Accessibility Settings

color options

monochrome muted color dark

reading tools

isolation ruler

Albari

Topics

Tips for Donors/ shawarwari ga masu bayar da tallafin kudi

Read this article in

Ba yau be masu tallafawa aikin jarida suka fara sha’awar labaran da su dadada wa jama’a ba. Jaridun da ke rayuwa kan tallafi kadai irinsu National Geographic da Mother Jones sun yi shekaru gommai ana karantawa. Gidauniyar farko da aka yi dan tallafawa bincike mai zurfi a aikin jarida an kafa ta ne a shekarar 1969 yayin da rediyon kyauta na jama’a a Amirka kuma ya bulla a 1971. Bayan yakin cacar baki, gwamnatocin yamma da gidauniyoyi sun tura billiyoyin dala zuwa kasashen waje domin abun da suka kira “bunkada kafafen yada labarai” wanda zai samar da kafofin yada labarai masu ‘yancin kansu a kasashen da suka daina amfani da salon gurguzu da kasashe masu tasowa.

Sai dai a ‘yan shekarun da suka gabata, da yadda shafukan yanar gizo suka rika daukar labaran karya wanda ya yi sanadiyyar koma bayan da aka samu dangane da ‘yancin fadan albarkacin baki, masu bayar da tallafi sun fara mayar da hankalinsu kan kamfanonin aikin jaridan da ke da ‘yancin kan su. Wannan labari mai dadi ne domin aikin jarida na gaske musamman ma bincike mai zurfi a aikin jarida na matukar bukatar taimako. Alhamdulillah kuma akwai rahotanni da dama da za su iya taimakawa wadanda ke da niyyar bayar da kudi wajen lakantar bayanan abubuwan da faruwa da fagen aikin jaridar a zahiri. Wadannan rahotanni sun duba batutuwan da suka danganci auna tasirin zuba jari a aikin jarida, aiki da kungiyoyin jarida da kuma yadda za’a zabi shirye-shiryen da suka dace.

Kuna iya fada mana idan akwai abubuwan da ku ka gs sun dace mu kara

Tallafawa kafafen yada labarai na duniya: Abin da ya kamata masu bayar da tallafi su sani dangane da bayyani, yayi da batutuwan da suka shafi fannin:  Wannan rahoron na shekarar 2019 Sarah Amour-Jones da Jessica Clark masu bayar da shawara a Media Impact Funders suka rubuta. Bincikensu ya “yi amfani da bayanai daga taswirar bayanan tallafin kafafen yada labarai, sakamakon binciken manyan kungiyoyin da ke tallafawa shirye-shiryen da ke da dangantaka da kafafen yada labarai a duniya, nazarin bayanai da rahotannin da aka riga aka yi da ma shawarwarin da kwararru suka bayar dangane da abubuwa daban-daban da suka shafi tallafawa kafofin yada labarai.

Mahimman kanu sun hada da:

 • Bayanan da ake da su dangane da tallafawa kafofin yada labarai da bukatar inganta hanyoyin samun bayanai
 • Ra’ayin masu bayar da tallafi dangane da tallafawa kafafen yada labarai da inda suke da damuwa.
 • Bukatar inganta matakan tsaro tsaknin masu kafafen yada labarai da masu tallafa mu su
 • Mahimmancin hadin kan yankuna wajen fadada inganta ‘yancin yada labarai da kafafen yada labarai masu sahihanci da nagarta
 • Kalubalen da kafafen yada labarai masu ‘yancin kan su ke fiskanta a India da Afirka
 • Tsari na musamman na tallafawa aikin jarida a Turai da sauransu.

Aikin Jarida da Fagen Samun Tallafi: Sabbin samfura da kawancen tabbatar da dorewa da bunkasar fagen: Sarah Amour-Jones mai bayar da shawara a kamfanin Media Impact Funders ce ta rubuta wannan rahoton a 2019 wanda ya rubuta yadda tallafi ke cigaba da taka rawar gani wajen tallafawa aikin jarida – Musamman a aikin bincike mai zurfi na cikin gida.

