Takardun koyar da Bincike Mai Zurfi a Aikin Jarida
Ku na neman shawarwari, rubuce-rubuce ko darussa? A kasa za ku ga takardun da ke jagora kan bincike mai zurfi da kuma misalai na abubuwan da ke faruwa a kasashen duniya. Da yawansu kyauta ne sai dai inda aka ce ba haka ba.
Ku na iya samun jagora a takardun da aka wallafa cikin harshen Chinese da Sapinaci. Idan kuma ku na da karin bayanan da ku ke so mu wallafa kuna iya tuntubar mu. Ku tura mana sako ta hanyar email.
Bincike Mai Zurfi a Aikin Jarida
Investigate – The Manual: Wannan littafin ya na duba batutuwan da CiFAR ta bayyana a matsayin abubuwa masu mahimmanci ga binciken cin hanci da rashawa, miyagun laifukan kudi da kwato kaddarorin da aka sace, wadanda su ne fannonin da suka fi amfani wajen: tsara ka’iada da bincike, makaman yin bincike mai zurfi a shafukan intanet, kundin bayanai da iko ko ‘yancin samun bayanai tare da kariya duniyar dijital. An kara misalai guda uku a matsayin domin sake bayyana yadda ake amfani da makaman aiki da dabaru, bisa bayanan da aka samu daga bincike ukun da aka yi a wasu kasashe, wadanda ‘yan koyon aiki a wurinmu suka wallafa. Akwai shi kuma a harshen Faransanci
Modern Investigative Journalism: Wanda Mark Lee Hunter da Luuk Sengers tare da Marcus Lindemann suka rubuta. An kawatanta shi a matsayin manhajar ta “gota abin da malami ke koyarwa a aji : Yana taimakawa sabbin malamai a fannin su koyi yadda ya kamata su koyar, ta kwatanta irin tambayoyin da dalubai za su tambaya (tare da amsoshinsu), tare da ayyukan da za su yi a aji da wanda za su kai gida su yi wadanda kuma ke koyarwa ta hanyar tattaunawa da kuma kwarewa.” Marubutan Story-Based Inquiry (ku duba kasa) ne suka bayyana haka. Ku na kuma iya duba kasidar da aka gabatar a babban taron GIJC19
Investigative Journalism Manual: Wannan jagorar mai amfani sosai an fara ta ne a matsayin littafin da zai taimakwa ‘yan jarida a Afirka da misalai, wanda gidauniyar Konrad Adenauer ta Jamus ta wallafa. Wannan sabon da aka wallafa yanzu na la’akari da duniya baki daya kuma an tsara shi ne ya taimakwa ‘yan jaridan da ke fama da dokokin da ke kuntata musu, inda babu gaskiya kuma basu da makaman aiki. Akwai shi a harsunan Bahasa da Mongolia da kuma shafin yanar gizo-gizo.
Digging Deeper: A guide for investigative journalists in the Balkans / Jagora na ‘yan jarida masu bincike mai zurfi a yankin Balkan BIRN suka wallafa wannan kuma ana iya saye duk sadda ake so. Kungiyar Masu Rahotannin Bincike Mai Zurfin (BIRN) na mayar da hankali ne kan samo bayanai a yankin baki daya. Daga cikin wadanda suka bayar da gudunmawa a littafin har da marubuciya Sheila Coronel darektan Cibiyar Bincike Mai Zurfi na Stabile da ke jami’ar Columbia, ita ma ta bayar da shawarwari da kuma irin salon da ta ga ya fi dacewa a irin wadannan rahotannin. Ana iya sauke babin farko na littafin a kyauta. Ana iya samun su a harsunan turanci da Macedonianci
Investigative Journalism Handbook (2020) Daga Cibiyar Kafofin Yada Labarai na Aljazeera
Drehbuch der Recherche (Script for Investigations) Wannan jagora ce kan gudanar da bincike wanda Mark Lee Hunter da Luuk Sengers su ka rubuta kuma aka wallafa a Jamus. Littafin ya na cikin harshen Jamusanci
Exposing The Truth: A Guide to Investigative Reporting in Albania: Wannan littafin mai shafuka 73 ya na amfani da misalai ne da irin salon aiki da shawarwarin da aka riga aka gwada aka san karfinsu. OSCE da BIRN suka wallafa. Akwai shi da turanci da Albanianci.
