Accessibility Settings

color options

monochrome muted color dark

reading tools

isolation ruler

Image: Pexels

Hadin gwiwa a shirye-shiryen bincike mai zurfi na cigaba da samun karbuwa.

Aiki tare da abokan tarayya na iya habakawa da kuma kara yawan abubuwan da ake bukata wajen aiki da ma yawan wadanda za su karanta labaran da aka wallafa. Ana iya samun kwarewa na musamman, kamar yin nazarin bayanai, kirkiro zane-zanen hotuna ko kuma tsara shirin ta yin amfani da fannoni daban-daban na yada labarai.

Akwai rubuce-ribuce da dama dangane da hanyoyin yin hadin kai wajen bincike mai zurfi – Yadda za’a gina dangantaka mai aminci, a kirkiro dandalolin aiki, a yi musayar bayanai, a wallafa rahoton, a kula da abubuwan da suka shafi da’a da sauransu. Sai dai ba a yi rubuta da yaw aba kan yadda za’a yi “zawarcin” da ma yadda za’a tsara “zaman auren.”

A cikin wannan jagoran GIJN ta mayar da hankali kan batutuwan da suka hada da:

  • Yaushe ne hadin gwiwa ke da alfanu
  • Yadda ake samun abokan tarayya
  • Yadda ake “zawarcin” abokai
  • Abun da ya kamata a sanya a yarjejeniya
  • Ramuka ko tarkon da ya kamata a kula

Tare da takaita darussan da aka dauka, wannan jagora za ta bayyana mu ku rubuce-rubucen da ke da mahimmanci. Yawancinsu sun yi bayani sosai, amma ba’a kan matsalolin da a kan samu da farko kadai ba, har da abubuwan da kan faru a kowani mataki na hadin gwiwar.

Yayin da burinmu na farko shi ne hadaka tsakanin kafofin yada labarai biyu, mun kuma tabo batin hadin gwiwa tsakanin kafar yada labarai da kungiyoyi masu zaman kan su wato NGOs.

Ko da shi ke shawarwari mafi bayanai da inganci dangane da hadaka shi ne wanda Rachel Glickhouse ta rubuta wa ProPublica, kafar yada labaran Amurkan da ta yi suna wajen bincike mai zurfi: Collaborative Data Journalism Guide.

Yaushe ne ya kamata a hada gwiwa?

Wasu labarin kawai sun yi girma da yawa ta yadda kafar yada labarai daya ba za ta iya yin labarin yadda ya kamata ba a cewar Bastian Obermayer, wanda shi da Frederik Obermaier suka taka rawar gani wajen fallasa labaran Panama Papers da Paradise Papers. ‘Yan jaridan na Jamus ne suka raba bayanan da su ke da shi da Hadakar kasa da kasa ta ‘Yan Jaridan da ke bincike mai zurfi wadda ke da hedikwatarta a Washington DC, wadda kuma a yanzu haka sun zama masu ruwa da tsaki a irin aikin jaridan da ke bukatar hadaka irin wadda su ka yi.

Babban abin da ke taimakawa hadaka shi ne damar da yak e bayarwa a iya gudanar da binciken da ke ketara iyakokin kasashe.

Stefanie Murray, babban darektar Cibiyar Hadin-Kan Kafefen Yada Labarai da ke jami’ar jiha ta Montclair a birnin New Jersey ta ce kwararan dalilai guda biyar ne na fara hadaka.

  • Babban taro kamar zabe na karatowa kuma yana tattare da sarkakiya dakin labarai guda ba zai iya kula da shi yadda ya kamata ba
  • Akwai rikicin da ke tasowa ko kuma ma ya faru musamman kamar labari da dumi-dumi
  • Dakin labaran ba shi da masaniyar wani bati wanda ake dauka a kusan kowani dakin labari da masu sauraro daban-daban wadanda kuma suke da banbance-banbance iri-iri.
  • Wani dakin labari na samun matsala wajen yin labari da kan shi yana ganin kamar yana bukatar taimakon wasu ‘yan jaridan.
  • Dakin labarin ya sami wasu kudaden da za su tallafa mi shi wajen aiwatar da wani shirin hadin gwiwa.

An kuma dauko wani bangaren da ta yi tsokaci a littafin jagorar ProPublica mai suna Wato shin wannan shirin ya cancanci a mi shi hadaka?

