Accessibility Settings

color options

monochrome muted color dark

reading tools

isolation ruler

Albari

Samun kaiwa ga bayanan jama’a a duk lokacin da aka bukaci haka

Read this article in

A kasashe da dama a yankin nahiyar Afrika, samun damar kutsawa cikin kundin bayanan jama’a yakan zama abu mai matukar wuya har a wannan lokaci da muke. Dalilin haka kuwa shine rashin dokar da zai tilasta hukumomin gwamnatoci su budewa ‘yan jarida kofofin  su domin samun bayanan da suke bukata wanda suke tare dasu.

Sai dai kuma ba duka aka taru aka zama da ya ba, wasu kasashen suna bada damar samar da ireiren wadanana bayanai kai tsaye kuma cikin sauki. Ga wasu kyawawan hanyoyi da bayanai dake a adane domin ‘yan jarida a nahiyar Afirka da za su iya kaiwa ga idan bukatar hakan ya taso  domin samun bayanai game da ayyukan gwamnatoci musamman kasashen da ke da tsauraran dokoki game da samun bayanai irin haka.

Africa Freedom of Information Centre Wannan yana daya daga cikin mafi inganci wuri a nahiyar Afirka da za a samun bayanai. Bayan haka za a iya samun bayanai kan dokokin FOI a Afirka.

IFEX tana da kyakkyawan bayyani game da fadada dokokin FOI a Afirka, gami da wasu matsalolin da ake fuskanta wajen aiwatarwa.

Kenya: Akwai shafin Reporting on Good Governance in Kenya.org  ya bayyana dokokin ƙasa da na gida da dokoki samun bayanai tare da buga rahotanni kan abubuwan da ‘yan jarida za su bukata. Sannan kuma akwai littafi dake bayani akan dokokin Kenya daga jami’an Katiba.

Liberia: Shafin kundin InfoLib na bada bayanai ne a yanar gizo na yadda za a iya samun damar neman ‘yancin bayanai na FOI

Mozambique: A kasar Mozambique akwai shafin Guia do Direito à Informação Para Jornalistas, da ke bada bayanai kan yadda za a samu FOI wanda aka buga a 2016.

Nigeria: A Najeriya akwai shafin R2KNigeria wanda ke bada kwararan  bayanai kan  dokokin FOI. Ma’aikatar ma’aikatun hako ma’adinai ta Najeriya wato, The Nigeria Extractive Industries Transparency Initiative  na da shafin FOI wanda za a iya neman  damar samun bayanai daga gwamnati ta yanar gizo. Haka kuma ofishin inganta ma’aikatun gwamnati  wato The Bureau of Public Service Reforms na da shafin FOI da za a iya bi idan hakan ya taso. Haka kuma shirin inganta Tattalin Arziki da kare ‘yanci wato The Socio-Economic Rights and Accountability Project a watan Afirilun 2018 ya buga wani littafi mai suna: Amfani da Haƙƙinku na Bayanai don Kalubalantar Cin Hanci da Rashawa a Bangaren Lafiya, Ilimi da Ruwa  wato Using Your Right to Information to Challenge Corruption in the Health, Education and Water Sectors.

Rwanda: Akwai shafin Sobanukirwa wanda shafi ne dake kyauta da za a iya shiga don samun bayanai kuma yana cikin harsunan TuranciKinyarwanda da Faransanci

South Africa: Shafin Open Democracy Advice Centre shima yana samar da fom da za a cika domin samun bayanai da kuma taimako. San akwai Right2Know wanda kungiya ce da ke bada taimako wajen samun bayanai. Haka ODAC tana bada taimako domin samun bayanai.

Haka shima The Media Institute of Southern Africa yana da shafi da hanyoyi na yadda za a iya samun bayanai kan dokoki na FOI a ‘yankin Afirka.

Uganda:  A kasar Uganda akwai shafin Ask your Gov Uganda  wanda ke yanar gizo da masu amfani zasu iya samun bayanai kan duk abinda suke bukata daga kowane ma’aikatar gwamnati ta hanyar FOI.

Domin samun karin bayani game da samun bayanai ta hanyar FOI a bi nan global resources on freedom of information laws.

Republish our articles for free, online or in print, under a Creative Commons license.

Republish this article


Material from GIJN’s website is generally available for republication under a Creative Commons Attribution-NonCommercial 4.0 International license. Images usually are published under a different license, so we advise you to use alternatives or contact us regarding permission. Here are our full terms for republication. You must credit the author, link to the original story, and name GIJN as the first publisher. For any queries or to send us a courtesy republication note, write to hello@gijn.org.