Emergency Aid for Journalists/ Agajin Gaggawa ma ‘Yan Jarida
Abokan aikinmu da ke fuskantar barazana a duniya. Tun shekarar 1992, an kashe dubban ‘yan jarida sannan wasu dubban kuma sun fiskanci farmaki, tsoratarwa da hukuncin dauri, da fitina.
Akwia kungiyoyi da dama da ke bayar da agajin gaggawa duk sadda dan jarida ke fiskantar hatsari. Irin taimakon da suke bayarwa sun hada da magunguna, da daukar nauyin shari’a da ma fitar da ‘yan jarida daga kasashen da suke fuskantar hadari- Idan har akwai wanda ke fuskantar hadari, kada ya yi sake wajen tambayar taimako – akwai taimako.
The Committee to Protect Journalists/ Kwamitin Kare ‘Yan Jarida CPJ: CPJ wanda ke da mazaunin shi a birnin New York ya na gudanar da wani shirin da ke taimakawa ‘yan jarida a fannonin shri’a, kiwon lafiya da ma sauyawa ‘yan jaridan da ke fuskantar hadari wuraren zama. Yana kuma tallafawa iyalan ‘yan jaridan da aka yi wa kisar gilla ko kuma suka sami hukuncin dauri a kurkuku.
Reporters Without Borders/ ‘Yan jarida marasa iyaka ko kuma Reporters Without Borders: Wannan kungiya wadda aka fi saninta da sunanta na faransanci wato Reporters Sans Frontiéres na da mazauninta a birnin Paris. RSF tana bayar da tallafin kudi ga ‘yan jarida da gidajen labarai ta yadda za su iya kare kansu da iyalan wadanda aka daure a kurkuku. A shafin da ake kira Assistance Desk. Ana iya samun karin bayani kan kudaden insora na ‘yan jarida masu zaman kansu.
Free Press Unlimited/ Walwalar aikin jarida ba: Wannan kungiyar mai zaman kanta, wadda ke tabbatar da ci-gaban kafofin yada labarai mallakar kasar Holland ce, kuma tana da abin da ta kira Reporters Respond, wato asusu gaggawa na kasa da kasa wanda ke taimakawa ‘yan jarida da kafofin watsa labarai ta kai tsaye. Wannan kungiya tana amsa bukatun da ‘yan jarida suka tura mata cikin sa’o’i 24. Ana iya tura sakon E-mail zuwa reportersrespond@freepressunlimited.org ko kuma a kira +31208000400.
International Women’s Media Foundation/ Gidauniyar kasa da kasa ta mata masu aikin jarida IWMF: IWMF tana bayar da tallafi a fanin kiwon lafiya, da kudin sauya matsugunni da kuma taimako a fanin shari’a wa “mata masu aikin jarida ko da kafofin yada labarai ko kuma masu zaman kansu a fanin rediyo, talbijin, jarida da yanar gizo. Kungiyar ba ta daukan korifi daga wandada ke aiki a kungiyoyin da ba aikin jarida suke yi ba.
Lifeline Fund/Asusun Lifeline: Asusun Lifeline yana tallafawa kungiyoyin fararen hulan da suke fuskantar barazana ko hare-hare, da ma kungiyoyin ‘yan jarida. Tare da goyon bayan gwamnatoci da gidauniyoyi 17, Lifeline na bayar da tallafi na gaggawa na gajeren lokaci irin wanda za’a iya amfani da shi wajen zuwa asibiti, samun lauyoyi, sanya ido a kan shari’a, samun wurin zaman a wani gajereen lokaci, tsaro da kuma sayen kayayyakin aiki. Lifeline na la’akari da duk aiyukan da wanda abin ya shafa ya yi a baya, aiyukan da suka danganci kare hakkin bil adama da wanzuwar dimokiradiyya.
Media Defense/ Tsaro na kafafen yada labarai: Wannan kungiyar na birnin Landan kuma tana taimakawa ‘yan jarida ma’aikatan kafofin yada labarai da masu zaman kansa, da ‘yan kasa masu aikin jarida dan kansu wadanda ke fuskantar barazanar zuwa kotu. Kungiyar na kuma baiwa kafofin yada labarai kudaden da za su taimaka su wajen zuwa kotu da ma sauran aiyukan da za su tabbatar da ‘yancin walwalar kafafen yada labarai.
Rory Peck Fund/ Gidauniyar Rory Peck: mai mazauni a Landan, gidauniyar Rory Peck na tallafawa manema labarai masu zaman kansu da iyalansu a duk fadin duniya a karkashin shirinta na tallafawa manema labarai masu zaman kansu.
Rest and Refuge Fellowships: Akwai tallafi dan hutu da mafaka wa ‘yan jaridan da ke fuskantar matsaloli a kasashen da ke fama da ukubar yaki da sauran rigingimu. Shirin wanda ke samun goyon bayan RSF da Gidauniyar Taz Panter na bayar da kudaden tafiya da hutu na akalla watanni uku a birnin Berlin.
Cibiyar tabbatar da walwalar ‘yan jarida da kafofin yada labarai na Turai ta kaddamar da abin da ta kira “alarm centre” ko kuma cibiyar kararraurawa dan mata ma’aikata a kafafofin yada labarai inda za su iya kai karar duk wani harin da aka kai musu dan samun shawara da taimako.
Ko kuna da shawarwari? Turo mana sako ta hanyar email za mu sanya da sauran.