Bayanai a aikin Jarida: Kayayyakin aiki wajen kirkiro hotuna da jadawali na bayanan da aka samu
Akwai manhajoji da yawa wadanda ake amfani da su wajen ganin bayanai. Wadansu ba su da wahala wajen amfani kuma ba sai an sarrafa su ba, a yayin da wasu kuma su ke da wahalan koyo amma kuma sun fi bayar da irin dabarun da ake bukata. Ga wasu daga cikin wadanda ‘yan jarida su ka fi amfani da su:
ArcGIS wannan daga Esri ne kuma ana amfani da shi wajen raba taswirori a intanet. Yana kuma da ajiya da yawa na taswirorin da ake amfani da su a intanet amma ku tabbata kun yi amfani da wadanda ku ka yarda da sahihancin tushen su. Esri yana da abin da ake kira Storymaps wanda ke taimakawa wajen daidaita labarai da taswirori
CartoDB ana amfani da shi wajen kirkiro taswira. Akwai na kyauta wa dalibai. ‘Yan jarida kuma na iya biyan $199 kowace shekara dan samun damar amfani da shi a yayin da kungiyoyi kuma za su iya biyan na daidai abin da suke so.
Chartbuilder – Wannan manhajan na kyauta ne. Ba shi da abubuwa da yawa amma dai zai taimaka da tura hotuna zuwa manhajoji irin su SVG ko JSON
D3 kamar dakin ajiya da kirkiro bayanai ne na Javascript. Ana iya yin zane da shi. Akwai misalan ire-iren abubuwan da ake iya zanawa a nan/here. Akwai kuma darasi na bidiyo da za’a iya gani a nan/here. Duk abubuwan da ya kamata a karanta an fassara su zuwa harsuna daban-daban wadanda suka hada da Chinese, Spanianci, Rashanci, Harshen Turkiyya da Portuganci.
Datawrapper wannan a Jamus aka krikiro kuma bay a bukatar wani kwarewa na musamman. Ana iya zane iri-iri har ma da taswira. Akwai na kyauta amma ba zai bayar da abubuwa masu amfani da yaw aba. Na kudin kuma akwai farashi daban-daban. Akwai na dalibai, na mutun daya ko kuma kungiya sa’annan da dakunan labarai. Farashin ya kama daga $33 a wata zuwa $564 a wata. Ana iya samun bayanai a shafin kyauta kuma akwai darussa a rubuce a shafin Academy
Plotly Chart Studio shafi ne da ke taimakwa wajen zane da taswira da jadawali cikin sauki. Shi ma ana biya daga $99 a shekara wa dalibai zuwa $840 a shekara wa ma’aikata
Plotly.js na kyauta ne kuma ana iya amfani da shi wajen yin JavaScript. Yana bukatar ilimin programming. Akwai sigogi daban-daban a R, Python da sauran harsunan fasahar. Akwai rubuce-rubuce a kan shi a GitHub
StoryMapJS manhaja na kyauta ne wanda ke taimakawa wajen rubuta labarai a intanet da ke bayyana wuraren da abubuwa suka faru. Sabon manhaja ne amma kuma bas hi da matsala kuma kusan kowa na iya amfani da shi
Tableau shi ma yana yin duk hotuna da zane-zanen. Ana iya duba shafin domin ganin farashi. Kyauta ne ga mambobin Investigative Reporters and Editors. Tableau Public kyauta ne sai dai shi kuma ba shi da armashin da sauran ke da shi.
Timeline JS shi ma kyauta ne kuma yana taimakawa wajen yin duk zanen da ake bukata musamman irin wanda za’a iya latsawa a ga abin da ake so a gani. Akwai shi a harsuna 40. Bayanan na kan manhajan lissafin google ko kuma google spreadsheet dan haka babu wahalan kara bayanai ko sabunta shafin.