Accessibility Settings

color options

monochrome muted color dark

reading tools

isolation ruler

Bayanai a aikin Jarida: Nazarin Bayanai – Manhajan Lissafi (Analysing Data – Spreadsheets)

Yawancin lokuta manhajar lissafi ce makamar aiki na farko da ‘yan jarida kan koyi amfani da shi. Wannan na da mahimmanci waken tsabacewa da kuma yin nazarin bayanai. Microsoft Excel da Google Spreadsheets ne aka fi amfani da su. A kasa mun yi muku tanadi wadansu manhajojin da su ma za su taimaka muku wajen inganta fahimtanku na aiki da wadannan manhajoji

Data Journalism Training: Beginner Excel/Horaswa kan bayanai dan aikin jarida Wannan darasi ne da MaryJo Webster ta shirya wanda ke bayyana yadda ake shirya bayanan da za’a yi amfani da su a Excel. Ta kuma nuna wadansu daga cikin fasahohin da ake amfani da su cikin hotuna. Wannan darasin zai fi amfani ga wadanda suka amfani da babban Komfutar da ke kan teburi.

Cousera and edX su ma suna bayar da darussa kyauta a bidiyo akwai Excel domin kasuwanci, nazarin bayanai da sauransu, wadannan ba lallai dan aikin jarida ba ne amma kuma suna iya koyar da makaman aikin da za’a iya amfani da su wajen gudanar da aikin jarida.

Finding stories in spreadsheets/ Samo labarai cikin alkaluma ko manhajan lissafi (2016) Wanda dan jarida Paul Bradshaw ya rubuta yana bayar da bayani dalla-dalla ga ‘yan jaridan da ke neman fara aiki da irin wadannan bayanan. Yana bayar da shawarwari kan yadda dan jarida zai gane mene ne labari a cikin alkaluman da ke gabansa. (Ana iya saye)

GFCGlobal – Ya na gabatar da darussa kyauta kan manhajan lissafi na Excel inda yak e duba batutuwan da suka hada da gyarawa, da hotuna. Akwai jarabawa a karshen darasin

Mr Excel – Duk wata amsar da ake nema dangane da manhajan lissafi na Excel ana iya samu a nan. Bill Jelen ya na da shawarwari da dama tunda tun 1998 ya ke tara bayanai dangane da shi.

A Reporter’s Guide to Excel/Jagorar masu dauko rahotanni kan Excel (2016) Wannan na bayar da bayanai daki-daki tare da hotuna na yadda ake amfani da Excel a aikin jarida musamman yadda ake tsabtace alkaluma. Akwai kuma misalai wadanda za’a iya amfani da su wajen koyo.

Spreadsheets for Journalism/ manhajan lissafi dan aikin jarida (2019) Wannan takaitaccen bayani ne wanda dan jarida mazsaunin Amurka Brant Houstan ya rubuta dangane da yadda ake amfani da Excel wajen yin nazarin bayanai da alakaluma. Ya bayyana abubuwan da su ka fi dacewa da Excel da kuma yadda ake yin lissafi da shi.