Finding Expert Sources/ Samun kwararrun majiyoyi
Read this article in
Kuna neman majiyoyi? Samun kwararru a wani fanni na musamman yawanci da shi ne ake fara labari. GIJN ta gudanar da bincike kan shawarwari da dama dangane da kwararrun majiyoyi. Bayan da aka cire wadanda aka daina yayinsu, da wadanda suke tattare sarkakiya da ma wadanda na talla ne kadai, mun samu kadan wadanda za’a iya amfani da su. Daga kasa za ku ga shidda daga cikin kundin bayanan da ke aiki wanda yawancin ‘yan jarida ke amfani da su wajen samun kwarraru.
Kuna kuma iya zuwa shafin cibiyar bayanan mata ma’aikatan jarida wato Women in Journalism Resource centre.
SCiLine: Kwalejin Ci gaban Kimiyya na Amirka ne ke daukan nauyin wannan kuma “tsari ne mai zaman kanshi wanda ke hada ‘yan jarida da kwarraru kyauta kuma a kan lokaci, da ma sauran masu sadarwa a kafofin jarda, rediyo da talbijin da ma labarai na dijital dangane da batutuwan da suka shafi kimiya.” Wajibi ne a tura sako dangane da abin da ka ke bukata, wa’adin da ka ke da shi da fannin kwarewar da ka ke bukata
Dandalin Ku Nemi Kwararriya a Fanin Kimiyya, dandali ne da mata masana kimiyya 500 ke daukar nauyin shi. “yana sada mata masana kimiyyan da aka tantance wadanda kuma suke da kwarewa mai zurfi a fannoni daban-daban na kimiyyar da duk wanda ke bukatar tattaunawa da masana kimiyya a labarin shi, ko ya gayyaci babban mai magana a taro ko mahawara ko koyarwa ko kuma taron karawa juna sani. Ana iya samun macen da za ta hada gwiwa da ku a wani shiri ko kuma dai kawai ta kasance kwararriya a kowane irin fanni ake bukata.
Diverse Sources/ Majiyoyi daban-daban – Wannan kundin bayanai na kwararru a fannonin kimiyya, kiwon lafiya da muhalli, wadanda bas u yi suna sosai na
Expertise Finder/ Manhajan gano gwani – wani tsohon dan jarida kuma kwararren injiniya a fannin sarrafa “software” ya kirkiro wannan manhajan da zai iya gano kwararru n da ke kusa da unguwar ku. Manhajjan zai fitar da sunayen wadanda aka riga aka tantance a matsayin majiyoyi a jami’o’in da ke kasashen Amirka da Canada da ma cibiyoyin nazari masu daraja. Shafukan sun bayyana sunayen majiyoyin da fannonin da suka kware, sun bayar da takaitaccen bayani dangane da su, sun kuma bayar da lambobinsu ta yadda za’a iya tuntubar su. Duk wannan kyauta ne kuma kamfanin na samun kudaden shigan shi daga makarantu ne, wato Jami’o’i da kwalejoji, ta hanyar shirya takardun da suka kunshi sunayen kwararru a fannoni daban-daban.
Shesource: Wannan shiri ne wata kungiyar mata mai zaman kanta ne mai suna Women’s Media Centre ko kuma cibiyar ‘yan jarida mata. Shirin ya kunshi bayanan mata kwararru 1,100 wadanda aka tantance a fannoni daban-daban dangane da batutuwa iri-iri a duk fadin duniya. Ana iya amfani da sunayensu ko kalma guda a fannin kwarewar da ake bukatar taimako. Akwai kuma takaitaccen tarihin su da hotuna. Za’a iya tuntubar su kai tsaye bayan an cika wasu takarkadu a shafin.
Women Plus: Wannan kungiyar ma ta mata ce. Ya kunshi mata sama da 750 wadanda suka zabi kansu a fannin fasaha ko kuma abin da suka kira “tech experts” kwararru a fannin fasaha. Sunayen na shirye daki-daki a fannonin da ake bukata.
