{"id":501192,"date":"2022-07-25T02:28:28","date_gmt":"2022-07-25T06:28:28","guid":{"rendered":"https:\/\/gijn.org\/?page_id=501192"},"modified":"2024-05-23T16:05:10","modified_gmt":"2024-05-23T20:05:10","slug":"freelancing-dandalolin-da-ke-samarwa-marubuta-da-kudi-2","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/gijn.org\/ha\/riyoyin\/freelancing-dandalolin-da-ke-samarwa-marubuta-da-kudi-2\/","title":{"rendered":"Freelancing: Dandalolin da ke samarwa marubuta da kudi"},"content":{"rendered":"<div class=\"elementor-element elementor-element-5a61abf2 elementor-widget elementor-widget-text-editor\" data-id=\"5a61abf2\" data-element_type=\"widget\" data-widget_type=\"text-editor.default\">\n<div class=\"elementor-widget-container\">\n<p>Ana ganin karuwa a yawan shafukan da ke taimakon marubuta suna samun kudi a yayin da suka wallafa labaransu da kan su. Wajibi ne ku yi bincike dan tantance ko wannan abu ne da ya dace da ku.<\/p>\n<p>A wannan sashen, ba za mu duba wuraren da ke taimakawa wajen kirkiro da shafi, ki wasiku ko taskokin blog ko kuma ma duba batun Plug-ins wato fasahohin da ke taimakwa wajen saye da sayarwa ko biyan kudi ba. Ba kuma zamu mu shiga batun shafukan sochiyal mediya irin su Telegram, facebook, Reddit da WhatsApp ba.<\/p>\n<p>An kwatanta irin karuwan da ake samu wajen kirkiro wasikun email masu zaman kansu a cikin wani <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.nytimes.com\/2020\/09\/23\/business\/media\/substack-newsletters-journalists.html\">labarin da aka wallafa a jaridar New York Times<\/a> a watan Satumban 2020, wani a <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.axios.com\/pandemic-spurs-journalists-to-go-it-alone-via-email-613ca2d5-e8d5-4235-9582-48cc028e9d8b.html\">Axios<\/a> da <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/medium.com\/trust-media-and-democracy\/journalists-getting-paid-how-online-platforms-are-boosting-income-for-writers-3035409666bb\">wani na uku kuma a Medium<\/a> wanda mai bayar da shawara kan kafofin yada labarai Mark Glaser ya rubuta.<\/p>\n<p>A wani sashen mun tattauna hadin gwiwa ta hanyar manyan kamfanoni a intanet irin su Labaran Apple da SmartNews wadanda \u2018yan jarida masu zaman kansu ba suwa samu.<\/p>\n<p>Rarraba shirye-shiryen sauraro na podcast shi ma wani batun ne. Akwai shawarwari a wannan labarin,\u00a0<a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/robertkatai.com\/submit-podcast-network\/\">22 Top Networks to Submit Your Podcast in 2020\/ Kafofin yada labarai 22 da ya kamata ku baiwa shirin podcast din ku a 2022<\/a>\u00a0wanda kwararre kan talla a Amurka Robert Katai ya rubuta.<\/p>\n<p>Adadin sabbin wuraren wallafa labarai na ninka kanshi. Wannan fanni ne da ke sauyawa kullun dan haka yana da mahimmanci a yi bincike sosai kafin a yanke shawara. Wani wajen da zai taimaka shi ne\u00a0<a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/bloggingguide.substack.com\/p\/new-to-blogging-guide-start-here\">Blogging Guide\/Jagorar Rubutu<\/a> a Blog na Casey Botticello.<\/p>\n<h4><b>Wuraren Sayar da Labarai<\/b><\/h4>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/medium.com\/\"><b>Medium<\/b><\/a><\/p>\n<p>Wannan dandalin da aka kaddamar a shekarar 2012 ya ce yanzu mutane akalla milliyan 120 na ziyartar shafin kowani wata kuma shi ne waurin da \u201ckowa yana da labarin da zai raba sa\u2019anan za\u2019a turo muku wadanda suka yi fice.\u201d<\/p>\n<p>\u201cIdan mutun ya yi rajista zai iya bin mawallafan da ya fi so da rubuce-rubucensu. Zai iya ajiye labaransu domin ya dawo ya karanta daga baya, ya wallafa na shi tsokacin da sauransu. <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/help.medium.com\/hc\/en-us\/articles\/225168028\">A cewar shafin<\/a> \u201cwallafa labarai a nan kyauta ne kuma za\u2019a raba labarinka ga wadanda ke bin ka tare da milliyoyin masu karatu da ke sha\u2019awan irin batun da ka yi tsokaci a kai.