The Hidden Scenario: Littafin da Luuk Sengers da Mark Lee Hunter su ka rubuta a 2019 “ya mayar da hankali ne kan yadda kirkiro da labarin da ya kunshi hasashen abubuwan da suka faru zai iya taimakawa wajen bincike.” Ana iya saye daga Cibiyar Aikin Jarida na Bincike Mai Zurfi.
Follow The Money: A Digital Guide to Tracking Corruption / Ku bi Kudin: Jagora na Dijital Dangane da Gano Cin Hanci da Rashawa: Wannan littafin kyauta ne wanda Cibiyar ‘Yan Jarida na Kasa da Kasa suka wallafa. Akwai shi da Turanci, Rashanci da harshen mutanen kasar Georgia.
Global Investigative Journalism Casebook: Wannan littafin na tafe daura da Story-Based Inquiry (ku duba a kasa) . Yana kunshi da labaran da aka rubuta bayan kammala bincike mai zurfi da kuma yadda masu dauko rahotannin suka yi binciken labaran.
Golbal Investigative Journalism: Strategies for support: Wannan bincike ne da kuma tattaunawar da aka yi game da yadda bincike mai zurfi ke bazuwa a kasashen duniya yanzu, karkashin jagorancin David E. Kaplan. Littafin ya bayyana shawarwari tare da tsarin kungiyoyi masu zaman kansu wadanda ke binciken da hanyoyin samun tallafi tare da hanyar samun kungiyoyi a duniya baki daya. Cibiyar Taimakwa Kafofin Yada Labarai a Duniya ta wallafa a harshen turanci.
Citizen Investigation Guide: Wannan jagorar na 2019 daga GIJN an yi shi ne domin ya taimakwa ‘yan kasa wadanda ba ruwansu da aikin jarida wajen yin bincike da rubuta rahotanni.
Guide to Investigative Journalism: Wannan jerin rahotannin da tashar PBS ke yi a Amurka na koyawa masu dauko rahotanni yadda za su gano labari, su yi hira da jama’a, su nemo bayanan da ake bukata, sa’anan su shirya labarin a watsa shi ga jama’a. A harshen turanci aka buga.
Introduction to Investigative Reporting wanda Brant Houston ya rubuta (Poynter News University) Darasi ne wanda dalibi zai bi daki-daki da kan shi a shafin yanar gizo-gizo. Ana biyan $29.95 na dalan Amurka
Investigating Religion: An Investigative Reporter’s Guide wanda Debra L. Mason da Amy B. White su ka rubuta. Ana iya saye daga IRE. Da turanci aka wallafa
Investigative Journalism Manual: Wanda Kungiyar ‘Yan Jaridan Afirka masu Bincike Mai Zurfi wato Forum for African Investigative Reporters (FAIR) su ka rubuta. Wannan cikakken jagoran ya bayar da shawarwari da shafuka na musamman wadanda ke magan kan kiwon lafiya da da’a da kuma misalai daga kasashen Afirka. An rubuta shi a harsunan da suka hada da Turanci, Bahasa (harshen Indonesiya) Spanianci, harshen Vietnam, Koreanci, Mandarin, Japanese, Burmese, Sinhalese, Tamil, Mongolian, Nepal, Dzongkha, Bengali
Investigative Journalist’s Guide to Company Accounts – Wanda Raj Bairoliya ya rubuta tare da tallafin Cibiyar Bincike Mai Zurfi na ‘Yan Jarida wato Centre for Investigative Journalism. Akwai shi idan ana so saya. Jagorar yana taimakawa masu bincike wajen fahimtar sha’anin kudin manyan kamfanoni ko kuma dan su iya tambayar abubuwan da suka dace.
Investigative Oline Search: Wannan wanda Cibiyar Bincike Mai Zurfi na Yan Jaridar da ke da mazaunin ta Burtaniya ta wallafa a 2011, yana tattauna yadda ake samun bayanai a intanet da kuma yadda ake tantance shi.
Investigative Photography: Supporting a story with pictures / Bincike Mai Zurfi da Daukar Hotuna: Tallafawa labarai da hotuna wanda CJ Clarke, Damien Spleeters da Juliet Ferguson suka wallafa a turanci. Ana iya saye wurin CIJ
Investigavie Reporters Handbook Karo na 5, wanda Brant Houston da wasu masu dauko rahotanni da editoci a fannin bincike su ka rubuta. Ana iya sayen littafin a IRE. An rubuta da turanci ne.