Expertfile: Wannan ya kunshi kwararru a batutuwa fiye da 25,000, kuma yana samun taimako wajen rarrabawa daga hadakar da ya kulla da kamfanin dillanci labarai na Associated Press.
The China – Africa Project/ Shirin Hadin Gwiwa na China da Afirka – Yana dauke da sunayen kwararrun da suka iya sharhi kan kowane bangare na dangantakar da ke tsakanin China da Afirka
ProfNet – yana karkashin jagorancin kamfanin PR Newswire kuma kyauta ne ga duk dan jaridan da ya yi rajista.
Finding Experts using the Internet 2018/ Samun kwararru ta hanyar amfani da yanar gizo 2018 – Babban kundi na kwararru wanda Marcus P Zillman ya hada wa LLRX wato bayanai na shari’a da fasaha wa kwararru a fanin shari’a. A shekarar 1996 Edita kuma mawallafiya Sabrina I. Pacifici ta girka kamfanin da ake kira LLRX.com
The Conversation Research and Expert Database/ Bincike da kundin bayanan kwararru na dandalin tattaunawar The Conversation: Shafin ya wallafa sunayen marubutan da suka taba rubutu a shafin The Conversation, wadda “kafa ce mai zaman kanta ta wallafa labarai da ra’ayoyi daga al’ummar manazarta da masu bincike, kai tsaye zuwa ga al’umma.”
Help a Reporter Out/ Taimaki dan jarida (HARO) mallakar kamfanin Cision ne wanda kamfanin bayanan sirrin kafofin yada labarai ne da ke da mazaunin shi a birnin Chicago a Amirka. Wannan tallafi kyauta ne wa duk wanda ya yi rajista kuma yana bai wa kwararrun manema labaran da ba su yi rajista ba damar aikar da korafi a rubuce, wanda ke bayyana labarinsu a takaice, abin da suke bukata da wa’adin shi. Editocin HARO za su tantance korafin su turawa majiyoyi ko wakilansu da ke aiki da su. Wadanda ke sha’awa sai su bayyana wa dan jaridan da ya rubuto korafin, wanda kuma zai iya sakaya sunansa. A cewar kamfanin, ‘yan jarida 55,000 da majiyoyi 800,000 suka yi rajista da su. Dukkansu kuma na da adireshin email.
Manhajojin Google Scholar da Microsoft Academic kundin bayanai ne da ke baiwa masu bincike cikakken jerin kasidun da manazarta ko kwarru a fanin illimi suka wallafa, wadanda za’a iya ganowa a shafin batun da suka tabo. Za’a iya amfani da kwanan wata da adadin mutanen da suka yi amfani da rubutun domin gano irin kwararrun da suka dace da abin da dan jaridan ke bukata. Wasu daga cikin shafukan kwararrun sun bayyana takaitaccen tarihinsu da kasidun da suka wallafa, wadanda ke alaka da su, fannonin nazarin, wadanda suka yi rubutun da su da adireshin shafin yanar-gizon su. Kadan daga cikin ayyukansu ana iya samu ta PDF ko kuma kai tsaye daga adireshinsu na yanar gizo. Duk wanda ya yi rajista da Google scholar zai iya samun email alert wadda hanya ce da ke sanar da duk sadda aka sami sabon kasida a fanin da suke sha’awa ta email.
Shoeleather, kundin bayanan Amirka ne da aka fara a 2018 don gano marubutan da ba suwa zama a biranen da ke da manyan kafofin yada labarai kamar New York, Los Angeles, Washington D.C.; da San Francisco, amma kuma a yankunan da suka fizo suna da kwarewa sosai kuma a shirye suke su bayar da nasu labaran.
Wani bayani mai kyaun gaske na yadda za’a iya samun majiyoyi a yi amfani da su yadda ya kamata sannan a kare su ya na babi na shidda a littafin bincike a aikin jarida ko kuma The Investigative Journalism Manual a turance, wanda shiri ne da aka yi a 2010 a karkashin shirye-shiryen kafofin yada labarai na duniya a karkashin ayyukan gidauniyar Konrad Adenauer.
Kuna da wanda kuke so ku kara? Rubuto mana a GIJN