\u201d<\/p>\n<p>Medium na samun kudaden shiga daga kudin da ake biya. Ana biyan $5 wata-wata ko kuma $50 kowace shekara, <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/medium.com\/membership\">mutun na iya zama mamba dan samunduk labaran da ke kan Medium<\/a> da wasu karin abubuwa.<\/p>\n<p>Masu kirkiro shirye-shirye ko kuma content creators na iya samun kudi saboda aikinsu. Domin samun karin bayani kan medium fara daga\u00a0<a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/medium.com\/creators\">nan\/here<\/a>. Ana iya samun kudi daga <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/help.medium.com\/hc\/en-us\/articles\/115011928308-Write-for-members\">Medium Partner Program<\/a>.<\/p>\n<p>\u201cYayin da partner program kyakyawar hanya ce ta wallafa labarai a Medium kada \u2018yan jarida masu zaman kansu su za ci za su kudance kamar&#8221; <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/contently.net\/2018\/02\/01\/resources\/tools\/social-media\/medium-pros-cons\/\">yadda Tallie Gabriel<\/a> \u2018yar jarida mai zaman kanta ta bayyana daga farkon shekarar 2018:<\/p>\n<\/div>\n<\/div>\n<div class=\"elementor-element elementor-element-0b0af3a elementor-blockquote--skin-border elementor-blockquote--button-color-official elementor-widget elementor-widget-blockquote\" data-id=\"0b0af3a\" data-element_type=\"widget\" data-widget_type=\"blockquote.default\">\n<div class=\"elementor-widget-container\">\n<blockquote class=\"elementor-blockquote\">\n<p class=\"elementor-blockquote__content\">\u201cDomin daukan nauyin aikinsu, \u2018yan jarida masu zaman kansu su yi amfani da Medium a matsayin kafa na biyu da ke tura masu sha\u2019awan labaransu zuwa shafin sun a kansu. Ku wallafa labarai a shafinku sa\u2019annan ku sa Medium dan ku sami karin mutanen da za su karanta a kan adireshinku tare da \u2018yar wasika daga karshe.\u201d<\/p>\n<\/blockquote>\n<\/div>\n<\/div>\n<div class=\"elementor-element elementor-element-d7b4cbc elementor-widget elementor-widget-text-editor\" data-id=\"d7b4cbc\" data-element_type=\"widget\" data-widget_type=\"text-editor.default\">\n<div class=\"elementor-widget-container\">\n<p>A watan Janairun 2020 Medium ya rawaito cewa kashi <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/blog.medium.com\/2020-writing-goals-intentions-and-motivation-81bfe7f65929\">68 cikin 100<\/a> na marubutan da suka rubuata akalla labari daya wa mambobi sun sami kudi. Y ace kashi 8 cikin 100 na wadanda suke rubutu a kai- a kai sun sami fiye da $100 kuma $21,650.88 ne kudi mafi yawan da wani marubuci a taba samu a dandalin, sa\u2019annan $8,855.73 ne kudi mafi yawa da labari daya ya taba masu.<\/p>\n<p>Domin shawara kan wallafa labarai a Medium ku duba wadannan shafukan:<\/p>\n<ul>\n<li><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/winningwp.com\/medium-vs-wordpress\/\">Medium ko WordPress<\/a> \u2013 Yadda ya kamata a zabi dandalin da ya fi daidai.<\/li>\n<li><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/findingtom.com\/best-medium-publications-write-for\/\">Fitattun jaridun Medium guda 10 da ya kamata ku turawa labarai a 2020<\/a><\/li>\n<li><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/medium.com\/feedium\/can-i-make-money-on-medium-1c7a9fcf72e9\">Zan iya yin kudi a Medium<\/a>? Labarin JJ Pryor (2019) wanda ke tabbatar da cewa zai yiwu.<\/li>\n<li><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/thisonlineworld.com\/medium-writing\/\">Yadda ake samun kudi a Medium<\/a> \u2013 Yadda na sami sama da $1000 wajen rubutu a Medium<\/li>\n<li><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.nichepursuits.com\/how-to-make-money-on-medium\/\">Yadda ake samun kudi a Medium<\/a>: Cikakken jagora ga wanda bai taba aiki da Medium ba, wanda Shane Dayton ya rubuta<\/li>\n<li><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.wordstream.com\/blog\/ws\/2016\/07\/19\/medium-optimization-tips\">Shawarwari na kara yawan mutanen da za su karanta labarin ku a