Investigative Reporting: A Toolkit for Reporters: Wannan littafin mai shafuka 107 wanda Cibiyar Kasa da Kasa ta ‘Yan Kasuwa Masu Zaman Kansu wu kawallafa a 2009 tare da tallafi daga USAID da jaridar Al-Masry Al-Youm. A turanci aka rubuta.
Investigative Reporting in Emerging Democracies: Models, Challenges and Lessons Learned / Rahotannin Bincike Mai Zurfi a Dimokiradiyya mai Tasowa: Masu abun koyi, Kalubale da darussan da aka koya – Labarin Drew Sullivan dangane da shirin rahoton fitattun masu aikata miyagun laifuka da cin hanci da rashawa tare da shawarwari na tsara shirye-shirye makamantan wannnan, bukatar samarwa editoci kariya da sauransu. Cibiyar Taimakwa Kafafen Yada Labarai na Kasa da kasa ta wallafa shi a harshen turanci.
Manual for Arab Journalists on Freedom and Information and Investigative Reporting / Littafin jagora ta ‘yan Jarida Larabawa danagane da Walwala da Bayyanai da Bincike Mai Zurfi. Wannan kyauta ne ana iya saukewa littafin mai shafuka 21. UNDP ce ta dauki nauyin wallafawan kuma ana iya samun shi a Harshen Turanci da Larabci.
The News Initiative. Wannan wanda google ke bayarwa darassi ne mai sassa 9 a kan bincike mai zurfi a aikin jarida wandanda za’a iya amfani da su da makaman aikin da google ta kirkiro.
The Science Writers’ Investigative Reporting Handbook / Littafin jagora wa marubutan Kimiya: Littafin da Liz Gross ta rubuta a 2018 dan yin bitan labarin da ke bayan yadda ake samun labarai domin gano bayanan da aka boye da kuma son zuciyar (idan akawai) da aka sakaya.
Raising Hell: A Citizen’s Guide to the Fine Art of Investigation: Cibiyar Bincike Mai Zurfi na masu dauko rahotanni , wadda kungiya mai zaman kanta ce ta kan bayar da shawarwari da koyarwa ga al’umma kan yadda za su gudanar da bincike su gano cin hanci da rashawa a gwamnatoci su kuma fallasa wuraren da ke fama da magudi.
Reporting in Indigenous Communities / Rahotanni a al’ummomin na ‘yan asali Wannan daya daga cikin masu dauko rahotannin gidan talbijin na CBC da ke Canada Duncan McCue ya rubuta a 2011. Ana iya amfani da shi wajen rahotannin al’ummomin ‘yan asalin ko’ina a duniya.
Story Based Inquiry: Cikakkiyar jagora ce ta bincike mai zurfi wanda Mark Hunter, Drew Sullivan, Pia Thosden, Rana Sabbagh da Luuk Sengers su ka rubuta. UNESCO ce ta bayar da kudin yin wanann aikin wanda ke nuna hanyoyi, dabaru, har da bincike da rubutu da yadda za’a tabattar da nagartar aikin a kuma yada. Akwai shi a harsuna daban-daban ciki har da Turanci, Larabci, Faransanci, Rashanci, Spanianci da sauransu.
The Story Tells the Facts / Labari na Fadan Gaskiya wanda Mark Lee Hunter da Luuk Sengers suka rubuta yana bayyana dabarun rubutu har da yadda ake tsara labari mai karfi, mai daukar hankali wanda kuma karshen shi zai bar wadanda su ka karanta da abin tunani a kau.
Undercover Reporting: Wannan ba littafi ba ne amma kundin bayanai ne da ke kan intanet wanda aka fara shi a matsayin littafin da zai taimakawa wadanda su ke bincike dan rubuta wani littafi mai suna Undercover Reporting: The Truth About Deception. Wanda ke magana kan yarda mai daukan rahotanni zai saje da jama’a ya batar da kama domin ya dauko labarin da zai fallasa gaskiya. Shafin na dauke da misalai da yawa, akwai wadanda ma aka yi shekaru 100 da suka gabata.
