shi ne waurin da “kowa yana da labarin da zai raba sa’anan za’a turo muku wadanda suka yi fice.”

“Idan mutun ya yi rajista zai iya bin mawallafan da ya fi so da rubuce-rubucensu. Zai iya ajiye labaransu domin ya dawo ya karanta daga baya, ya wallafa na shi tsokacin da sauransu. A cewar shafin “wallafa labarai a nan kyauta ne kuma za’a raba labarinka ga wadanda ke bin ka tare da milliyoyin masu karatu da ke sha’awan irin batun da ka yi tsokaci a kai.”

Medium na samun kudaden shiga daga kudin da ake biya. Ana biyan $5 wata-wata ko kuma $50 kowace shekara, mutun na iya zama mamba dan samunduk labaran da ke kan Medium da wasu karin abubuwa.

Masu kirkiro shirye-shirye ko kuma content creators na iya samun kudi saboda aikinsu. Domin samun karin bayani kan medium fara daga nan/here. Ana iya samun kudi daga Medium Partner Program.

“Yayin da partner program kyakyawar hanya ce ta wallafa labarai a Medium kada ‘yan jarida masu zaman kansu su za ci za su kudance kamar” yadda Tallie Gabriel ‘yar jarida mai zaman kanta ta bayyana daga farkon shekarar 2018:

“Domin daukan nauyin aikinsu, ‘yan jarida masu zaman kansu su yi amfani da Medium a matsayin kafa na biyu da ke tura masu sha’awan labaransu zuwa shafin sun a kansu. Ku wallafa labarai a shafinku sa’annan ku sa Medium dan ku sami karin mutanen da za su karanta a kan adireshinku tare da ‘yar wasika daga karshe.”

A watan Janairun 2020 Medium ya rawaito cewa kashi 68 cikin 100 na marubutan da suka rubuata akalla labari daya wa mambobi sun sami kudi. Y ace kashi 8 cikin 100 na wadanda suke rubutu a kai- a kai sun sami fiye da $100 kuma $21,650.88 ne kudi mafi yawan da wani marubuci a taba samu a dandalin, sa’annan $8,855.73 ne kudi mafi yawa da labari daya ya taba masu.

Domin shawara kan wallafa labarai a Medium ku duba wadannan shafukan:

Substack

Substack na jaddada saukin fara wasikar labarai kyauta amma kuma a sami kudi. “Babu wata kwarewar fasahar da ake bukata: A hada lambar asusun banki kawai a sanya farashi,” a cewar shafin.

Substack na daukan kashi 10 cikin 100 na kudin da ake biya shekara-shekara da kuma kudin ruwan da ake cirewa a kati da senti 30 na aikin da banki ya yi. Marubutan da suka zabi su wallafa labaransu kyauta na iya amfani da substack kyauta su ma.

Shafin na zargin wai akwai milliyoyin mutanen da ke karanta labaransu kuma mutane fiye da 250,000 na biya.

Tun watan Yulin 2020, substack ke bayar da tallafin lauyoyi tana amfani da lauyoyin kafafen yada labarai su bayar da shawarwari ga marubuta kamar yadda suka bayyana a wannan labarin ko kuma blog post. Ya kuma fara wani shirin koyarwa wato fellowship program. Substack na kuma tallafawa masu shirye-shiryen saurare na podcast.

A watan Mayun 2020 a kasidar da ya rubuta What’s Next for Journalists? Wanda ya kirkiro substack Hamish Mckenzie ya yi tsokaci kan yadda arziki a aikin jarida ke raguwa, yana mai cewa “Muna kokarin gina wani sabon salo ne na bunkasa tattalin arzikin kafafen yada labarai wanda zai baiwa ‘yan jarida damar cin gashin kansu.”

Patreon

Mai mazauni a San Francisco, an kaddamar da Patreon a shekarar 2014 domin samar da dandalin da zai dace da zamanin dijital da mu ke ciki yanzu. Wadanda suka kirkiro dandalin suna amfani da subscription wato hanyar biya kafin ka samu damar shiga shafin. Suna kuma bayar da abubuwan da ke jan ra’ayin mutane su yi amfani da shafin.