Medium<\/a><\/li>\n<li><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/medium.com\/@the_manifest\/the-dos-and-don-ts-of-publishing-on-medium-com-8fbde6667932\">Abubuwan da ya kamata a yi da wadanda ya kamata a kaucewa a Medium.com wanda Manifest.com<\/a> suka rubuta a 2018<\/li>\n<li><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/medium.com\/@richtucker\/test-results-publishing-on-medium-vs-linkedin-vs-personal-blog-739433486f80\">Sakamako: Wallafa labari a Medium ko LinkedIn ko Personal Bloh<\/a>. Kasidar Rich Tucker a 2018<\/li>\n<\/ul>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/substack.com\/\"><b>Substack<\/b><\/a><\/p>\n<p>Substack na jaddada saukin fara wasikar labarai kyauta amma kuma a sami kudi. \u201cBabu wata kwarewar fasahar da ake bukata: A hada lambar asusun banki kawai a sanya farashi,\u201d a cewar shafin.<\/p>\n<p>Substack na daukan kashi 10 cikin 100 na kudin da ake biya shekara-shekara da kuma kudin ruwan da ake cirewa a kati da senti 30 na aikin da banki ya yi. Marubutan da suka zabi su wallafa labaransu kyauta na iya amfani da substack kyauta su ma.<\/p>\n<p>Shafin na zargin wai akwai milliyoyin mutanen da ke karanta labaransu kuma mutane fiye da 250,000 na biya.<\/p>\n<p>Tun watan Yulin 2020, substack ke bayar da tallafin lauyoyi tana amfani da lauyoyin kafafen yada labarai su bayar da shawarwari ga marubuta kamar yadda suka bayyana a wannan labarin ko kuma\u00a0<a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/on.substack.com\/p\/legal-support-for-substack-writers\">blog post<\/a>. Ya kuma fara wani shirin koyarwa wato <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/library.substack.com\/p\/announcing-the-next-substack-fellowship\">fellowship program<\/a>. Substack na kuma tallafawa masu shirye-shiryen saurare na podcast.<\/p>\n<p>A watan Mayun 2020 a kasidar da ya rubuta\u00a0<a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/on.substack.com\/p\/whats-next-for-journalists\">What\u2019s Next for Journalists<\/a>? Wanda ya kirkiro substack <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/on.substack.com\/people\/1\">Hamish Mckenzie<\/a> ya yi tsokaci kan yadda arziki a aikin jarida ke raguwa, yana mai cewa \u201cMuna kokarin gina wani sabon salo ne na bunkasa tattalin arzikin kafafen yada labarai wanda zai baiwa \u2018yan jarida damar cin gashin kansu.\u201d<\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/www.patreon.com\/\"><b>Patreon<\/b><\/a><\/p>\n<p>Mai mazauni a San Francisco, an kaddamar da Patreon a shekarar 2014 domin samar da dandalin da zai dace da zamanin dijital da mu ke ciki yanzu. Wadanda suka kirkiro dandalin suna amfani da subscription wato hanyar biya kafin ka samu damar shiga shafin. Suna kuma bayar da abubuwan da ke jan ra\u2019ayin mutane su yi amfani da shafin.<\/p>\n<p>A karshen 2019 mutane sama da 100,000 sun yi amfani da Patreon, kuma yana samun tallafa daga mutane fiye da milliyan 3. Ya ma sa ran biyan masu amfani da shafin su wallafa abubuwa $1 billiyan a 2019. Kuna iya samun karin bayani kan yadda wurin ke aiki a\u00a0<a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.patreon.com\/about\">nan\/here<\/a>\u00a0da\u00a0<a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/blog.patreon.com\/rewards-independent-journalists\">nan\/here<\/a><\/p>\n<p>Domin bita wadanda yawancinsu masu kyau ne, ku duba manhajoji irinsu <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/writersedit.com\/self-publishing\/what-is-patreon-and-how-can-indie-authors-use-it\/\">Writer\u2019s Edit<\/a>,\u00a0<a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.merchantmaverick.com\/reviews\/patreon-review\/\">Merchant Maverick<\/a>, da <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/venturebeat.com\/2019\/03\/19\/patreon-now-offers-creators-3-plans-with-fees-ranging-from-5-12\/\">VentureBeat<\/a>. Akwai wadansu abubuwan da ba\u2019a nuna amma ba za su iya hana bincike mai zurfi na aikin jarida ba. Kudin da akan samu ya banbanta.