{"id":501120,"date":"2022-07-19T02:08:33","date_gmt":"2022-07-19T06:08:33","guid":{"rendered":"https:\/\/gijn.org\/?page_id=501120"},"modified":"2025-03-12T05:44:43","modified_gmt":"2025-03-12T09:44:43","slug":"kulla-yarjejeniya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/gijn.org\/ha\/albari\/kulla-yarjejeniya\/","title":{"rendered":"Kulla Yarjejeniya"},"content":{"rendered":"<div class=\"elementor-element elementor-element-7e1c44a5 elementor-widget elementor-widget-text-editor\" data-id=\"7e1c44a5\" data-element_type=\"widget\" data-widget_type=\"text-editor.default\">\n<div class=\"elementor-widget-container\">\n<p>Kulla yarjejeniya ma bincike mai zurfi a aikin jarida zai yi la\u2019akari da abubuwa da dama wadanda ba su da mahimmanci a misali labarin maguna<\/p>\n<p>Akwai mahimman abubuwan da kowani irin labari ke da shi wadanda ya kamata a mayar da hankali a kai wadanda suka hada da:<\/p>\n<ul>\n<li>Bayani dangane da suffan aikin da yadda za\u2019a yi sauyi idan bukatar ta taso<\/li>\n<li>Sharuddan biya<\/li>\n<li>Wanda ke da hakkin mallakar labarin<\/li>\n<\/ul>\n<p>Bincike mai zurfi na da wasu batutuwa da ke bukatar sa ido na musamman<\/p>\n<ul>\n<li>Yadda ya kamata a biya da kyau wa babban shiri<\/li>\n<li>Kula da hakkin mallaka<\/li>\n<li>Yadda za\u2019a biya abubuwan da ba\u2019a san za\u2019a biya misali wahen samun bayanai daga FOIA<\/li>\n<li>Me zai faru idan shirin bai tafi yadda aka so ba?<\/li>\n<li>Me zai faru idan wanda ya kamata ya wallafa labarin ya ki wallafawa?<\/li>\n<li>Wadanne irin kariya na doka ne za\u2019a baiwa marubucin?<\/li>\n<li>Yaya za\u2019a yi da batun inshora na hadarin da marubucin zai fuskanta?<\/li>\n<li>Wadanne matakan kariya ne za\u2019a bayar?<\/li>\n<\/ul>\n<h4><b>Bukatar Yarjejeniya ko kwantiragi<\/b><\/h4>\n<p>Watakila ba sai an jaddada cewa kuna bukatar kwantiragi ba amma lallai kuna bukata.<\/p>\n<p>Idan babu, akwai yiwuwar \u201crashin biya, nauyin alhakin da ba naku ba, da matsaloli na shari\u2019a,\u201d Marubucin taskar blog a Amurka Ryan Robinson ya <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.ryrob.com\/freelance-contract\/\">jaddada mahimmancin<\/a> samun kwantiragi.<\/p>\n<p>\u201cKuna bukatar kwantiragi. Ga nawa.&#8221; <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/medium.com\/@jyssicaschwartz\/have-a-free-freelancer-contract-template-4a009f181830\">Dauka a cewar<\/a> Jyssica Schwartz a shafin Medium 2018<\/p>\n<p>Sai dai ba haka yake gudana ba kullun. Yarjejeniya na iya faruwa amma dole a tabbatar cewa an san duk abin da ya kamata ya kunsa.<\/p>\n<h4><b>Me Ya Kamata Ya Kasance a Cikin Kwantiragi<\/b><\/h4>\n<p>Wani wuri mai kyau da ya kamata a fara shi ne Yarjejeniyar Wallafa na Model ko kuma <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.acosalliance.org\/contracts\">Model Freelance Publishing Agreement<\/a> a turance, wanda <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.acosalliance.org\/\">ACOS Alliance<\/a>, wata kungiyar yada labarai ta kasa da kasa da ta kware a tabbatar da tsaro cikin harkokin da suka shafi kafafen yada labarai, tare da <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.vancecenter.org\/\">The Cyrus R. Vance Centre for International Justice<\/a> da ke birnin New York suka kirkiro. Haka nan kuma, <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/web.archive.org\/web\/20220420025656\/https:\/\/static.wixstatic.com\/ugd\/c1a6a6_128b76fdc82f41e79dfac6cff4a2d55b.pdf\">kuna iya duba manyan batutuwan<\/a> da aka tattauna a cikin <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/web.archive.org\/web\/20220420025711\/https:\/\/static.wixstatic.com\/ugd\/c1a6a6_a71a6ebc8aae48a3b4fd53566cdea669.pdf\">yarjejeniyar<\/a> da