Accessibility Settings

color options

monochrome muted color dark

reading tools

isolation ruler

Bayanai a aikin Jarida: Ganin Bayanai

Da zarar kun yi nazarin ku wata kila za ku so yin hotuna da taswirorin da za su nuna sakamakon da aka samu, Ga wasu daga cikin wuraren da za’a iya samun hanyoyin inganta labarai.

Chartable – taskar blog ce da aka fara a Jamus a karkashin jagorancin wadanda suka kirkiro manhajan da ke yin hotuna mai suna Datawrapper. Ya na dauke da misalai daga labaran da aka wallafa a kasashen duniya da ma yadda ake abubuwa kamar wannan littafin da Charlotte Rost ta rubuta kan hanyoyin amfani da launi a hotunan bayanai

The Chartmaker Directory wannan jaddawali ne da ke lisafta ire-iren bayanan da ake gani da misalai da kuma irin makaman aikin da ake amfani da su da yadda ake amfani da su.

Data Viz Done Right wannan taskar blog ne da ke nuna misalan yadda hotuna masu inganci kan gyara rahotannin da akan wallafa a duniya baki daya.

The Data Visualisation Catalogue wannan na dauke da ire-iren hanyoyin da za’a iya yin zanen inganta rubutu. Sai dai bayanin shi bai kai na Chartmaker Directory ba

Data Visualization: A Practical Introduction (2018) Wanda Kieran Heady ya rubuta. Wannan littafin na duba shika-shikan samar da bayanai maus inganci da kuma yadda ake amfani da bayanai a R. Healy dan asalin Ireland wanda ke nazarin al’umma da yanayin zamantakewa wanda ke koyarwa a jami’ar Duke. Ana iya sayen littafin a Amazon ko kuma a nan/here

Fundamentaks of Data Visualization (2019) wanda Claus O. Wilke ya rubuta ya yi bayani kan ginshikin data visualization a R kuma ya bayar da fifiko kan irin matsalolin da aka fi fuskanta wadanda yawancinsu kan kai ga bayanan da ke yaudarar jama’a. Wilke jagora ne a sashen nazarin muhallin dana dam da ke jami’ar Texas a Austin. Ana iya sayen littafin a intanet.

Interactive Data Visualization for the Web, 2nd Edition (2017) wanda Scott Murray ya rubuta ya yi bayani dalla-dalla kan amfani da jadawalli ga taswira ta yin amfani da fasahar da ake kira D3 visualization Library. Murray shi ne tsohon mataimakin farfesa a jami’ar San Francisco wanda yanzu yak e aiki da wata kafar yada labarai mai suna O’Reilly Media. (ana iya saye a nan)

Peter Aldhous mazaunin Amurka mai labarai kan kimiyya da kafar yada labaran Buzzfeed yana da shafi da kuma shawarwari da ke taimakawa wajen duba abubuwan da suka shafi R da taswira da nazarin layuka.

PolicyViz taskar blog ce da masanin tattalin arzikin nan dan Amurka Jonathan Schwabish ke kula da shi. Shafin na dauke da misalan irin yadda ya kamata hotunan su kasasnce kuma yana koyarwa a birane daban-daban a Burtaniya da Amurka. (Yana karbar $500 zuwa $800 ko wani zama)

The Truthful Art (2019) wanda Alberto Cairo ya rubuta na bayar da misalai a rubuce da kuma umurnin abubuwan da ‘yan jarida za su iya yi a zahiri. Akwai bayanai kan yadda za’a iya tantance bayanai. Cairo na da babban mukami a irin aikin jaridan da ke amfani da hotuna a jami’ar Miami kuma ya rubuta litattafai da yawa da kuma bidiyoyi da darussa. Ana iya sayen littafin amma kuma akwai shafuka 40 da za’a iya karantawa kyauta. Cairo yana kuma koyarwa a shafin makaranta na Cousera.

VisualizingData.com shafi ne da ke hedikwata a Burtaniya wanda ke da taskokin blog din da be bayar da shawarwari, horaswa a intanet da kuma ido da ido a biranen Manchester da Landan. Yawancin litattafan da rubuce-rubucensa kyauta ne, amma koyarwar kan kai tsakanin $400 zuwa $1,300 kowani zama.

The Visual Display of Quantitative Information (2001) wanda kwararre a illimin statistics ko kuma alkaluma Edward Tufte ya rubuta yana bayar da bayani ne kan yadda za’a iya sanya bayanai a hotuna tare da misalen irin zanen da za’a iya amfani da shi da taswira da kuma hanyoyin kaucewa alkaluman da za su yaudari jama’a. Tufte wanda jaridar New YorK Times ta taba kwatanta shi a matsayin “Da Vinci of Data” wato dai gwarzo a fanin na say a kan bayar da darussa a biranen Amurka da dama inda yak e karbar $380 kowani zama.

Which Chart Could I Use and Why? (2016) Wannan takaitacciyar jagora ce da Peter Aldhous ya rubuta dan bayar da shawara kan jadawali, da launin da suka fi dace wa da ire-iren bayanai.

Visualize This: The Flowing Data Guide to Design, Visualization and Statistics (2011) wanda Nathan Yau ya rubuta na bayar da jagora daki-daki na yadda za’a iya kirkiro hotuna daban-daban idan ana amfani da manhajoji irin su R, Javascript, da PHP. Yau wanda ya yi digirin digirgir a jami’ar UCLA ne ya samar da shafin FlowingData(shafin da ake biya dan samun darussa) sa’annan shi ya rubuta Data Points: Visualization that means something (2013)