Murray ta bayar da shawara cewa idan ana tunanin abokan tarayya, a fara da nazarin irin taimakon da dakin labaran ke bukata daga wadanda ake sa ran tarayyar da su. Wata kila za ku so ku nemi irin abokan da za su tallafa mu ku da abin da baku da kwarewa. Ku na bukatar karin masu dauko rahotanni ne? taimako wajen tura korafin neman bayanan da aka ajiye? Ku na bukatar kwararrun masu nazari? Harsunan da ba ku iya ba ko kuma samun dama shiga wasu al’ummomin da dama shiga wuraren ya kasance mu ku kalubale? Ko kuma dai kuna ganin tarayyar a matsayin dabara ce ta samun masu sauraro kuma kuna neman abokan da ke da yawan masu sauraro?

Cibiyar Hadin-Kan Kafofin Yada Labarai ta kuma wallafa jagorori kan batutuwa guda uku da suka shafi hadin-kai:

Yadda ya dace a nemi abokan tarayya

A cewar Glickhouse “shawarar farko dangane da hadaka ga wadanda ba su taba yi ba, daga kwararru a wannan fannin shi ne za’a fi jin dadin aikin idan aka yi hadakar da wadanda aka riga aka sani.” A jagorrar ProPublica, inda aka yi magana kan yadda ake nemowa a kuma tuntubi wadanda ake neman a yi tarayyar da su, ta kara da cewa, “Kun riga kun yadda da juna kuma kuna sadawa, wadanda su ne mafi mahimmanci wajen tabbatar da hadaka mai aminci.”

“Ka da ku sa ran cewa abokan hadakar za su zo wurin ku,” bisa la’akari da shawarar farko cikin shawarwari 10 na gudanar da hadaka mai nasara tsakanin ‘yan jarida, wani labarin da abokan GIJN Guilherme Amadoo, Xing Feng, Titus Plattner da Mago Torres suka rubuta a 2018. Sun fadada batun kamar haka:

“Kada ku bar labari mai kyau ya rube. Idan kuna da bayani mai mahimmanci kuma kuna iya hada kai da wani, ku nemi abokan tarayya ku nuna musu abin da ku ke da shi. A yi wannan wuri a yanayi nay au da kullum, wato ba a hukumance ba. Wata kila wannan ba sabon abu ba ne amma mun kula cewa tuntubar mutane shi ne mafi wahala a wajen irin mu masu daukar rahotanni, wadanda muka saba aiki mu kadai.”

Shawara na 2 ita ce “Ku nemi abokan tarayyar da suka fi dacewa da ku”

Wanda ya fi dacewa da ku ba lallai ne ya kasance wani fitaccen dan jarida daga wata kasaitacciyar kafar watsa labarai ba. Zai iya kasancewa dan jarida mai kuruciya daga wani dan karamin dakin labarai ko kuma wanda ke aikin jarida na sa kai wanda ke da hazaka sosai. Yawancin lokuta ‘yan jarida masu kuruciya sun fi kasancewa masu dadin sha’ani saboda suna da sha’awan yin nasara, sauraon jama’a dan su fahimci ra’ayoyinsu, suna kuma da zurfin tunani. Kamar yadda ku ke yi da majiyoyi ku duba ku ga inda manufofinku su ka zo daya. Ku yi binciken mafarinsu da irin karatun da suka yi. Ku nemi wani wanda ba lallai ku na da kwarewa iri daya amma dai kuna iya tallafawa juna.

Dan haka Glickhouse na bas a shawarar gudanar da bincike kan masu dauko rahotanni da kafofin yada labaran da ke ai ki kan batun. A ganinta yana da mahmmanci a kulla kawance wajen manyan tarukan masana’antar.

Ta kuma shawarci tuntubar wadanda ke Cibiyar Hadin-Kan Kafofin Yada Labarai dan samun shawara ko kuma duba cikin jadawalin ayyukan da suka yin a hadin-kai tsakanin ‘an jarida dan samun ra’ayoyi. Haka nan kuma ta ce ana iya yin amfani da abokai, wato ko wani ya san wani, ana iya tura sakon email ga wadanda ake sha’awar aiki da su ko da kuwa ba’a san su kai tsaye ba, da kuma tallatawa dan mutane su gani su neme ku su nuna sha’awa.

Baya ga kwarewa a fannin da ake mayar da hankali, akwai wasu bangarorin da su ma suke da mahimmanci. Wadannan sun hada da kwarewa wajen tafiyar da kungiyoyin ‘yan jarida, gudanar da shiri da kuma iya aiki da jama’a.