Aikin jarida da hanyoyin samun tallafi ma kafafen yada labarai, wanda Media Impact Funders suka rubuta a shekarar 2018 mai suna. “Abu biyar da ya kamata ku sani da hanyoyi biyar na farawa.” ‘Yar jarida Michele McLellan ce ta rubuta tare da tallafin gidauniyar Wyncote da ke Amirka.

Abubuwan biyar da suka shawarci a sani:

 • Aikin da gidauniyoyi ke so yana fuskantar hadari
 • Wajibi ne aikin jarida ya nemi sabbin hanyoyin kulla dangantaka da al’umma
 • Salon kasuwanci mai dorewa na da mahimmanci sosai
 • Aminci a aikin jarida na fuskantar barazana
 • ‘Yancin kai da gaskiya suna da mahimmanci a aikin jarida

Hanyoyi biyar na faraway:

 • Gano dabarun samun tallafi da zuba jari
 • Tallafawa sabbin dabarun kawo rahotanni, salon kasuwanci da hulda
 • Karfafa kawance da fadada iyaka da yawan wadanda su ke samun labaran
 • Mayar da hankali wajen samun bayanan al’umma
 • Koyon karin abubuwa dangane da samun tallafi

Tasirin bincike mai zurfi: Rahoto dangane da abubuwan koyi wajen auna tasirin bincike mai zurfi a aikin jarida, wanda GIJN ta fitar a shekarar 2017

Domin taimaka ma ma’aikata da masu goyon bayan aikin jaridar da ya tanadi gudanar da bincike mai zurfi, mawallafan sun yi nazarin ra’ayoyi da dama kan yadda ya kamata a auna tasirin bincike mai zurfi a aikin jarida dan ganin yawan shi a zahiri. Sun rawaito cewa “salon da ake amfani da shi wajen tantance yawan ba kai tsaye ya ke kamar yadda ake iya duba yawan mutanen da suka yi amfani da wani shafin yanar gizo ba” sa’annan kuma “tsarin binciken da zai duba ainihin yadda za’a iya auna tasirin bincike mai zurfi bai riga ya nuna ba.”

Ya ce:

Binciken da muka yi ya nuna mana cewa tabbas ana iya auna tasirin bincike mai zurfi kuma albarkacin ya wuce farashin da za’a kashe. Hakika, sau da yawa tasirin shi na da ban mamaki: Falasa masu cin zarafi, shawo kan cin hanci da rashawa, tabbatar da gaskiya, inganta mahimmacin alhakin da ya rataya a kan jama’a da shugabanni da karfafa dimokoradiyya, a ambaci kadan daga cikin gudunmawa masu mahimmancin da ya ke bayarwa – musamman a dimokiradiyya mai tasowa da kasashe masu tattalin arzikin da yanzu su ke bunkasa.

Gabatarwa ga shirin tallafawa aikin jarida da kafofin yada labaraiA shekarar 2018 aka wallafa. Kungiyar Ariadne tare da hadin gwiwar shirin gaskiya da rikon amana suka wallafa a yayin da Sameer Padania ya rubuta. “burin shirin shi ne taimakawa masu zuba jari wajen fadada fahimtarsu dangane da mahimman batutuwa, mahawarori da dabarun bayar da tallafi ga aikin jarida da kafafen yada labarai.

Tallafawa aikin jarida, gano sabbin dabaru: Labaran nasarori da ra’ayoyi na tabbatar da kawance mai dorewa Wannan rahoton na 2018 wanda cibiyar Shorenstein kan kafafen yada labarai, siyasa, da manufofin jama’a a Jami’ar Harvard ta wallafa ya kwatanta misalai ne na irin hadin gwiwar da ke tsakanin masu bayar da kudi da kungiyoyin kafafen yada labarai da ke Amurka.

