Bayanai a aikin Jarida: Nazarin Bayanai – SQL
Ana yawan amfani da SQL idan ana aiki da manhajojin ajiye bayanai. Yana da mahimmancin gaske a lokutan da ake amfani da bayanai masu yawan gaske wadanda Excel ba zai iya dazka ba domin yana iya hada bayanai daban-daban ya yi nazarinsu. Ana amfani da irinsu da dama a dakunan labarai, wadanda su ka hada da Postgresql da DB Browser SQLite.
Ga wasu shawarwari kan yadda za’a iya amfani da su.
Ga wata kasida mai kashi kashi uku kan yadda ake amfani da QL, an gabatar da kasidar yayin babban taron GIJN 2019. Jodi Upton daga jami’ar Syracuse da ‘yar jarida mai bincike mai zurfi Crina Boros da Helena Bengtsson daga gidan talbijin na Sveriges da ke Sweden su ka ributa. SQL (Part 1),SQL (Part 2), SQL (Part 3).
Excel to SQL Crosswalk (2017) wanda MaryJo Webster ta rubuta bayanai ne da ke nuna kamanceceniyar da ke tsakanin Excel da SQL dan ‘yan jaridan da ke so su fara amfani da SQL kuma sun riga sun dan san wani abu a kan Excel.
Introduction to SQL for Data Journalism/ Gabatarwa ga SQL ga masu amfani da bayanai dan aikin jarida (2014) wannan wani bangare ne na manhajan koyarwar a ajin Dan Nguyen, a jami’ar Stanford. Ya bayar da bayanai dangane da SQL, ta yin amfani da hotunan shafukan, misalai na koyo da adiresoshin shafuka da kuma amsoshi ga tambayoyin da aka fi yi. Ya kuma kara da wasu darussan da ke bayani a kan abubuwan da suka fi wannan wahala.
Khan Academy/ Makarantar Khan Ya na da darassin da ke bayar da gabatarwa ga SQL, darassin na cikin bidiyo kuma ya na bayar da bayanai daga mafi sauki zuwa mafi wahala.
Practical SQL (2018) wanda Anthony De Barros ya rubuta, bayanai ne dangane da manhajojin SQL da wadanda suka fi shi. Amma an yi bayanan yadda kowa zai gane. DeBarros ya dade yana irin wannan aikin. A yanzu haka shi edita ne na labaran irin wadannan bayanan a Washington, D.C. a jaridar Wall Street Journal (Ana iya saye)
Udemy ya na da darussa kan SQL kyauta a yanar gizo-gizo