The Verification Guide for Investigative Journalists / Jagorar Tantance Bayanai Wannan na da babi 10 da misalai uku. Batutuwan sun hada da makaman aikin bincike a intanet, bayanai, da labaran da masu amfani da shi su ke samu da kuma da’a. An wallafa shi dan a yi amfani da shi daura da wadansu littatafan da suka hada da Verification Handbook da Verification Handbook: Addittional Materials. Domin samun wadannan litattafan kuna iya zuwa wanann shafin here.
A Watchdog’s Guide to Investigative Reporting / Jagorar Masu Sanyo Ido Kan Bincike Mai Zurfi – Wannan ya fi mayar da hankali ne a kan nahiyar Afirka. Littafin da aka wallafa a turanci a shekarar 2005 na bayar da misalan ayyukan koyi kuma yana duba irin kalubalen da ake fuskanta a wanann fannin domin wadanda ke sha’awan shiga fannin a dama da su.
Data Journalism
Lessons from 30 Years of Teaching Journalists Data Journalism / Darussa daga koyar da ‘yan jarida na tsawon shekaru 30, wannan shawarwari ne Brant Houston ya rubuta. Na tsawon fiye da shekaru 10 yanzu, Houston ne babban darektan kungiyar editoci da masu dauko rahotanni na bincike mai zurfi
Teach Computational Thinking Not Just Spreadsheets or Coding / Koyar da Tunanin Lissafi Yadda ba sai an Dogara da Manhajojin Lissafi Kadai ba – shawarwarin Paul Bradshaw daga Jami’ar Birmingham/ Sashen Bayanan BBC
7 Countries 9 Teachers: A dossier of data journalism teaching strategies / Kasashe 7 da malamai 9: Kundin dabarun koyar da aikin jaridan da ke amfani da bayanai Wadanne hanyoyi ne suka fi dacewa a gabatar da bayanai irin na kidaya da lissafi ga dalubai? Nouha Belaid, Anastasia Valeeva, Bahareh Heravi, Roselyn Du, Kayt Davies, Adrian Pino, Eduard Martin Borregin, Soledad Arreguez da Jeff Kelly Lowenstein
Data and Computational Journalism, Wannan labarin na 2020 “na bayar da shawarwari hudu da za su taimaki masu koyarwa wajen gyara manhajar koyarwarsu ta yadda za su sanya bayanai irin na alkaluma, ganin yadda abubuwa ke sauyawa cikin gaggawa.” Marubutan Norman P. Lewis Mindy McAdams da Florian Stalph suka ce haka, kuma ga shawrwari hudun:
Na farko, ya kamata a ce koyar da kidaya da fahimtar alakaluma su kasance tilas. Ko a yi su a cikin darussan lissafin da ke ake da su yanzu, ko kuma a kirkiro mu su na su darassin. Na biyu, a koya wa dalubai yadda za su guji yin kuskure wajen fassara alkaluma ko kuma rubuta labarai kan alkaluman a darussan da suka kunshi rubuta labarai ko kuma amfani da hotuna da bidiyo. Na uku, ya kamata darussan da ke dangane da da’a su tattauna yadda amfani da alkaluma a matsayin hanyoyin fadan gaskiya kan kasance kalubale. Na hudu tunanin lissafi, ko kuma yadda za’a shawo kan matsala yadda komfuta ke yi abu ne da za’a iya koyarwa a azuzuwan da ke koyar da dabaru.
More Effective Teaching of Data Journalism to Working Journalists wanda Kuang Keng Kuek Ser daga Data-N ya gabatar a taroan GIJC19. Shawarwarin dan masu koyarwa ne wadanda ke koyar da Bayanai a Aikin Jarida ga ‘yan jaridan da ke aiki.
Hacking the Curriculum: How to teach data reporting in journalism schools / Yadda ake koyar da rahotannin bayanai a makarantun da ke koyar da aikin jarida Wani rahoton Cibiyar ‘yan jarida na Amurka na 2018 ya yi bayanin cewa “Shawararmu ita ce makarantun da ke koyar da aikin jarida su koyar da amfani da bayanan a matsayin daya daga cikin mahimman abubuwan da ya kamata kowani dalibi ya iya.
Where in the World Can I Study Data Journalism? / A ina a Duniyan Nan Zan iya Koyon Data Journalism ko kuma Bayanai a Aikin Jarida? Wannan labarin da aka wallafa a 2019, Bahareh Heravi ce ta takaita binciken da ta yi kan wannan batun a cikin wata kasidar da ta wallafa mai suna 3Ws of Data Journalism Education, Published by Data Journalism Practice. Kowa na iya samun wannan bayanin a shafin UCD Academic repository. Yana ma hade da taswira.
