Commercial Revenue: Essential Reading/Kudaden shiga daga hada-hadar kasuwanni: mahimman batutuwan karantawa
Kudaden shiga na kasuwanci na daukar suffofi daban-daban kuma zai iya bayar da karin kudin da ake bukata a kungiyoyin yada labaran da ba ruwansu da riba ko kuma ma cikakken tallafin da su ke bukata. Wannan ya hada da talla, da kudaden da masu sayen labarai ke biya wata-wata da sauransu:
Labaran Google da INN sun wallafa littafi mai tsokaci kan yadda kafofin labaran da ba ruwansu da riba za su iya samun kudaden shiga– Littafi ne da ke nuna wa dakunan labarai yadda za su bunkasa kudaden shiga daga talla, masu daukan nauyin taro, karban kudi dan wallafa wadansu batutuwa da ma sauran hanyoyin samun kudi.
Yadda ya kamata a auna kudaden shiga na kasuwanci a matsayin dabara ta tabbatar da dorewar kafafen yada labaran da ke bincike mai zurfi. A wannan kasidar, mawallafi Ross Settles ya mayar da hankalu ne kan kafofin yada labarai na dijital da kasuwanci a cibiyar aikin jarida da nazarin kafofin yada labarai da ke jami’ar Hong Kong
Darussa na koyarwa da koyon aikin jarida na kasuwanci da (Duba kwatancen da Jeremy Kaplan, darectan illimi a cibiyar Tow-Knight na aikin jarida na kasuwanci a jami’ar birnin New York)
Sabbin hanyoyin da mawallafa za su iya samun kudaden shiga daga yanar gizo
Reader Revenue Kit – Taska mai kunshe da labarai kan batutuwa daban-daban wadanda ke hannun American Press Institute