Bayanai a aikin Jarida: Tarukan karawa juna sani da horaswa dangane da amfani da bayanai a aikin Jarida
Read this article in
Akwai mai neman hanyoyin inganta illimi a fannin alakluma da lissafi? Wadannan shafukan suna koyar da jama’a kyauta ko kuma a farashi mai rahusa. Kuma akwai darussan a hotunan bidiyo dangane da batutuwa daban-daban da harsuna ma haka.
Kuna iya duba shafin GIJN a Youtube domin samun irin wadannan darussan kyauta.
Code Academy/Makarantar Code – Wannan na bayar da darussa kyauta da kuma farashi mai rahusa a darussan da suka hada da Python, SQL, PHP, C++, R, Java da sauransu. Akwai kuma zabin kasancewa mamba inda za’a rika biyan $20/wata-wata amma za’a dauka kudin shekara guda a tashi daya. Da wannan kudin mutun zai ci moriyar samun kwasa-kwasai daban-daban.
Cousera na bayar da darussa kyauta, ga wadanda kuma ke neman kwarewa ta musamman a wasu fannonin (Mutun na iya biyan $49/Kowace wata) a kimiyyar bayanai, alkaluma da kuma fasahohin shirye-shirye ko kuma programming language daban-daban a jami’o’i daga kusan duk kaasashen duniya. Ana gabatar da darussan a harsunan da suka hada da Turanci, Spanianci, Chinese, Rashanci, Faransanci, Jamusanci da wasu da dama.
Datawrapper: Kayayyakin gudanar da taron karawa juna sani.
edX na bayar da darussa kyauta a yanar gizo wajen tsara shiri, nazarin bayanai da alkaluma shi ma a harsuna da yawa, a ciki har da Turanci, Spanianci, Chinese, Rashanci, Faransanci da Jamusanci. Dalubai kuma suna da zabin biyan $99 dan samun takardar shaidar kammala karatu.
Investigative Reporters and Editors/ masu daukan rahoto da editoci masu bincike mai zurfi suna horaswa ta yanar gizo
Google News Initiative/ Dandalin Samar da Labarai na Google – na baiwa ‘yan jarida kayan koyon aiki, kuma sun fi mayar da hankali kan makaman aiki da google wajen samun bayanan da ake amfani da su a aikin jarida
Khan Academy/ Makarantar Khan na bayar da darussa kyauta a cikin hotunan bidiyo a yanr gizo inda suke koyarwa kai tsaye dangane da HTML, CSS, JS da SQL Languages
MIT Open Courseware tana bayar da darussa kyauta a Python, Java, da MATLAB. Kowani darasi na darasi cikin bidiyo da kuma ayyukan yi a gida.
Poynter’s News University – ta na bayar da darussa a bidiyo da kuma wadanda duk mai sha’awa zai iya yi a lokacin da yak e so. Batutuwan da ake koyarwa sun hada da nazarin bayanai, bincike mai zurfi a aikin jarida, da’a da kuma hanyoyin bayar da labarai. Yawancin darussan na bukatar biya amma akwai wadanda ba sai an biya kudi ba.
ProPublica ta wallafa darussa a YouTube dangane da batutuwan da suka shafi bayanai misali akwai gabatarwa ga code, yadda shafuka ke aiki, HTML, Basic CSS da CSS.
Workbench Training – Suna bayar da darussa kyauta kan amfani da manhajan lissafi da yin nazarin alkaluma domin amgani da su wajen rubuta labarai ko rahotanni
The Investigative Journalism Education Consortium/ Hadin gwiwar BIncike mai Zurfi da illimi a aikin jarida na da wata hadaddiyar manhaja daga masu koyar da bayanai a aikin jarida. Shafin IJEC na kunshe da abubuwa makamantan wannan har ma da misalan irin bayanan da za’a iya amfani da su wajen koyarwa.