International Journalism Consortium Wannan jaddawalin manhajoji ne da kwasa-kwasan da za’a iya yi a data journalism.
Computer-Assisted Reporting: A Comprehensive Primer: Littafi ne kan amfani da taimakon komfuta wajen fahimtar alkaluma idan aka zo rubuta labarai, wanda Fred Vallance Jones da David McKie su ka rubuta.
Computer-Assited Reporting: A Practical Guide: Karo na hudu, jagora ce kan amfanin da komfutar wanda Brant Houston ya rubuta.
Data Journalism Handbook – Littafi ne na kasa da kasa wanda aka yi hadin gwiwa tsakanin kwararru a fannin amfani da bayanai a aikin jarida wajen wallafawa. A ciki akwai bayanan kalmomi masu sarkakiya, misalan irin ayyukan da aka yi wa bincike na musamman, da shawarwarin yadda za’a saba da yin nazarin alkaluma. Wannan aiki ne na Cibiyar ‘Yan Jaridan Turai da giduaniyar Open Knowledge. Ana iya samun shi a Larabci, Turanci, Faransanci, Rashanci da Spanianci amma kuma ana iya samun shi a wasu karin harsuna guda 12.
Flowing Data – Kwararre kan alkaluma Nathan Yau wanda ya rubuta Data Points: Visualization that means Something da Visualize This: The Flowing data Guide Design, Visualization and Statistics. The Learning to Data na da darussa da litattafai wanda za’a iya amfani da su wajen lakantar batun.
Mapping for Stories: A Computer-Assisted Reporting Guide – Jagora ce ta amfani da komfuta wajen dauko rahotanni wanda Jennifer Lafleur da Andy Lehren su ka rubuta.
Teaching and Training
Model Curricula for Journalism Education / Manhajar da ta fi Dacewa Wajen Koyar da Aikin Jarida. Wannan jagora ce da ke mayar da hankali wajen koyar da aikin jarida a kasashe masu tasowa da ma demokiradiyya masu tasowa. Jagorar wadda UNESCO ta kirkiro na da kwasa-kwasai 17 a ciki har da bincike mai zurfi wanda za’a iya kwaskwarewa ya saje da bukatun kasar da za’a yi amfani da shi. Akwai shi a harsuna da dama wadanda suka hada da Turanci, Faransanci, Spanianci, Rashanci, Arabic, Chines, Nepali, Portuganci da Farsi.
International Journalism Education Consortium – Hadin-gwiwa ta kasa da kasa a illimin aikin jarida ita ma ta yi aiki a kan abubuwan da ya kamata a koyar dangane da batun bincike a aikin jarida da kuma manhajan da zai tabbatar an sami illimin aikin jaridar yadda ya kamata.
Algorithms for Journalists: Wannan ma manhaja ce da ke duake da fasahar Algorithms – wato dokokin da ake bi wajen amfani da alkaluma idan ana lissafi ko neman shawo kan matsala – wanda za’a iya koyarwa a azuzuwa, irin wanda Jonathan Stray ke koyarwa a jami’ar koyon aikin jarida ta Columbia a karkashin shirin jami’ar mai suna The Lede. Ana iya samun shi a GitHub (Inda ake ajiye bayanan da za’a iya saurare) akwai kuma adiresoshin shafukan da za’a iya dubawa, kasidu, rubuce-rubuce na karantawa da sauransu. Wannan darasin an yi shi ne dan wadanda suka san wani abu, (komin kankantan shi) a shirin Python.
Better News: Shafin da ke da abubuwa da yawa na taimakawa ‘yan jarida, wanda kuma ke karkashin jagorancin Cibiyar ‘Yan Jaridar Amirka. (American Press Institute)
AEJMC Task Force for Bridges to the Professions 2017 Report. Wani rahoton 2017 kan hadaka tsakanin masana a fannin ilimi da ‘Yan jarida daga Kungiyar Ilimi a Aikin Jarida da Sadarwa. (AEJMC)
Observations on how we teach drone Journalism / Sakamakon sanya ido kan yadda mu ke koyar da aikin jarida wanda Judd Slivka daga makarantar koyar da aikin jaridar Missouri (Amurka) ta rubuta.