A karshen 2019 mutane sama da 100,000 sun yi amfani da Patreon, kuma yana samun tallafa daga mutane fiye da milliyan 3. Ya ma sa ran biyan masu amfani da shafin su wallafa abubuwa $1 billiyan a 2019. Kuna iya samun karin bayani kan yadda wurin ke aiki a nan/here da nan/here

Domin bita wadanda yawancinsu masu kyau ne, ku duba manhajoji irinsu Writer’s EditMerchant Maverick, da VentureBeat. Akwai wadansu abubuwan da ba’a nuna amma ba za su iya hana bincike mai zurfi na aikin jarida ba. Kudin da akan samu ya banbanta. Grapheon kan duba duk kudin da aka samu daga Patreon

TinyLetter

Wannan wasika ce mai labarai wanda mutanen da suka kirkiro Mailchimp ke kawowa. Kyauta ne amma yana iya daukan mutane 5000 ne kadai.

Ko-Fi

Wannan kan taimaki masu rubuce-rubuce ko bidiyoyi samun tallafin kudi, sai dai sun gyara salon karbar kudin da cewa “buy me a cup of coffee” ko kuma da hausa, “saya mun kofin koffee.” Ko-Fi bay a karbar kudi. Duk wani kudi na zuwa Paypal. Idan mutun na biyan $6 a wata zai iya samun kowani shafi.

Wallafa Litattafai kai tsaye a Kindle

Wannan na taimakawa wajen wallafa litattafai na intanet da wadanda ma aka saba na takarda. Yana barin mawallafa su rike duk ‘yancin da suke da shi su kuma rika karbar kudin da ke shiga. Ana iya buga shi kai tsaye kuma ana raba shi ne ta hanyar Amzon. Kuna iya duba babban shafin. Sai dai kuma akwai wadansu matsalolin da ya kamata a duba. Wannan bitan da Doris Booth ta yi a 2019, 2019 Review a kasidar Writers and Readers ya nuna cewa akwai wadansu abubuwan da ke kasancewa kalubale wajen samun kudin da ma salon buga litattafan. Haka nan kuma kuna iya duba wannan labarin 2020 article a shawarwarin wallafa littafi a shirin zaben KDP inda kake baiwa Amazon duk wani ‘yancin da kake da shi a kan littafin. Akwai tsokaci da dama dangane da abubuwan da ya kamata a yi.

Wasu abubuwan da ya kamata a duba

Wallafa labarin a wasu shafukan zai taimaka wajen kara yawan masu karantawa. Akwai shafukan da ke taimakawa wadanda suka hada da AuthoryBuzzFeed CommunityLinkedIn, da Muckrack wadanda za su iya taimakawa wajen yada labari.

Sai dai wadannan ba su biya kuma akwai wadansu hadurra kamar raguwa a yawan mutanen da ke zuwa shafin ku. Binciken google zai iya kai mutane shafin wadanda ke taimakon a maimakon shafinku na ainihi wanda kuka saba amfani da. To amma kwararru sun ce wannan matsala ce da za’a iya shawo kai.

Domin tattaunawa dangane da irin wadannan batutuwan kuna iya karanta kasidar Carolyn Edgecomb daga Impact mai taken Do’s & Don’t’s of Republishing content on Medium.

Edgecomb ta hada da shawarwari kamar yadda za’a yi amfani da wata kalman sirri da za ta radawa google cewa duk wani ‘yanci na ku ne, kuma ka da ta sanya labarin a wani shafi na waje da ba na ku ba.

Kuna iya duba wadannan kasidun ma:

Kewaye da Duniya

Akwai shafuka da dama a kasashen duniya da za su iya ba ku damammaki. Ku taimaki GIJN wajen gina wannan kundin na wuraren da za ku iya wallafa abubuwa. Ku aiko mana da shawarwari a nan/here.

Republish our articles for free, online or in print, under a Creative Commons license.

Republish this article


Material from GIJN’s website is generally available for republication under a Creative Commons Attribution-NonCommercial 4.0 International license. Images usually are published under a different license, so we advise you to use alternatives or contact us regarding permission. Here are our full terms for republication. You must credit the author, link to the original story, and name GIJN as the first publisher. For any queries or to send us a courtesy republication note, write to hello@gijn.org.

Read Next