\u00a0<a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/graphtreon.com\/\">Grapheon<\/a>\u00a0kan duba duk kudin da aka samu daga Patreon<\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/graphtreon.com\/\"><b>TinyLetter<\/b><\/a><\/p>\n<p>Wannan wasika ce mai labarai wanda mutanen da suka kirkiro\u00a0<a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/mailchimp.com\/\">Mailchimp<\/a>\u00a0ke kawowa. Kyauta ne amma yana iya daukan mutane 5000 ne kadai.<\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/ko-fi.com\/\"><b>Ko-Fi<\/b><\/a><\/p>\n<p>Wannan kan taimaki masu rubuce-rubuce ko bidiyoyi samun tallafin kudi, sai dai sun gyara salon karbar kudin da cewa \u201cbuy me a cup of coffee\u201d ko kuma da hausa, \u201csaya mun kofin koffee.\u201d Ko-Fi bay a karbar kudi. Duk wani kudi na zuwa Paypal. Idan mutun na biyan $6 a wata zai iya samun kowani shafi.<\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/kdp.amazon.com\/en_US\/\"><b>Wallafa Litattafai kai tsaye a Kindle<\/b><\/a><\/p>\n<p>Wannan na taimakawa wajen wallafa litattafai na intanet da wadanda ma aka saba na takarda. Yana barin mawallafa su rike duk \u2018yancin da suke da shi su kuma rika karbar kudin da ke shiga. Ana iya buga shi kai tsaye kuma ana raba shi ne ta hanyar Amzon. Kuna <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/kdp.amazon.com\/en_US\/help\/topic\/G200635650\">iya duba babban shafin<\/a>. Sai dai kuma akwai wadansu matsalolin da ya kamata a duba. Wannan bitan da Doris Booth ta yi a 2019,\u00a0<a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/authorlink.com\/rants\/avoiding-the-pitfalls-of-publishing-with-amazon-kindle-self-publishing-platform\/\">2019 Review<\/a> a kasidar Writers and Readers ya nuna cewa akwai wadansu abubuwan da ke kasancewa kalubale wajen samun kudin da ma salon buga litattafan. Haka nan kuma kuna iya duba wannan labarin\u00a0<a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/justpublishingadvice.com\/the-pros-and-cons-of-amazon-kdp-select-exclusivity\/\">2020 article <\/a>a shawarwarin wallafa littafi a shirin zaben KDP inda kake baiwa Amazon duk wani \u2018yancin da kake da shi a kan littafin. Akwai tsokaci da dama dangane da abubuwan da ya kamata a yi.<\/p>\n<h4><b>Wasu abubuwan da ya kamata a duba<\/b><\/h4>\n<p>Wallafa labarin a wasu shafukan zai taimaka wajen kara yawan masu karantawa. Akwai shafukan da ke taimakawa wadanda suka hada da <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/authory.com\/?utm_source=google&amp;utm_medium=CPC&amp;utm_campaign=Keyword&amp;utm_term=authory&amp;campaignid=9918137738&amp;adgroupid=101915287673&amp;adid=433160850365&amp;gclid=Cj0KCQjw-O35BRDVARIsAJU5mQX2_xhmVb6m1MRvbvDAtiCzTIZOHjW_l909dVlWe_o8s0S_diiw6fMaAvduEALw_wcB\">Authory<\/a>,\u00a0<a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.buzzfeed.com\/community\">BuzzFeed Community<\/a>,\u00a0<a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.linkedin.com\/feed\/\">LinkedIn<\/a>, da <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/muckrack.com\/\">Muckrack<\/a>\u00a0wadanda za su iya taimakawa wajen yada labari.<\/p>\n<p>Sai dai wadannan ba su biya kuma akwai wadansu hadurra kamar raguwa a yawan mutanen da ke zuwa shafin ku. Binciken google zai iya kai mutane shafin wadanda ke taimakon a maimakon shafinku na ainihi wanda kuka saba amfani da. To amma kwararru sun ce wannan matsala ce da za\u2019a iya shawo kai.<\/p>\n<p>Domin tattaunawa dangane da irin wadannan batutuwan kuna iya karanta kasidar <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.impactbnd.com\/team\/carolyn-edgecomb\">Carolyn Edgecomb<\/a> daga Impact mai taken\u00a0<a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.impactbnd.com\/blog\/dos-donts-of-re-publishing-content-on-medium-or-linkedin\">Do\u2019s &amp; Don\u2019t\u2019s of Republishing content on Medium<\/a>.