Algorithms Course Materials at Columbia Journalism School / Makaman aiki da na koyon fasahar Algorithms a makarantar koyar da aikin jarida ta Columbia CJS – Manhajar koyar da algorithms wanda farfesa Jonathan Stray ya rubuta.
The Field Guide to Security Training / Jagorar horas da ‘yan jarida kan tsaro Manhaja ce da ke karkashin jagorancin OpenNews, kungiyar da ke taimakwa masu kirkiro da fasahohi da zane-zane, da nazarin alkaluma su taru su kuma hada gwiwa a shirye-shiryen aikin jarida, kuma tare da BuzzFeed Open Lab suna bayar da tallafin zuwa kara illimi kan fasahohi a BuzzFeed News.
Wasu karin litattafai masu amfani
The Mojo Handbook: Theory to Praxis, Wannan jagora ce mai shafuka 350 jagora ce wadda marubucin GIJN Ivo Burum ya rubuta wadda kuma ke bayar da darussa na yadda ake amfani da wayar hannu dan bayar da labarai, ga wanda ke kokarin gane bakin zaren cikin gaggawa. Akwai shawarwari kan yadda ake nadan bidiyo da muryoyi, da gyarawa duka a kan wayar hannun da ma yadda ake bayar da labarai masu daukar hankali. Littafin ya yi bayanai kan kusan komai da komai.
The James W. Foley Journalism Safety Modules. Wadannan darussa ne wadanda aka kirkiro domin nunawa daluban da ke karanta aikin jarida da sadarwa cewa kariya da tsaro suna da mahimmancin gaske ga aikin jarida mai dorewa. Gidauniyar James W. Foley ce ta kirkiro wadannan tare da hadin-gwiwar Kwalejin Sadarwa ta Diederich da ke Jami’ar Marquette. Darussan guda 16 wadanda ke maganan kariya sun yi la’akari da batutuwa da dama a ciki har da tantance hadarin da ke tattare da zuwa dauko labarai, nauyin da ya rataya a kan manajojin dakunan labarai, tsaron mata da ‘yan jaridan da ake wa kallon tsiraru, rahotannin tashin hankali (Har da zanga-zanga) aiko rahotanni lokacin annoba, kula da kai, da wuraren samun kulawa, hira da majiyoyin da ke da hadari, rahotanni kan rikice-rikice a kasashen waje, kare bayanan dijital da kuma dauko labaran da ke da nasaba da yanayi. A kan hanya, dalubai za su koyi tabbatar da kariya a matsayin wani bangare mai mahimmancin gaske ga aiwatar da aikin jarida mai karko, mai lafiya kuma cikin da’a. Gidauniyar James W. Foley na da abubuwa da dama da ya ke gabatarwa.
“A Taste of Trouble” / Dandanon Rigima,” Shekaru 20 da suka gabata, Aniruddha Bahal ya janyo rigima sosai bayan da ya gudanar da bincike kan badakalar “gyaran wasannin” da wasu manyan jami’an wasan Cricket ke yi a Indiya. Ba karamin abu ba ne mutun ya kalubalanci babbar hukumar wasanni a Indiya kamar yadda Bahal ya yi, dan haka sai aka rika mi shi lakaba da “Mahaifin aikin Jarida a Indiya.” Littafin da ya fitar kwanan nan “A Taste of Trouble,” ya rubuta lokacin lockdown ne, wato lokacin da aka hana fita sakamakon COVID-19. Littafin ya fara daga rayuwarsa tun yana yaro zuwa sadda ya kafa na shi ofishin bincike mai zurfi a aikin jaridar a lokacin da – a cewar wata jaridar India, Hindustan Times – “Fadar gaskiya ko day aba ta cikin ajandar kafafen yada labaran kasar.”
Empowering Independent Media: US Efforts to Foster a Free Press and an Open Internet Around the World: Wannan littafo ne wanda ke duba ci-gaban kafofin yada labaran da ke da mahimmanci ga kafofin yada labaran da ba ruwansu da yin riba, da kungiyoyi masu zaman kansu a kasashe masu tasowa da masu sauyawa. Littafin ya duba bangarori 7 na ci-gaban kafofin yada labarai, wadanda suka hada da: Tallafi, dijital, kafafen yada labarai, dorewa, dokokin kafafen yada labarai, kariya, Ilimi da sanya ido da kimantawa.