“Dangantaka na da mahimmanci,” a cewar Stefanie Murray a kasidar da ta rubuta wa Cibiyar Hadin-Kan Kafofin Yada Labarai a 2018 mai suna Kuna tunanin shiga hadaka a shirin dauko rahotanni? Ga darussa 8 daga shirye-shirye 6. Ta kuma yi karin bayani kamar haka:

“Zabi abokan hadakar kamar yadda za ku zabi abokanku idan har kuna da damar yin hakan – aminci tsakanin juna yana da mahimmancin gaske. Kuma iya yin magana bayyane, dariya wasu lokuta da jin dadin aikin da kuke yi zai inganta shirin a karshe. A tunani na daya daga cikin mahimman darussan da na dauka shi ne dangantaka mai karfi tsakanin bangarorin da ke hadakar,” Laura Lee, Editar Education NC, ta fada mana.”

Shugabanin hadin gwiwa “sun yi amfani da matakai daban-daban wajen daukar ma’aikata, tattaunawa da su, kula da su da duk sauran mutanen da ke aiki da su,” a cewar wata kasidar da Joy Jenkins da Lucas Graves daga Cibiyar Nazarin Aikin Jarida na Reuters da ke Oxford (2019) su ka rubuta.

Wani abin da ya kamata a mayar da hankali a kai wajen zaben abokan tarayya ya taso a babban taron GIJN da aka yi a birnin Hamburg a 2019. Wata sa’a a kan zabi abokan aikin “tun kafin a kammala bincike yayin da aka sami bukatar fara wasu rahotanni.” Wannan sakon ya zi daga wurin Axel Gordh Humlesjö, wani mai daukan rahotanni da ke aiki da gidan talbijin na Sweden wato SVT kamar yadda aka kwatanta a cikin kasidar da Rowan Philip ya rubutawa GIJN. Humlesjö ya kara da cewa:

“Babban abin da na kowa a kan hadaka shi ne: Wa ku ke bukata ku yi nasara; wa ye ba ku bukata? Idan kuna aiki da wani batun sirri daga Majalisar Dinkin Duniya misali kuma za’a iya kashe wasu majiyoyi a kasar Kwango, sai ya zama mana da mahimmanci a ce muna da irin abokan da za mu iya kallo a tsaban idanunsu mu yarda da su. Mun gayyaci mujallar manufofin ketare a tsakiyar shirin domin mun gano cewa muna bukatar wani wanda ke birnin New York wanda kuma ya ke da abokan hulda na kut da kut a cikin Majalisar Dinkin Duniya wanda kuma zai iya aiki da wannan batun a nan a kasa.”

Wani jagoran daga Ofishin kula da Bincike Mai Zurfi a Aikin Jarida a Burtaniya wato Bureau of Investigative Journalism wanda ya fara baiwa al’umma karfin gwiwar shiga a dama da su, na tuna mana cewa ana iya yin kawance da wadanda ba ‘yan jarida ba:

“Yadda mu ke gani, kawance shi ne sabon takara. A dandalinmu da ke intanet, kwararru a fanin fasaha na taimakwa ‘yan jarida da ayyukansu. Kwararru a fanin zane-zane na taimakawa dakunan labarai; al’umma tana taimakawa da bayanai; kwararru na kawo lambobin jama’a da wadanda ke da masaniyar abubuwan da sukan faru a bayan fage; ‘yan jarida kuma sun araba bayanai da hirarraki da sakamakon bincike.”

Nan gaba

Zaben abokan tarayya shi ne matakin farko.

Shawarwari kan matakan farko da ya kamata a dauka yayin da ake kokarin fara hadakar na da mahimmanci ga yanayin zaben. Abun da ake ta maimaitawa shi ne ku tabbatar akwai yarda a tsakaninku. Ga wasu rubuce-rubuce da za su iya taimakawa:

Wasu rubuce-rubucen da za’a iya dubawa kuma wadanda ke dauke da darussa daga ayyukan da aka yi a baya da misalai da hadin gwiwa da sauransu:

Republish our articles for free, online or in print, under a Creative Commons license.

Republish this article


Material from GIJN’s website is generally available for republication under a Creative Commons Attribution-NonCommercial 4.0 International license. Images usually are published under a different license, so we advise you to use alternatives or contact us regarding permission. Here are our full terms for republication. You must credit the author, link to the original story, and name GIJN as the first publisher. For any queries or to send us a courtesy republication note, write to hello@gijn.org.