Bayanai a aikin Jarida: Farawa – Litattafai
Read this article in
Aikin jaridan da ke mayar da hankalin kan bayanan da ake tattarowa daga yanar gizo batu ne da ke sauyawa kullun. Dan haka ne GIJN ke sabunta bayanan da ke shafukanta a kai-a kai.
A babban taron GIJN19 da ya gudana a birnin Hamburg, mahalarta sun saurari kasidar da aka yi wa taken “Aikin jaridan da ake yayi, daga masu amfani da na’urori masu illimi zuwa sabbin dabaru”, wanda Sarah Cohen daga jami’ar jihar Arizona, Brant Houston daga jami’Ar Illinois da kuma Jennifer LaFleur daga jami’ar Amirka suka gabatar.
Haka nan kuma, a taron na GIJC19, malamin da ke koyar da aikin jarida a jami’ar Columbia, farfesa Gianna ta tattauna kan aikin jarida mai samun lambar yabo da yadda suka yi: Shekarar matattu, kiwon lafiya da miyagun laifuka.
Domin samun Karin bayani dangane da aikin jaridan da ke mai da fifiko kan bayanai, a duba wadannan littattafan da jagorori a wannan fannin daga ko’ina a duniya suka rubuta, wadanda da yawa daga cikin litattafan kyauta ne a yanar gizo.
Ayyukan da suka yi fice wajen aiki da bayanai a aikin jarida (wanda aka wallafa 2017) na dauke da shawarwari da dakunan labaran da ke fara amfani da data journalism za su iya amfani da shi. Kuang Keng Kuek Ser ne ya rubuta wa gidauniyar zuba jari domin bunkasa kafafofin yada labarai.
The Curious Journalist’s Guide to Data Journalism – Jagorar dan jarida mai neman zurfafa fahimtar data journalism (2016), wanda dan jarida mazaunin Amirka Jonathan Stray ya rubuta ya bayar da kyakyawar bayani kan yadda ya kamata a rika tunanin bayanai: “Wannan ba “yadda ya kamata a yi amfani da bayanai ba ne,” illa “Yadda bayanai ke aiki.””
Data for Journalists- Bayanai dan ‘yan Jarida: Jagora wajen rubuta rahotanni tare da tallafin na’ura mai kwakwalwa, (Karo na 5, 2018) farfesa a fannin jarida Brant Houston ya rubuta. Wannan na kunshe da bayanai daki-daki kan yadda ya kamata a yi nazarin bayanai. Yana ma hade da misalan da za’a iya amfani da su wajen ganin salon nazarin a zahiri. (Akwai na saidawa ga mai sha’awa)
The Data Journalism Handbook 2 (2019) Littafin Jagora na Bayanai dan aikin Jarida. An yi bita an fadada wannan ne daga Littafin jagora na farko wanda aka wallafa a 2012. Litattafan biyu suna bayar da mahimman kanu dangane da da bayanai na aikin jarida. Jonathan Gray da Liliana Bounegru ne editocin da suka yi aiki a kai daga Public Data Lab. Editocin sun sami gudunmawar kasidu daga jagorori a fanin bayanan wadanda ke nahiyar Turai. Ana iya karantawa a harsuna da dama wadanda suka hada da Arabic (PDF), Azerbaijan, Chinese, Turanci (PDF) , Faransanci, Girkanci, Japanianci , Rashanci , Spanianci da Ukranianci.
The Data Journalist (2017) Dan jarida mai amfani da bayanai: Wannan yana bayar da gabatarwa mai kyau daga manyan ‘yan jaridan Canada guda biyum Fred Vallace-Jones da David McKie. Akwai darussa a yanar gizo. (Duk mai sha’awa na iya saye ta hanyar yanar gizo)
Data Literacy: A User’s Guide – Illimin Bayanai: Jagorar Mai Amfani da Bayanan (2015) babban farfesan illimin jarida mazaunin Amirka, David Herzog ya yi bayani daki-daki dangane da hanyoyin amfani da bayanai. Herzog ya ma hada har da hanyoyin samun bayanan, yadda ya kamata a tantance, a tsabtace a kuma yi nazarin su.” (su ma ana iya saye)
Facts are sacred – Bayanan Gaskiya na da tsarki – tsohon ma’aikacin jaridar The Guardian Simon Rogers ya rubuta, inda ya bayar da kyawawan misalai daga bayanan da ke taskar blog din The Guardian.
Getting Started with Data Journalism – Fara amfani da Data Journalism (2016) ‘yar jarida mai zama a Burtaniya Claire Miller ta bayar da shawarwari masu taimakon gaske dangane da batun musamman wajen samun irin bayanan da ake bukata, tsabatace su da kuma gano labaran da ke cikin bayanan. (Ana iya saye)
How to Lie with Statistics – Yadda ake Karya da Alkaluma – Wannan littafin wanda Darrel Huff ya rubuta kyakyawar misali ne na yadda za’a iya yin kuskure wajen amfani da alkaluma a cikin labarai. An fara wallafa wannan littafin ne a 1954 amma har yau ana koyi da darussan da ya gabatar. (Ana iya saye)
John Allen Paulos – Malami ko kuma farfesa a jami’ar Temple ya rubuta litattafai da dama ya kuma yi sharhi kan amfani da alkaluma a al’umma da labarai. (Ana iya saye)
Numbers in The Newsroom – Alkaluma a dakin labarai (2014) Littafi ne mai amfani wajen rubutu da kuma amfani da alkaluma daga jerin litattafai masu bai wa editoci da masu dauko rahotanni bayani dangane da bincike a aikin jarida. ‘Yar jarida Sarah Cohen wadda ke zama a Amirka ce ta rubuta. Duk wani mai amfani da alkaluma wajen rubuta labarai da rahotanni yana bukatar wannan littafin.
Precision Journalism: a Reporter’s introduction to Social Science Methods/ Aikin jarida mai daidaito : gabatar da mai daukan rahotanni ga hanyoyin illimin zamantakewa (2002). Duk wanda ke sha’awan shiga Data Journalism na bukatar wannan littafin. Daya daga cikin wadanda suka yi jagora wajen amfani da alkaluma da illimin zamantakewa wajen kawo rahotanni, Philip Meyer ne ya rubuta wannan. An ma kaddamar da lambar yabo a sunan mazaunin Amirkan, dan karrama masu dauko rahotanni wadanda ke bincike mai zurfi a aikin jarida da editoci masu amfani da bayanai (musamman alkaluma)