Accessibility Settings

color options

monochrome muted color dark

reading tools

isolation ruler

Albari

Topics

Fadada amfani da Soshiyal Mediya a Dakunan Labarai: Jagora kan rarrabawa da ma’amala da masu sauraro

Read this article in

Image: Shutterstock

Idan kuna karanta wannan akwai yiwuwar cewa kun riga kun fahimci mahimmancin masu sauraronku ko karanta labaranku. Mai yiwuwa ba ku bukata na in fada mu ku cewa fahimtar masu sauraronku shi ne sanin irin shafukan da suke ziyarta idan suka shiga intanet kuma irin labaran da suke so shi ma yana da mahimmanci ga dorewar kowace irin kafar yada labarai. Duk da haka, ko da ma kun san wadannan abubuwan dangane da masu sauraronku da karanta ku akwai karin abubuwan da za’a koya a kuma yi tunani a kai. Wannan jagora ce ta kungiyoyin da ke kokarin inganta fahimtarsu ta wadanda ke karanta su a intanet da wadanda ke neman jan ra’ayin sabbin ma’abota.

Yayin da kuke karanta wadannan shawarwarin, babban abun dauka shi ne: Idan kuna so ku yi nasara, ku rika mayar da hankali kan yadda ku rarraba ayyukanku kamar yadda ku ke daukan lokaci ku kirkiro ku rubuta. Kuna iya rubuta labari mai sosa rai ko tasiri amma kuma idan kuka nade hannu kuka zauna kuna sa ran masu karatu za su zo shafinku ne kawai su karanta, ke nan kun bata lokacinku. Domin shiga hayaniyar shafukan intanet, ya kamata ku mayar da hankali wajen inganta dangantakar da ke tsakaninku da wadanda ke karanta labaranku dan su tuna da sunanku su cigaba da dawowa.

Su Waye Masu Sauraronku? Wane Dandali Za Ku Iya Amfani da? 

Tun kafin ku fara yin wani abu, ya kamata ku yanke shawarar irin wadanda ku ke so su karanta labaran ku. Shin kuna kokarin samun masu sauraron da ba su cancanta ba ne? kuna kokarin samun matasa ne ko dattawa?

Idan na tambayi kafofin yada labarai irin mutanen da su ke fatan samu, suna yawan cewa, “Oh muna so mu kai ga kowa ne! Muna son masu karatu da yawa.” Amma wajibi ne kafofi su sanya irin burin da za su iya cimma su kuma fayyace wadanda suke ganin za su ci moriyar irin batutuwan da za su wallafa.

Da zarar kun tabbatar da wadannan abubuwan dangane da wadanda za su karanta labaraku za ku iya yanke shawara kan inda kuke so a raba bayanan. Akwai wurare da yawa inda za’a iya wallafa ayyukanku, amma ba za ku iya kasancewa a dukkansu ba, yin haka ma ba zai yi kyau ba. Zaben wadanda suka fi dacewa da abin da ku ke rubutawa, wadanda ke karantawa da wurin da kuke so ku yi aiki a duniya na da mahimmanci.

Wani abu kuma da yawancin kafafen yada labarai kan tambaya shi ne: Shin mu sa kanmu a wannan manhajan da ke tashe? Kafin ku shiga doki ku yi rajista a shafukan soshiya mediya 50 a lokaci guda, ku yi tunanin wannan: Shafukan da mutane ke amfani da shi zai canza ko da yaushe, amma kuma abin da za ku sa zai kasance yadda ya ke. Abin da wannan ke nufi shi ne babu wani riba a bin duk wata manhaja mai kyalkyali da ta fito idan dai ba abin da masu karanta ku ke sib a ne. Alal misali akwai lokacin da kowa ya yi tunanin wai snapchat ce makomar soshiyal mediya sa’annan kuma kusan kowa ya fara amfani da Facebook Live amma a kwana a tashi duka biyun ba su da irin tasirin da aka zaci za su yi.

