Bayanai a aikin Jarida: Makaman Nemowa, Tantancewa da Shirya Bayanai
Read this article in
Akwai bayanan da ba su da kan gado? Wadannan manhajojin za su taimaka muku wajen sarrafa su ta yadda za ku iya amfani da su a saukake.
OpenRefine – Wannan manhaja ce ta kyauta wadda ake amfani da ita wajen samo bayanai, gyarawa da kuma tsara su yadda za su yi amfani. Yana da mahimmanci sosai musamman idan akwai bayanai da yawa wadanda aka samo su a birkice. Akwai shi a harsunan Ingilishi, Chinese, Spanianci, Faransanci, Rashanci, Potuganci (wanda ake amfani da shi a Brazil), Jamusanci, harshen kasar Hungary, Ibranianci, harshen kasar Philippines, Cebuano, da Tagalog. Ana iya samun darasi mai kyau a nan/here.
Samun bayanai daga fayil na PDF abu ne da ‘yan jarida da dama ba su son yi. To amma akwai manhyjoji na kyauta da dama da za su iya taimakawa da wannan daikin. Tabula wannan yana taimakawa wajen samun bayanan da aka jera su cikin rukunnan da aka zana. Wata kuma it ace XPDF wadda take tallafawa bayanai a wasu harsunan da ba turanci ba. CometDocs wannan na da shafukan kyauta amma kuma akwai wanda ake biya wanda zai bai wa mutun wurin ajiya mai girma dan ajiye manyan bayanai.
CSVKit wannan na taimakawa wajen juya bayanai da kuma aiki da CSV dan yin amfani da bayanan da aka zana.
Workbench wannan makaman aiki ne da ake amfani da su wajen samo bayanai, tantancewa da tsabtacewa kafin a yi nazarinsu. An samo wannan ne daga makarantan koyon aikin jaridar Columbia wato Columbia’s School of Journalism.