Bayanai a aikin Jarida: Shirya Bayanai – Shawarwari
Read this article in
Da zarar aka sami bayanai, ana iya duba wadannan shawarwarin na kyauta da darussan da ke tsokaci kan yadda za’a iya bincike a kuma tsabtace su kafin a fara yin nazarin su.
Wannan labarin kyakyawar misali ce na abubuwan da ya dace mutun ya yi idan akwai gurabe a bayanan da mahukunta suka bayar (2021).
Data Biographies: How to Get to Know Your Data/ Hanyoyin gano tarihin bayanai (2017) taskar blog ce da Heather Krause ke rubutawa. Krause tana tare da shafin bai wa ‘yan jarida shawarwari dangane da bayanan aikin jarida a Canada mai suna idataassist wanda ke bayanai kan hanyoyin bincike da kuma tara bayanan (har ma da irin abubuwan da ke bayar da alamun samun kalubale nan gaba) na bayanai tun kafin a fara nazarin su.
The Quartz Guide to Bada Data/ Jagorar Quartz wajen gane gurbatattun bayanai (2018) Wannan fayil ne a kan GitHub wanda ke tattauna irin matsalolin da aka fi gani a cikin bayanai da hanyoyin gyarawa. An fassara shi ziwa harsunan Chinese , Japanese , Portuganci da Spanianci.
ProPublica’s Guide to Bulltetproofing Data/ Shawarar ProPublica kan hanyoyin inganta tsaron bayanai (Updated 2018) Jennifer Lafleur ta hada tare da tallafi mai dimbin yawan da ta samu. Fitattun hanyoyin tantance bayanai. Har yanzu ana kan ingantawa dan haka kuna iya karawa da na ku shawarwarin
Wannan tutorial/darasin wanda dan jaridan Beljiyam Stijn Debrouwere ya hada yana bayani ne kan irin kurakuran da ake yawan samu a bayanai da kuma yadda za’a kaucewa yi mu su fassarar da ba dai-dai ba. Ana iya samun shi kyauta a shafin datajournalism.com.
Get started with OpenRefine/ Yadda ake amfani da fasahar OpenRefine (2017) Wannan darasin takaitacce ne inda ake amfani da hotuna a bayyana yadda ake amfani da fsahar tantance bayanan da ake kira OpenRefine. Wata malama a jami’ar UCLA mai suna Miriam Posner ta krikiro.
Cleaning Data in OpenRefine/ Tsabtacewa ko tantance bayanai a OpenRefine (2018) Wannan cikakken jagora ne tare da misalai da darussa cikin bidiyo wanda ke kwatanta yadda ake sarrafa bayanai idan ana amfani da OpenRefine. John Little ne ya kirkiro wannan. Little kwararre ne a kimiyan bayanai wanda ke aiki a dakin litattafan jami’ar Duke.
Wannan tutorial/darasin wanda dan jaridan Beljiyam Maarten Lambrechts ya koyar gabatarwa ne ga amfani da manhajan Excel dan tantance bayanai da kuma tsabtace su yadda za’a iya ganewa cikin sauki. Wannan koyarwar na bukatar rajista amma ba’a biya. Ana iya samun shi a kan shafin datajournalism.com.