Ba wai wannan na nufin ka da a yi amfani da wadannan shafukan ba ne. Amma domin yin amfani da lokacinku yadda ya kamata, ya fi dacewa a mayar da hankali wajen inganta abubuwan da dama kuka saba amfani da su, Misali samar da wasikar labarai wanda za’a rika aikawa wadanda suka dade suna karanta jaridar ya fi bude sabon shafi a Instagram.

Abin da wannan ke fada shi ne ku yi amfani da shafukan da wadanda ku ke so su rika karanta ku, su ke amfani da shi a kasashen da ku ke. Abin da ya dace da kafar yada labarai a Australia ba zai dace da kafar yada labarai a Senegal ba. Idan masu karanta shafinku na Vietnam kuma ba wanda ke amfani da Tiwita, to kuwa ba ku bukatar Tiwita, Idan kuna so matasa a Italy su karanta labaranku kuma matasan Italy ba su amfani da facebook ba ku bukatar Facebook. Idan kafarku ba ta da kudi wannan matakin na da mahimmanci a gare ku.

Sabbin shafuka da yawa za su zo kowani wata ko shekara. Ya kamata ku rika bincikensu, ku ga ko suna habaka ko ba su yi musamman a yankunan ku. Idan har ku ka ga cewa mutane da yawa na amfani da shi a kasashen da ku ke so ku kai labaran to kuwa zai yi kyau ku sanya ido ku gani. Haka nan kuma, ka da ku rika la’akari da irin abubuwan da ake sanyawa a shafuka wajen yanke shawara. A maimakon haka ku duba irin hanyoyin sadarwar da suke amfani da shi. Ni na kan yi nawa kamar haka:

1. Hanya guda ta Sadarwa

Idan kuna watsa labarai ne ga jama’a wannan na nufin yawancin maganan daga gefe daya ne, dan haka ba ku sa ran samun martani ko kuma ma rabawa. A irin wadannan shafukan, ku bai wa masu karantawa damar mayar da martani ko turo sako. Ku kuma yi magana da masu karatu cikin aminci ba tare da wani boye-boye ba. To amma matsalar dai ita ce babu ma’amala ta kai tsaye a nan take. Wasu daga cikin manhajojin da ke yin haka sun hada da

  • Telegram
  • WhatsApp
  • Newsletter

2. Gefe daya ke magana amma jama’a na da damar tofa albarkacin bakinsu.

Kuna raba aikinku da masu sauraro amma martanin da za ku ji/gani shi ne idan sun yi rubutu a karkashin bidiyon. Wadansu daga cikin abubuwan da akan rubuta na iya tasiri a kan ra’ayoyin mutanen da ke zuwa shafin ku. Dan haka idan har ba za ku karanta ku bayar da amsa nan take ba, yana da mahimmanci ku rika dubawa kuna ganin abin da mutane ke fada. Misalan irin wadannan kafofin sun hada da:

  • Hotunan Instagram
  • Bidiyo/YouTube
  • LinkedIn

3. Tattaunawa gaba da gaba tsakanin bangarori biyu

Wannan ya tanadi rubutu a kan intanet da samun amsa nan take. A kan wadannan shafukan, mutun zai ji kamar ana tattaunawa kai tsaye ne, kuma masu sauraro/karatu na sa ran samun martani nan da nan. Wadannan sun hada da:

    • Twitter
    • Instagram Live
    • Kungiyoyin WhatsApp

Image: Shutterstock

Shawarar da na fi bayarwa shi ne ku tantance ko kafar yada labaranku za ta iya sanya ido kan tattaunawar; misali kuna da kudin da za ku iya biyan edita na soshiyal mediya? Ko wanda zai rika kula da masu sauraro/karatu? Idan haka ne, zai yi kyau ku bude shafi a wadannan fannonin uku (one-way broadcasts, one-way conversation da two-way converstion) Ku sami shafi a Tiwita da Instagram da ake duba martanonin mutane. Amma idan ba ku da kudi, sai ku mayar da hankali kan wasikun labarai da Telegram.