<\/p>\n<p>Edgecomb ta hada da shawarwari kamar yadda za\u2019a yi amfani da wata kalman sirri da za ta radawa google cewa duk wani \u2018yanci na ku ne, kuma ka da ta sanya labarin a wani shafi na waje da ba na ku ba.<\/p>\n<p>Kuna iya duba wadannan kasidun ma:<\/p>\n<ul>\n<li><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/medium.com\/blogging-guide\/understanding-canonical-links-and-medium-article-seo-for-your-blog-or-website-25a5afe2b71c\">Medium Article Canonical Links<\/a> \u2013 Casey Botticelo<\/li>\n<li><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.pathfinderseo.com\/what-is-content-syndication\/\">What Is Content Syndication &amp; How Does It Impact SEO<\/a>? Maddy Osman daga Pathfinder SEO<\/li>\n<\/ul>\n<h4><b>Kewaye da Duniya<\/b><\/h4>\n<p>Akwai shafuka da dama a kasashen duniya da za su iya ba ku damammaki. Ku taimaki GIJN wajen gina wannan kundin na wuraren da za ku iya wallafa abubuwa.\u00a0<a href=\"mailto:toby.mcintosh@gijn.org\">Ku aiko mana da shawarwari a nan\/here<\/a>.<\/p>\n<div class=\"oembed-container\"><iframe loading=\"lazy\" title=\"How Journalists in Asia Can Better Market Investigative Stories\" width=\"500\" height=\"281\" src=\"https:\/\/www.youtube.com\/embed\/APSeR63veXU?feature=oembed\" frameborder=\"0\" allow=\"accelerometer; autoplay; clipboard-write; encrypted-media; gyroscope; picture-in-picture; web-share\" referrerpolicy=\"strict-origin-when-cross-origin\" allowfullscreen><\/iframe><\/div>\n<\/div>\n<\/div>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Ana ganin karuwa a yawan shafukan da ke taimakon marubuta suna samun kudi a yayin da suka wallafa labaransu da kan su. Wajibi ne ku yi bincike dan tantance ko wannan abu ne da ya dace da ku. A wannan sashen, ba za mu duba wuraren da ke taimakawa wajen kirkiro da shafi, ki wasiku [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":3031153,"featured_media":1130077,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_acf_changed":false,"_price":"","_stock":"","_tribe_ticket_header":"","_tribe_default_ticket_provider":"","_tribe_ticket_capacity":"0","_ticket_start_date":"","_ticket_end_date":"","_tribe_ticket_show_description":"","_tribe_ticket_show_not_going":false,"_tribe_ticket_use_global_stock":"","_tribe_ticket_global_stock_level":"","_global_stock_mode":"","_global_stock_cap":"","_tribe_rsvp_for_event":"","_tribe_ticket_going_count":"","_tribe_ticket_not_going_count":"","_tribe_tickets_list":"[]","_tribe_ticket_has_attendee_info_fields":false,"republication-tracker-tool-hide-widget":false,"footnotes":"","_tec_slr_enabled":"","_tec_slr_layout":""},"categories":[23116],"tags":[],"gijn_topic":[],"series":[],"gijn_language":[17798],"gijn_region":[],"class_list":["post-501192","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-riyoyin","gijn_language-ha-ha"],"acf":[],"ticketed":false,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/501192","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/users\/3031153"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=501192"}],"version-history":[{"count":3,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/501192\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":1527391,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/501192\/revisions\/1527391"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/media\/1130077"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=501192"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=501192"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=501192"},{"taxonomy":"gijn_topic","embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/gijn_topic?post=501192"},{"taxonomy":"series","embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/series?post=501192"},{"taxonomy":"gijn_language","embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/gijn_language?post=501192"},{"taxonomy":"gijn_region","embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/gijn_region?post=501192"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}