Accessibility Settings

color options

monochrome muted color dark

reading tools

isolation ruler

Raphael Hünerfauth for GIJN

Hadakar Kungiyoyin ‘Yan Jarida Masu Bincike Mai Zurfi wato GIJN ta bayar da damar kasancewa mamba kyauta ga wadanda ke sha’awar kasancewa mamabobi daga kungiyoyi masu zaman kansu, kungiyoyin illimi ko wadanda ke aiki shigen irin na samar da illimi, da wadanda ke tallafawa masu dauko rahotannin da ke aikin bincike mai zurfi, da ma wadanda ke kula da bayanai. To sai dai hukumomin gwamnati ba za su iya shiga kungiyar ba, su ma ‘yan jarida masu zaman kansu ba su da hurumin shiga kungiyar da kuma ‘yan kasuwan da aikinsu ke dogaro da ribar da su ke samu duk da cewa aikinmu na tallafawa ‘yan jaridan da ke aiki a kowane bangare na zamantakewar al’umma.

Ana bayyana bincike mai zurfi a aikin jarida a matsayin wani tsari wanda ke bin diddigin batutuwa ta hanyar gudanar da bincike da rubuta rahotanni wadanda su kan tanadi fallasa wani batu na sirri da kuma amfani da bayanan gwamnati yayin da ake mayar da hankali kan tabbatar da adalici tsakanin al’umma dan ganin cewa kowa ya yi la’akari da alhakin da ya rataya a wuyarsa. Domin samun karin bayani dangane da wannan kuna iya zuwa kundin bayanan GIJN wato GIJN Resource Center.

Duk wanda ke sha’awar kasancewa mamba a GIJN na iya nuna hakan ta hanyar cike fam. Bayan haka kwamitin gudanarwar kungiyar za ta tantance kafin ta amince. Wannan kwamitin kolin kungiyar kan gana sau uku a shekara dan haka zai dauki watanni kafin a tantance fam din. Idan har kungiyarku ta cika sharuddan da aka gindaya kuna iya cika fam din da ke karshen wannan shafin.

Domin wadanda ke sha’awar kasancewa mamba za mu fayyace abin da muke nufi da kungiyoyi masu zamna kansu. Wadannan sun hada da kungiyoyin da ke bayar da agaji, kungiyoyin ba ruwansu da riba, kungiyoyin mambobi, gidauniyoyi, kungiyoyin da ba ruwansu da gwamnati, kungiyoyin illimi, makarantun shirye-shiryen koyon aikin jaridar da ke inuwar jamio’i ko makamantansu a kasashen duniya.

A halin yanzu GIJN na da kungiyoyin mambobi 227 a kasashe 88 a duniya.

GIJN Ta Takaita Mambobin Zuwa:

  • Kungiyoyin da ke raba ‘yan jarida masu bincike mai zurfi zuwa rukunnan kungiyoyi da kungiyoyin hadaka.
  • Kungiyoyin da ke tallafawa/rubuta rahotannin bincike mai zurfin, ko ta yin amfani da kafarsu ko kuma tare da hadin gwiwar wata kafar yada labaran ta badan muddin rahoton na dauke sakamakon binciken mahimman batutuwan da rahoton ya shafa.
  • Kungiyoyi, cibiyoyi da hukumomin da ke koyar da bincike mai zurfi a cikin ayyukan da suke yi.

Duk wadanda ke sha’awar zama mambobi, sai sun bayar da shaidar cewa suna tallafawa ayyukan bincike mai zurfi sosai a kungiyarsu ko ta wajen horaswa, bunkasa cigabar ayyukan, goyon baya, rahotanni, wallafawa ko watsawa labarai irin wadanda aka samu bayan an gudanar da bincike mai zurfi. Wannan ne zai kasance hujjar cewa kungiyar na aikin da ta ce tana yi. GIJN kuma za ta bukaci ganin shaidar rajista a matsayin  kungiyar da ba ruwanta da riba, ma’aikata, kasafin kudi da shafin intanet da kuma shafin sadarwa a shafukan sada zumunta na soshiyal mediya.

GIJN ba ta karbar kudin yin rajista. Ta kan dai bukaci mambobi su taka rawar gani a ayyukanta su kuma yi aikin jarida mai sahihanci wanda ya tanadi fadin gaskiya, ba sani ba sabo, da kuma adalci. Haka nan kuma akan shawarci mambobi su tallafa wajen tura ma’aikatansu zuwa babban taron GIJN wanda ake yi bayan kowanne shekaru biyu.

Duk mambobin da basu cika sharuddan kungiyar ba, ana iya dakatar da su ta hanyar kuri’a a lokacin da kwamitin gudanarwra kungiyar ta zauna.

