Samun gudunmawa daga jama’a: Mahimman karatu (Crowdfunding: Essential Reading)
Binciken GIJN na bayar da shawarwari dangane da ya kamata a tsara a kuma aiwatar da gangamin neman kudi daga jama’a, sunayen shafukan kasa da na yankuna da ake aiwatar da irin wannan gangamin da ma irin dabaru da abubuwan da ya kamata a yi amfani da su.
A babban tarn GIJN wanda aka gudane a birnin Hamburg Tamas Bodoky na Atlastszo da ke kasar Hungary, ya fadada wannan a karkashin rukunoni bakwai (kuna iya ganin cikakken bayani a nan tipsheet)
- Samar da hanyoyi da dandaloli daban-daban na karbar gudunmawa
- Mayar da hankali wajen samun gudunmawa da yawa daga wadanda za su rika bayar da kadan amma a kai-a kai.
- A kasashen da karkashin mulkin da ba shi da sassauci, masu bayar da gudunmawa sun fi so a sakaya sunayensu
- Kayayyakin kyauta ko saidawa masu dauke da tambarin kamfanin/kafar yada labaran suna taimakawa wajen samun masu bayar da gudunmawa
- Talla na da mahimmancin gaske
- A yi amfani da abubuwa masu kayatarwa da ban dariya wajen shirya gangamin karbar gudunmawar daga jama’a
- Auna abin da ke aiki da wanda ba ya yi
Domin karin bayani duba shafin GIJN
Samun gudunmawar jama’a domin ‘yan jarida
- Shawarwari dangane da samun gudunmawa daga jama’a
- Shafukan samun tallafin jama’a a duniya baki daya
- Shafukan yankuna
- Shawarwari da darussa
- Ababen shirya gangamin samun gudunmawa daga jama’a na kyauta
Abubuwan da ya dace ku yi kafin ku fara neman tallafi daga jama’a Cibiyar ‘yan Jaridan Turai