Burin kowani shafi daban ne, kuma ba wanda zai amfana idan har ba’a yi amfani da shi yadda ya kamata ba. Misali, ku yi amfani da Tiwita yadda aka tsara tun farko: mayar da martani ga masu sauraro/kallo/karanta ku da kuma tattaunawa da su. Ka da ku rika magana ku kadai domin ba RSS feed ba ne kuma yin amfani da shi ta haka ba zai ja ra’ayin ma’abotan kafarku ba.

Baya ga haka, kada ku yi tunanin wai tattaunawa ta kai tsaye da ma’abota shafukanku ne kadai hanyar fahimtarsu, kuna iya fahimtarsu ma ko a kafar da watsa labarai da shirye-shirye kadai ku ke yi. Misali a wasikun labarai yanzu, ana iya latsawa a duba a ga batutuwan da suka fi daukar hankali, labaran da aka fi karantawa, da ma yankin da ake bude wadannan batutuwa.

Wani batu mai mahimmanci kuma wajen zaban shafi shi ne samun damar shiga shafin. Misali idan an fi amfani da Facebook a yankin da ku ke aiki amma kuma duk sadda kuka wallafa abu ana cirewa watakila zai fiye muku ku mayar da hankali kan wasikun labarai da Telegram. Ba wai hanaku izinin wallafa abu a shafin zai tsaya nan ba ne amma zai taimaka muku wajen duba ire-iren zabin da kuke da shi wajen biyan bukatar masu sauraronku

Bacin samun damar shiga ana kuma bukatar a ga ko za’a iya biya. Misali idan har kuna so ku kai labaran ga al’ummomin masu karamin karfi ne inda basu da layukan intanet masiu karfi. A maimakon bude tasha a YouTube da za’a dauki lokaci ana kokarin sa bidiyo gara an rika aikar mu su da sakon text. A kuma gaji shafuka da manhajoji da ke bukatar biya domin idan ma’abota suka shiga suka ga sai sun biya wata kila ba za su so ba.

Daga kasa jadawali ne na kafofin sadarwar da aka fi amfani da su da yadda kafofin yada labarai ke amfani da su, da kuma adiresoshin zuwa shafukan da ke karin bayani dangane da yadda ake amfani da su. Duk wadannan kyauta ne amma duk inda kuka ga alamar $ to ana biya.

Platform/ Shafi ko Dandali Note/Tips/Bayani
WhatsApp –watsa labarai/kungiyoyi/Kasuwanci ($)
Tiwita
Facebook – Shafi/Kungiya/ Live
Telegram
Mailchimp
Instagram – Stories / Live
YouTube
Text Messaging / Sakon Text
TikTok

Hanyoyi da daman a gabatar da labarai

Idan ya zo ga shafukan da suka fi dacewa da kafar yada labaranku, babu wata amsa ta kai tsaya. Ya danganta ne da inda ku ke a duniya, yawan ma’aikatan da ku ke da si da kuma abin da kuka sani game da masu sauraron ku. Ku dai tuna: Ka da ku wahalar da kanku. Ku yi tunani da kyau kan abubuwan da ya kamata su dauki hankalinku da wanda ba dole ba ne sai kun yi.

Dan haka yanzu misali mu dauka cewa ba ku san wadanda ke sauraronku ko karanta labaranku ba da shafukan da za su fi taimaka muku wajen samun su a inda ku ke. Yanzu ne za mu bayyana muku yadda za ku iya gabatar da ayyukanku.

Kowani shafi ko dandali yana da abin da ya ke bayarwa, kuma yayin da akan kai ga gane kowani shafi da yadda ya ke aiki, da yawa na da suffofi daban-daban. Misali Instagram na da kyau wajen hotuna da bayanan da za’a iya sauraro kamar a rediyo. A Tiwita, ba’a bukatar take kawai sai dai a raba adireshin sakon da ake so a gabatar; ana kuma iya amfani da shi dan bayar da labari, misali ana iya wallafa abubuwa goma a jere suna bin juna a abin da ake kira “thread” da turanci. Telegram na da kyau wajen gabatar da kanun labarai kuma ana iya hadawa da bidiyo.