Abin da GIJN ke baiwa mambobinta

  • Suna da ‘yancin zabar wadanda za su kasance a kwamitin gudanarwarsu
  • Suna iya zaban irin manyan taruka wato confeences ko kuma na karawa juna sanin da suke so su halarta da ma irin taimkon da su ke so a ba su.
  • Shawarwari dangane da batutuwan da suka shafi dorewa, hanyoyin samun kudi, rahotanni da fasahohi
  • Tallata ayyukanku a harsuna da yawa
  • Samun manhajojin da ake amfani da su kyauta ko kuma sayensu da rangwame
  • Damar kasancewa cikin kungiyar hadakar da ke tabbatar da cigaban aikin jaridar da ya shafi buncike mai zurfi a duniya baki daya.
  • Tallafi sadda mambobi ke fiskantar hari

Abubuwan da GIJN ke yi

  • Wallafa taswirar hanya, shawarwari da labarai dangane da sabbin ci-gaban da aka samu a aikin jaridar bincike mai zurfi da na bayanai, sabbin samfuran rahotanni da hanyoyin samun kudi da ma batutuwan da suka shafi tsaro da shari’a. A shekarar 2021 GIJN da abokan huldarta sun wallafa labarai fiye da dubu daya a harsuna 20.
  • Karfafa kungiyoyin da ke bincike mai zurfi ta hanyar hada kawance tsakanin ‘yan jarida ko ta yanar gizo-gizo ko kuma ido da ido. Tare da tallafin kungiyoyi 227n da mu ke da su a kasashe 88.
  • Shirya babban taron ‘yan jarida masu bincike mai zurfi a Kasashen Duniya kowanne shekaru biyu. Tun shekara ta 2001, yayin da take aiki da abokanta, GIJN ta hada ‘yan jarida fiye da 10,000 daga kasashe sama da 150.
  • Shirya babban taron GIJN na yankin Asiya, wanda ake yi bayan kowanne shakaru biyu, da kuma bayar da goyon baya lokacin manyan tarukan da akan gudanar a yankunan da tarukan karawa juna sani a yankunan Afirka, Kudancin Amurka da duniya baki daya.
  • Horas da ‘yan jarida a duniya maki daya dangane da makaman aikin da ake amfani da su a aikin jaridar da ya shafi bincike mai zurfi, dabaru, da kundin bayanai wajen tarukan karawa juna sani, lekcoci, bidiyoyi a shufukan yanar gizo da kuma koyarwa a yanar gizon.
  • Rarraba bayanai a soshiyal mediya cikin harsuna 12 tare da hada ‘yan jarida da sauran ‘yan uwansu a duk kasashen duniya
  • Wallafa Labaran bincike mai zurfi da dumi-duminsu – Shawarwari da makaman aiki, bayanai kan hanyoyin gudanar da aikin, labarai masu jan hanakali. Sabbin samfura/dabaru da mahawarori dangane da makomar rahotanni irin wadanda ke sanya ido kan lamura. Mutane a kasashe akalla 140 ke amfani da shafukanmu kowace rana.
  • Damar amfani da kundin dubban bayanai kan dinbin batutuwa a harsuna daban-daban tare da shawarwari, kudaden tallafi, hadakar kungiyoyi da sauransu
  • Gudanar da dandalin taimako wa wadanda su ke da tambayoyi dangane da bincike mai zurfi kuma ta na da kwararru fiye da 100 a fannoni da suka hada da aikin jarida, kungiyoyin da ba ruwansu da riba, tsaro, bayanai, da sauransu. Tun shekarar 2012 mutane fiye da 12,000 suka bukaci taimako ta wannan dandalin.
  • Wallafa manyan abubuwan da suka shafi irin aikin jaridar da ya yi ficce a duniya da ke kan kalandarmu, kuma akwai fiye da 50 kowace shekara.
  • Bayar da kyautar Global Shining Light ga kungiyar da ta taka rawar gani wajen kawo rahotannin bincike mai zurfi yayin da ta ke fiskantar barazana, bayan kowane shekaru biyu
  • Samar da taimako ga kungiyoyi mambobi wanda ya hada cigaban ayyukansu, samar mu su da manhajojin aiki a farashi mai rahusa, zabin irin taron da su ke so su halarta, jefa kuri’a wa wadanda su ke so su kasance mambobin kwamitin gudanarwar kungiyar da ma tallafa mu su a lokacin da su ke fiskantar barazan.

Neman zama mamba na GIJN

Domin neman zama mamba a GIJN kuna iya zuwa wannan adireshin domin cike fam. Kwamitin gudanarwar GIJN, wanda ke ganawa sau a shekara ne zai tantance wadanda suka cancanci shiga kungiyar. Kafin ku cike fam din ku tabbatar cewa kun cika sharuddan da aka gindaya na kasancewa mamba: Wato, kungiyarku ba ruwanta riba ko kuma ta illimi ce wadda ke aiki wajen tallafawa bincike mai zurfi a aikin jarida kuma tana da dangantaka da aikin jaridar da ke amfani da bayanai wato Data Journalism a turance.