Bayanai a aikin Jarida: Nazarin Bayanai – Python
Python (wanda ke nufin mesa) shi ne wanda ‘yan jarida su ka fi amfani da shi kuma yana da amfani wajen neman bayanai a shafuka, da tsabtace su da ma yin nazarin su. Ga wasu daga cikin wuraren da za’a iya koyon amfani da python.
A Byte of Python – wannan littafi ne a yanar gizo wanda aka rubuta shi musamman dan koyon python. An rubuta shi ne kuma dan wadanda ba su riga sun lakanci amfani da shi ba yana kuma zuwa da inda za’a iya ajiye abubuwa a shafin GitHub tare da darussan da za’a iya koyo da su.
Shafin datajournalism.com na bayar da darassin gabatarwa dangane da Python wa ‘yan jaridan da ke amfani da Jupyter Notebook. Winny de Jong wata ‘yar jarida a Holland c eke koyar da darussan.
First Python Notebook wannan ma jagora ce ga masu koyon amfani da Python wanda tsohon edita kuma dan jarida da ke aiki da jaridar Los Angeles Times Ben Welsh ya rubuta.
Google’s Python Class – Gabatarwa ce kan yadda ake amfani da Python da kuma umurnin yadda za’a iya hadawa a yi amfani da shi.
Learnpython.org – na da darussa a rubuce wadanda za’a iya yi a yanar gizo a shafin da ake kira Python Shell ba tare da an sauke bayanan ba. Batutuwan da ake koyarwa a nan sun fi na google yawa.
Learn Python 3 the Hard Way (2017) – wanda Zed Shaw ya rubuta gabatarwa ce ga coding da ke amfani da Python. Idan aka saya kai tsaye daga shafin marubucin, littafin kan zo da bidiyoyin da ke bayani dalla-dalla.