Google search Tips For Journalists / Shawarwari na Yin Bincike a Shafin Google Wannan gajeruwar jagorar tana bayar da bayanai masu mahimmanci wajen amfani da shafin google dan yin bincike. Expertisefinder.com ta hada bayanan.
Journalists Survival Guide / Jagorar ‘Yan Jarida: Wannan an wallafa ta ne a Beirut karkashin jagorancin gidauniyar Samir Kassir. Wannan jagorar mai hotuna an yi ta ne dan taimakawa ‘yan jarida da masu fafutukan da ke aiki a yankunan da ke fama da yaki ko tashe-tashen hankula. Amma kuma yana dauke da bayanai kan yadda ake tabbatar da tsaro a duniyar dijital ta yadda ko kun yi bincike a intanet ba wanda zai iya gane inda kuka shiga ko abin da kuka bincika. Akwai shi a Turanci da Larabci
Legal Leaks Toolkit: A Guide for Journalists on How to Access Government Information: Wannan littafin na da tsawon shafi 75 kuma yana dauke da bayanai dangane da shika-shikan aikin jarida, har zuwa sahihan hanyoyin samun bayanai Kungiyar Access Info Europe tare da hadin gwiwar Kungiyar da ke dauko rahotannin yankin gabashin Turai.
Reporting Atrocities: A Toolbox for Journalists Covering Violent Conflict and Atrocities: Wannan cikakken littafin mai shafuka 61 ya duba yanayin rikici, yadda ake labarin shi, da rawar da ya kamata dan jarida ya taka a irin wannan lokacin. Marubucin Afirka ta Kudu Peter Toit ya rubuta yayin da Internews kuma suka wallafa.
Reporting on Corruption: A Resource Tool for Governments and Journalists: Wannan littafin mai shafuka 117 ya bayar da shawarwari ga gwamnatoci da ‘yan jarida ne kan labaran cin hanci da rashawa. Littafin wanda Ofishin Majalisar Dinkin Duniya kan Miyagun kwayoyi da laifuka su ka wallafa, ya dan goce daga tattaunawar cin hanci da rashawan kadan amma kuma akwai bayanai masu amfani sosai wadanda suka hada da yadda ake kare majiyoyi, ‘yancin samun bayanai, da hanyoyin kula da kai.
SEEMO Safety Net Manual. Guidelines for journalists in Extraordinary Emergency Situations: Wannan Kungiyar Kafafen yada labaran yankin Kudu Maso Gabashin Turai ne su ka wallafa shi a matsayin wani bangare na babban tsarin kare wadanda ke aikin jarida a yankin.
Tragedies and Journalists / Abubuwan Takaici da ‘Yan Jarida: Jagora mai shafuka 40 wanda ke da shawarwarin da za su taimakawa ‘yan jarida masu daukar hoto, da editocin da ke rahoto kan tashin hankali yayin da su ke kokarin kare kansu da wadanda abin ya shafa. Cibiyar Aikin Jarida da Rauni na Dart ta wallafa. Joe Hight da Frank Smyth su ka rubuta.
Verification Handbook /Littafin Tantancewa: littafi ne na ‘yan jarida da ma’aikatan agaji daga Cibiyar ‘Yan Jarida na Turai. Yana bayar da makaman aiki da dabaru da yadda ake amfani da bayanan da aka samu lokacin da ake fama da rikici na gaggawa.
Who’s Running The Company: A Guide to Reporting on Corporate Governance: Wannan gabatarwa ce ga rahotanni kan shugabanci a kamfanonin fararen hula, kuma yana da bangarori daban-daban wadanda ke magana dangane da kwamitin gudanarwa, rahotannin kudi, da kuma sanya ido kan abubuwan da kamfanin ke yi. Kungiyar kudi na kasa da kasa na Bankin Duniya ta wakkafa wannan rae da Cibiyar ‘Yan jarida na Kasa da Kasa. Akwai shi a harsunan da duka hada da Turanci, Faransanci, Spanianci, Portuganci da Mongolia da Rashanci da Bahasa.
Security and Covering Conflict: IJNET ta wallafa jerin jagorori ga tsaron ‘yan jaridan da ke aiki a wuraren rikici daga kungiyoyi da dama. Wadansunsu na cikin harsuna daban-daban