Masu bayar da tallafin tabbatar da tasirin kafofin yada labarai hadaka ce da ke samun goyon bayan mambobi wadanda ke yunkurin inganta al’umma ta yin amfani da kafafen yada labarai da fasaha. Shafinsu na dauke da cikakken bayani dangane da tushen taswirar tallafawa kafafen yada labarai da ke nuna duk kafafen da ake tallafawa a duk fadin duniya. Akwaibidiyon da ke kwatanta yada za’a iya amfani da hanyoyin bincike masu sarkakiya. Kundin bayanan ya fara ne daga 2009 kuma a kan kara sabbin bayanai a-kai a-kai kuma ana iya samun bayanai har zuwa 2015 da farkon 2018. Masu bayar da kudi na Media Impact sun fitar da rahotanni daban-daban tare da abubuwa biyar da ya kamata a sanin da aka kwatanta daga farko. Rahotannin farko sun hada da:

Bincike mai zurfi a aikin jarida: zai ninka jarin da aka zuba: Bayanin da James Breiner wani mai bayar da shawara kan kafafen yada labarai ya rubuta a 2019

Bincike mai zurfi na aikin jarida a duniya baki daya: Dabarun tallafawawani rahoton da aka rubuta a 2013 ma Cibiyar Kasa da Kasa ta Taimakwa Kafafen Yada Labarai lokacin taron Asusun Kyauta na Kasa ga Dimokiradiyya, inda babban darektan GIJN David Kaplan ya duba hanyoyin da za su fi dacewa wajen tallafawa bincike mai zurfi a aikin jarida na kwararru a kasashe masu tasowa da wadanda ke fuskantar sauyi. Wannan ya kunshi tarihin yadda aka fara rahotannin batutuwan da aka yi wa bincike mai zurfi da ma yadda ya yadu a duniya baki daya tare da shawarwari ga hadakar kuniyoyin da ba ruwansu da riba, cibiyoyin rahotanni da na horo

Dabarun hulda da kafafen yada labarai na Dot Connector Studio kan taimaka wa kamfanoni da masu bayar da tallafi su tattauna su samar da dabaru sa’annan su yi nazaribn tasiri. “Zai iya taimakawa wajen nazarin bururruka domin auna alfanunsu da kuma bayyana irin dangantakar da mutun ke so ya kulla da wadanda ke amfani da kafar yada labaran,” a cewar bayanain. Dot Connector Studio kungiya ce mai taimakawa kafafen yada labarai da dabaru. ‘Yar jarida Jessica Clark ta kirkiro kamfanin a 2013. Clark tana kuma bincike a Open Doc Lab da ke cibiyar fasahar da ke jihar Massachusetts.

Gidauniyar Dimokiradiyya ya samar da wata taswirar tsare-tsare dan taimakawa masu bayar da kudi da kungiyoyi wajen fahimtar abubuwan da ke taka rawa wajen labaran cikin gida da shigan jama’a siyasa domin a dama da su, da gano wuraren da ke bukatar taimako.

Hira da Maria Teresa Ronderosdarektan shirin aikin jarida mai zaman kanshi a gidauniyar Open Soceity. A wannan hirar da aka yi a 2018 tace OSF na karkata ga amfani da “tsarun da zai tabbatar cewa kudaden tallafin da za’a bayar sun goyi bayan sabbin dabaru musamman wadanda za’a iya kwaikwaya a yi amfani da su a duk kasashen duniya.” Ta kuma kara da cewa akwai sha’awar irin wadannan tsare-tsaren wadanda “ke ganin kansu a matsayin wadanda ke jagorantar al’ummar mutanen da suke da bayanai da illimi dangane da batutuwa daban-daban.

Raba bayanai da jama’a ta halatattun hanyoyi – Shawarwari kan hanyoyin tattaunawa don masu bayar da tallafirahoto ne dangane da binciken da aka wallafa a 2018 wanda kamfanin Ariadne ya gudanar, wanda ya sami tallafin 360 tsakanin watannin Maris da Oktoba

Republish our articles for free, online or in print, under a Creative Commons license.

Republish this article


Material from GIJN’s website is generally available for republication under a Creative Commons Attribution-NonCommercial 4.0 International license. Images usually are published under a different license, so we advise you to use alternatives or contact us regarding permission. Here are our full terms for republication. You must credit the author, link to the original story, and name GIJN as the first publisher. For any queries or to send us a courtesy republication note, write to hello@gijn.org.