Bayanai a aikin Jarida: Farawa – Shawarwari
Read this article in
Wadannan bayanai na kyauta za su taimakawa duk wanda ke fara aiki da irin wadannan bayanan a karon farko.
Jagora na hadin gwiwa wajen Data Journalism: Wannan littafin shawarwarin da ProPublica ta wallafa a 2019 ya duba batutuwan da suka hada da:
- Ire-iren hadin gwiwar da za’a iya yi a dakunan labarai da yadda ya kamata a fara
- Yadda ake hadin gwiwar da ya shafi bayanan da aka tattaro daga sassa daban-daban
- Tambayoyin da suka dace a yi kafin a fara hadaka dan amfani da bayanan da aka samu daga wurare daban-daban
- Yadda ya kamata a yi hadin –kai da bayanan da bangarori biyu ko fiye za su raba
- Hanyoyin girkawa da kuma tafiyar da ayyukan da suka shafi bayanan
Data Journalism: MaryJo Webster’s Training Materials – Kayayyakin Horaswar da MaryJo Webster ta kirkiro ya kunshi kasidun da za su taimakawa duk wanda ke fara aiki da bayanai, wadanda suka hada da shawarwari, jerin sunayen litattafan da za su taimaka wajen inganta fahimta, umurni dangane da R, SQL, da alkaluma, da ra’ayoyin labarai. MarJo Webster ‘yar jarida ce da ke aiki da Minnesota Star-Tribune a Amurka.
Structuring and Sharing Data Investigations/ Tsarawa da raba binciken bayanai, wanda Marcel Pauly da Patrick Stotz daga jaridar Der Speigek na Jamus suka rubuta wa babban taron GIJN a shekarar 2019.
Data Editorial Process/Hanyoyin amfani da bayanai wanda Emilia Diaz-Struck daga Hadin gwiwar kasa da kasa na ‘yan jarida masu bincike mai zurfi ta rubutawa babban taron GIJC 2019
How to do #ddj With a Small Newsroom and a Limited Budget/ Hanyoyin amfani da #ddj a kananan dakunan labarai da karamin karfi kasida ce mai cike da shawarwari masu amfani wanda Pinar Dag ta gabatar a GIJC19 daga datajournalismturkey.
Glossary of Statistical Terms for Beginners – Jaddawalin kalmomin da ake amfani da su wajen rubutu kan bayanan da suka shafi alakaluma wanda iMedLab ya shirya.
Reverse Engineering Step by Step/ Hanyar fayyace bayanai ta yin amfani da dabarar Reverse Engineering ko kuma yin amfani da manhajoji dan komawa baya wanda Felix Ebert da Vanessa Wörmer na Süddeutsche Zeitung, Thorsten Holz na jami’ar Ruhr da ke Bochum a Jamus da Hakan Tanriverdi daga Bayerische Rundfunk (Rediyo) suka shirya wa GIJC19.
Data Journalism Tools/ Kayayyakin gudanar da aikin data Journalism daga shirin aikin jaridar kimiyya na Knights da ke jami’ar MIT. Wannan ya hada da jerin litattafai, manayan taruka, kayayyaki da sunayen ‘yan jaridan da suka kware wajen aiki da bayanai.
How to: Plan a journalism project that needs data entry/ Yadda ake tsara shirin jaridan da ke bukatar bayanai – Labari ne da Paul Bradshaw ya wallafa shafin ‘yan jarida
Diving Into Data Journalism/ Shiga aikin amfani da Bayanai a Aikin Jarida (2016) Samantha Sunne ta rubutawa kungiyar API. Wannan na kunshe da shawarwari da kuma ginshikan fara amfani da shi a dakunan labarai da ma irin kalubalen da za’a iya fiskanta wajen yin hakan.
Introduction to Data Journalism/Gabatarwa ga Data Journalism – manhaja ce ko kuma taswirar da dan jaridan Amurka Peter Aldhous ya rubuta domin karantarwa a jami’ar Berkeley. Yana dauke da darussa kan alkaluma, yadda ake samu a tsabtace da kuma amfani da manhajan lissafi wato spreadsheet da kuma irin zane-zanen da za su taimaki jama’a wajen fahimta.
Data Journalism: A guide for editors/ Bayanai dan aikin jarida: Jagora ga editoci Wannan labarin wanda Maud Beelman da Jennifer Lafleur suka rubuta kuma aka wallafa a 2019 na da taken “Gyara labaran bincike kan shi na da na shi kalubalen, musamman idan mutum bai saba da hanyoyin samun bayanan ba.”
A shekarar 2019, karidar the New York Times ta wallafa irin abubuwan da su ke amfani da su a dakunan labaransu dan inganta illimi kan bayanai.
In Data Journalism, Tech Matters Less Than the People/ A aikin jaridan da ya fi mayar da hankali kan amfani da bayanai, fasaha ta fi mutane mahimmanci. Ben Casselman wani mai daukan labaran da suka mayar da hankali kan tattalin a jaridar New York Times, ya na amfani da wani salon da ake kira harshen fasaha mai suna R kuma yana aiki da bayanai masu dimbim yawa. Sai dai a wani labarin da ya rubuta a 2019 ya ce idan dai rahoto mai kayatarwa ake so a rubuta babu majiyar da ta fi yin hira da jama’a dan samun bayanai.
Quick Guide to Data Journalism/ Takaitacciyar jagora ga amfani da bayanai a aikin jarida wanda DataCamp ya rubuta ya bayar da ma’anar amfani da bayanai a aikin jarida, ya bayar da shawarwari kan irin harsuna ko kuma fasohohin da suka fi dacewa a koya da wuraren samun litattafai shafukan Tiwita da suaransu
Ricochet wanda Chrys Wu ya rubuta na da shawarwari da kasidu daga shekara da shekaru na zuwa manyan tarukan IRE da NICAR. Akwai shawarwari da dama har ma da misalai.
Data Journalism Archives/ Ajiyan bayanan aikin jarida– Wannan rubuce-rubuce ne da yawa daga shafin Better News wadanda Cibiyar ‘Yan jaridan Amurka wato American Press Institute da Knight Temple Lenfest News Initiative suka dauki nauyi.