Duk da cewa in aba ku shawarar raba aikin ku, wannan ba yana nufin idan kuna da wani babban binciken da zai dauki hankali, ku dauka ku tura shi a TikTok ba. Amma kowani labari da ku ke da shi, ku yi tunani da kyau dangane da irin zabin da kuke da shi na sanya labarin a intanet kafin ku yanke shawara. Ku baiwa jama’a zabin zuwa shafinku su karanta cikakken labarin amma kuma ku dauke mahimman kanun labarin ku tallata shi a kafofin sadarwa dan mutane da yawa su sami labarin.

Ga wadansu abubuwan da za ku iya amfani da su wajen yanke shawara kan yadda za ku wallafa labarin da kuka rubuta da kanku.

  • Text: Yadda kuka rage tsawon labarin, ku ka fayyace, ku ka kuma tsara kuka rubuta duk ya danganci ra’ayinku da abin da kuke so ku yi
  • Audio: Labaran da ake sauraro ba podcast ne kadai ba, kuna iya dauko muryoyi daga tattaunawar da aka yi ku wallafa a tiwita. Ku na iya hada wadannan muryoyin da tsokaci ko kuma zanen hotuna irin na grafiks sai a hada da muryoyi a sa a Facebook
  • Image: Wato hotuna, ana iya amfani da hotuna ko kuma zanen grafiks- wata kila akwai wadanda suka fi son sauraro ko karanta labarai hade da hotuna
  • Video: Gajerun bidiyoyi masu bayar da bayanai

Idan kuna neman yadda za ku raba labarai, ba kafafen yada labarai ‘yan uwanku kadai za ku duba ba, akwai misalan hanyoyi masu jan hankali da yawa kama daga kungiyoyi masu zaman kansu zuwa manyan kamfanoni.

Yadda ake Auna tasirin Aikin da ku ke yi 

Image: Shutterstock

Awo na da mahimmanci wajen fahimtan ma’abotan shafin. Duk da haka zai fi ma’ana idan aka bayyana burin da ake so a cimma. Dan haka kafin ku fara auna mutane nawa su ka ziyarci shafin ko su ka latsa alamar amincewa da aikinku wato like ko ma dai suka yi tsaokaci a kai, dole ku fayyace abin da kafarku ta bayyana a matsayin nasara. Misali idan ba ku da girma sosai, burinku na cimma wani adadi na masu sauraro ne ko kuma kara yawan wadanda ke ma’amala da shafin zuwa 3000? Idan kuna da girma kuna son wadanda suke amfani da shafin su cigaba da dawowa ne ko kuma kuna so ku sami sabbin mambobi? Babu kamfanoni biyu da za su kasasnce da buri iri daya, dan haka ya kamata ku fayyace na ku.

Dangane da yawan mutane a shafin ga wata ‘yar shawara: Idan ya zo batun awo, akwai hanyoyi da daman a fahimtar ma’abotan shafukanku. Misali, kuna iya ganin tsawon lokacin da suka yi a shafinku wanda zai iya fada muku ko sun ji dadin karatun da suka yi ko ba su ji ba. Sa’anan yayin da samun mutane da shafin na da kyau, ba lallai ne ya kasance wai labaran sun yi tasiri ko sun dauki hankalin wadanda su ka ziyarci shafin ba. Akwai abubuwa da yawa da za’a iya yi dan inganta dangantaka da wadanda ke karanta labaranku ta yadda za su rika zuwa ko yaushe. (Domin samun karin bayani kan awo ku duba shafin Beyond Metrics: A Beginner’s Guide to Metrics that Matter.)

