Accessibility Settings

color options

monochrome muted color dark

reading tools

isolation ruler

Image: Pixabay

Riyoyin

Samun Tallafi dan Shirye-shiryen da ke Bukatar Bincike mai Zurfi

Read this article in

Image: Pixabay

Akwai tallafi dan rahotanni daga wurare da dama. Wasu sukan bayar da tallafi ga kusan kowani irin batu wasu ko suna da abin da su ke tallafawa.

Mu a nan GIJN muna da jadawalin wuraren samun tallafi da kuma kudin taimakwa ‘yan jarida na kasa da kasa

Jerin sunayen wuraren da GIJN ke da shi na mayar da hankali a kan irin damammakin da ‘yan jarida za su iya samu a matakin kasa da kasa. Yayin da shirye-shiryen da ke samun tallafi sukan bayar da gudunmawar su ne kai tsaye ga shirin rahotannin, kuna iya duba na tallafawa ‘yan jaridan kansu wato fellowship. Yawancinsu na kara illimi ne wadansunsu kuma suna hada karatun da rahoto na musamman ko kuma za su iya barin dan jarida ya rika rahotanni a yayin da ya ke karatun.

Dan samun karin bayani a matakin kasa da yankuna, ku duba damammakin da ke kan shafin IJNET. Gidauniyar Rory Peck ita ma tana da jerin sunayen a wannan shafin. Kafofin samun kudi na Amirka fiye da 100 na kan wannan shafin wanda za’a iya samu ta shafin News Media Alliance.

Shawara kan yadda ake nema

Da zarar kuka sami kungiyar da za ta taimaka, ku karanta bayanansu da kyau. Yawancin masu bayar da tallafi su kan bayar da jagora dalla-dalla kan irin shirye-shiryen da suke rajin marawa baya da kuma bukatu daban-daban da irin alfanun da za’a samu. Wadansunsu na da wa’adi tsayayye, wadansunsu kuma ana iya daga wa’adin. Watakila kuma akwai dokoki kan harshe, rubutun ko inda za’a iya wallafawa.

The News Alliance Media ya wallafa wani littafin jagora mai shafi 11 a shafin shi da ke bayani kan samun kudaden tallafi na grant. Ya duba inda ake samun grants, yadda ake samu, yadda ake yin kasafin shi, abubuwan da ya kamata a yi da zarar aka yi nasarar samu, abin da ya kamata a kula idan an zo sanya hannu a kontiragin da sauransu.

Ga wasu daga cikin shawarwarin da suka bayar dangane da yadda ya kamata a shirya:

  • Ku yi rajista dan samun wasikun labarai wadanda masu bayar da tallafi da kafofin yada labaran kasa suke bugawa dank u sanya ido kan sabbin shirye-shiryen tallafi, abubuwan da ya kamata a fi baiwa fifiko da kuma wa’adi
  • Ku rika duba shafin masu bayar da tallafin dan samun sabbin bayanai dangane da batutuwa da kuma irin rahotannin da suke tallafawa
  • Ku tabbatar kuna da akalla shafi daya na takaitaccen bayani: Ko da ba ku da wata kungiyar ba da tallafi a zuciya, ya kamata ku na da dan rubutun da ya bayyana shirin ku, irin bururrukan da ku ke da shi da bukatunku. Wannan zai taimaka wajen nuna inda ya kamata ku fi bayar da karfi
  • Ku yi waya: Yawancin ma’aikata a irin wadannan wuraren a shirye su ke su bayyana mu ku dalilin da ya sa takardarku ba ta yi nasara ba.

Daga Karshe karanta labarin Eric Karstens How Not to Win a Journalism Grant wanda ya rubuta a 2018. Karstens ya dade yana aiki a fannin tallafi a matsayin mai bayarwa da kuma mai karba. Ga gargadin da ya fi yi wa ‘yan jarida:

  • Rashin karanta sharuddan da aka gindaya
  • mantawa da batun da ya kamata a yi magana a kai
  • Rashin fayyace bayanin yadda ya kamata
  • Rashin bayyana kanka yadda ya kamata
  • Rashin tabbatar wa mai bayar da tallafin cewa za ku iya yin aikin yadda ya kamata
  • Nuna cewa bi ta kan kudin kawai za ku yi idan babu abin da ya jada wanda ke neman tallafin da ma’aikatan da kuma batun da ake so a bincika
  • Yin riga malam masallaci
  • Bayar da kasafin kudin da bas hi da nagarta
  • Rashin sanin irin kalmomi da salon da ake amfani da shi

Ana kumaiya ganin wasu karin shawarwarin a “the mechanics and art” of writing a good proposal wanda za’a iya samu a kundin bayanan ‘yan jarida da kafafen yada labarai wato Journalism and Media Lab (Jamlab).

Republish our articles for free, online or in print, under a Creative Commons license.

Republish this article


Material from GIJN’s website is generally available for republication under a Creative Commons Attribution-NonCommercial 4.0 International license. Images usually are published under a different license, so we advise you to use alternatives or contact us regarding permission. Here are our full terms for republication. You must credit the author, link to the original story, and name GIJN as the first publisher. For any queries or to send us a courtesy republication note, write to hello@gijn.org.