Bayanai a aikin Jarida: Samun Bayanai – Yin Amfani da dokokin da suka bayar da damar amfani da bayanan gwamnati
Mahukuntan gwamnati yawancin sun a da hanyar da ke taimakawa ‘yan jarida da ma al’umma baki daya wajen samun bayanai. Daga kasa, akwai kadan daga cikin wasu batutuwan da za su taimaka wajen fahimtar dokokin da su ka shafi bayanan gwamnati a inda ku ke, da ma yadda za su taimaka mu ku wajen rubuta wasikun neman bayanan,
The National Freedom of Information Coalition ko kuma Hadakar ‘Yancin samun bayanai na kasa, wata kungiya mai zaman kanta ne a Amurka da ke da shawarwari dangane da Dokokin ‘Yancin Samun Bayanai na Kasa da Kasa wanda aka fi sani da FOI a shafin su tare da bayanai kan dokokin kwace jiha.
Reporters Committee for Freedom of the Press/ Kwamitin masu daukan labarai dangane da ‘yancin walwalar ‘yan jarida – Budaddiyar jagorar gwamnati (An sabunta 2019) na dauke da bayanai daki-daki dangane da dokokin da suka tanadar da walwalar samun bayanai zuwa rukunnai daban-daban wadanda suka hada da wanda zai iya neman bayanan da suke samun goyon bayan dokar ta FOI abun da ake kira bayanan gwamnati, yadda ake daukaka korafi da sauransu. Wannan kuma ya hada da bayanan da suka danganci samun irin bayanan da aka ajiye a yanar gizo.
Society for Professional Journalists FOI for Pros/ Kungiyar kwararrun ‘yan Jarida – Wadannan suna fayyace yadda ake neman bayanai bisa tanadin FOI, daga fahimtar dokar da ake amfani da ita, zuwa irin kalmomin da za’a yi amfani da su da kuma yadda za’a daukaka korafi ko da an hana mutun samun bayanan da ya bukata.
How to get a faster FOIA response/Hanyoyin samun amsa ga bukatar FOIA da gaggawa – Shawarwarin samun amsa daga mahukuntan da ba za su amsa tambayar ga na samun bayanai ba. Muckrock su ka rubuta