Idan kuna da kayayyakin awo da kudin da zai taimaka wajen samar da kayan a cikin gida, wannan na da kyau kwarai! Amma idan akwai tsada kuma ba ku da shi, akwai abubuwa da yawa da za su iya taimakawa. Da yawa kyauta ne, wasu kuma suna baiwa kungiyoyi masu zaman kansu ragi na musamman. A yayinda wasu kuma su ke bayar da wani bangare kyauta. Ga wadansu shawarwari

Manhaja Abin da ya ke yi Farashi?
Buffer Ana amfani da shi dan sa labarai a kafofin sadarwa a lokacin da ake so. Ana kuma iya auna sakamakon a kuma yi ma’amala da alummar a shafukan Tiwita, Facebook, Instagram, Instagram stories, da pintrest Akwai kudi amma kungiyoyi masu zaman kansu na iya samun rangwame.
Later Wannan na taimakawa wajen shiri, wallafawa da auna sakamakon labaran Instagram da wadanda aka sanya a sauran kafofin sadarwa Akwai
Sprout social Wannan na taimakawa wajen inganta dangantakar shafin da sauran dandaloli a soshiyal mediya akwai
Mailchimp Wannan na da abubuwa da yawa, ana iya fahimtar ma’abotan shafin, ku na iya auna kokarin ku, inganta kasuwanci da ma kwatanta inganci manhajoji domin sanin wanda ya fi dacewa da ku Akwai amma akwai kuma wasu bangarorin da za’a iya amfani da su a kyauta
Twitter Analytics Twitter kan bayar da manhajan awon ta amma na tsawon wata guda kacal Babu
Google Analytics Google na bayar da shawarwari da yawa Babu
Facebook Analytics Facebook na taimakawa da nazarin shafuka kyauta idan kuka sanya shafin a manhajan Babu
Chartbeat Wannan na yin awo kai tsaye ya bayar da shawarwarin inganta ma’amala da masu sauraro, yanke shawara kan labaran da za’a dauka ya kuma kara yawan masu karatu Akwai
BuzzSumo Wannan na taimakon mutane su gano batun da ya fi daukar hankali ko kuma shafin da ke tashe. Akwai, amma kuma akwai bangarorin da za’a iya amfani da su a kyauta

Daga irga yawan mutanen da suka karanta labaran twitter zuwa bangaren duniyan da masu karanta labaran su ka fito. Wadannan abubuwa suna bayar da hanyoyin auna duk shafukan sada zumunta ban a ku kadia ba.

Duk da haka, kuna iya amfani da su yadda ku ke so domin ku cimma na ku burin. Kuna iya shiga kungiyoyin Facebook da ke tattauna sauye-sauyen da ake wa shafukan sada zumunta misaki wannan mai suna Social Media Group na da amfani

Wasu abubuwan da ya kamata a tuna

Ga abubuwa ukun da a ra’ayi na su ke da mahimmanci

  1. Ka da ku sami editan soshiyal media bayan ya wallafa labari ku ce “wannan labarin na da kyaun gaske yana bukatar mutane su gani” ya tabbatar mutane da yawa sun gani. Ba zai iya yin almara ba, idan har labarin yana da kyau kuna so mutane su gani kamata ya yi a tattauna da shi tun farko kafin a wallafa.
  2. Ka da ku ce kuna son rahoto ya yadu cikin hanzari wato ya je “viral” wannan ba wanda ya san sadda irin wannan zai faru. Akwai dai irin matakan da ya kamata a dauka wajen inganta labarin ya dauki hankali amma kuma babu tabbas
  3. Kanu labarai da hotuna na da mahimmanci a labari. Idan aka sa masu kayatarwa lallai za su dauki hankalin jama’a

Rossalyn Warren direkta ce a fannin dijital a GIJN. Ita kuma ‘yar jarida ce da ke zama Landan wadda ta ke bayar da gudunmawa ga kafafen yada labarai irinsi The Guardian, CNN, BBC da sauransu. Ta kuma taba dauko rahotanni wa BuzzFeed.

Republish our articles for free, online or in print, under a Creative Commons license.

Republish this article


Material from GIJN’s website is generally available for republication under a Creative Commons Attribution-NonCommercial 4.0 International license. Images usually are published under a different license, so we advise you to use alternatives or contact us regarding permission. Here are our full terms for republication. You must credit the author, link to the original story, and name GIJN as the first publisher. For any queries or to send us a courtesy republication note, write to hello@gijn.org.