ma samfurin ta (Duk wadannan na rubuce a cikin harshen larabci ne)<\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/firenewsroom.org\/\">Editoci da Masu Daukan Rahotanni Masu Zaman Kansu<\/a>Sun kirkiro samfurin yarjejeniya na labarai wa \u2018yan jarida masu zaman kansu da kafofin da ke aiki tare da su. Kuna iya samun karin bayani daga\u00a0<a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.firenewsroom.org\/program\/fire-contract-template\">nan\/here<\/a><\/p>\n<p>FIRE tana kuma taimakawa da lauyoyin kwantiragi ga wadanda ke bukata a matsayin wani bangare na shirin shawarwarin da ta kaddamar a 2021 dan tabbatar da kariya a fuskan shari\u2019a. Kungiyar mai mazauninta a Amurka na bayar da lauyoyin da za su tattauna da wanda ke bukata na tsawon sa\u2019a guda kamar yadda suka rubuta a shafin su a karkashin\u00a0<a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/firenewsroom.org\/legal-assistance\">Legal Assistance<\/a>. Domin samun wannan taimakon, \u201cwanda ke bukatar wannan taimakon zai iya kasancewa a ciki ko wajen kasar \u2013 amma wajibi ne yana aikin jarida kuma ya na aiki ko shirya wani rahoton da ya kunshi <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/firenewsroom.org\/program\/guidelines-and-application\">labarai masu zurfin bincike<\/a> wdanda ke da alaka da kafofin yada labaran da ke amfani da harshen turanci a Amurka.\u201d<\/p>\n<p>FIRE ta kuma dauki nauyin wata koyarwa ta Webinar da manyan editoci, ranar 28 ga watan Satumba 2021 dangane da abubuwan da suka shafi kwantiragi. An nadi shirin kuma kuna iya sauraro a\u00a0<a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.firenewsroom.org\/request-recording-fire-panel-9-28-21\">nan\/here<\/a><\/p>\n<p>Ya kamata ku fahimci cewa dokoki da sharuddan kwantiragi za su banbanta bisa la\u2019akari inda mawallafa ko kafafen yada labarai su ke.<\/p>\n<p>Akwai kafofi da yawa a intanet da ke da kwantiragi. Mai yiwuwa akwai irin wanda zai fi dacewa da ku. Ku bincika kuna yin amfani da mahimman kalmomi irinsu \u201cModel Freelance contracts\u201d ko \u201cfreelance writer agreement\u201d ko \u201cfreelance writing contract\u201d<\/p>\n<p>Akwai batutuwan da suka zo daidai ko\u2019ina wadanda ya kamata a mayar da hankali kai. Wadannan sun hada da:<\/p>\n<ul>\n<li>\n<ul>\n<li>Kwatancen yanayin aikin da suke yi<\/li>\n<li>Yadda ya kamata a kula da sauye-sauye<\/li>\n<li>Sharuddan biya<\/li>\n<\/ul>\n<\/li>\n<\/ul>\n<ul>\n<li>Wanda ke da hakkin mallaka<b>\u00a0<\/b><\/li>\n<\/ul>\n<h4><b>Karin Karatu<\/b><\/h4>\n<ul>\n<li><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/cmgfreelance.ca\/en\/justsayno\/\">Tattaunawa kan kwantiragi<\/a> daga <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/cmg.ca\/\">Canadian Media Guild<\/a><\/li>\n<\/ul>\n<ul>\n<li><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.freelancersunion.org\/about\/\">The Freelance Union<\/a><b>,\u00a0<\/b>kungiyar da ke wakiltan dubban ma\u2019aikata masu zaman kansu a Amurka, tana bayar da <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.freelancersunion.org\/contract\/\">shawara kan kwantiragi<\/a><\/li>\n<\/ul>\n<ul>\n<li><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.nasw.org\/about-national-association-science-writers-inc\">The National Association of Science Writers <\/a>da ke da mazaunin shi a Berkeley, Carlifornia, ya na da shafi mai kyau kan freelancing, da ma bayyana kan yadda ake yarjejejniyar kwantiragi. Kuna kuma iya karanta\u00a0<a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.nasw.org\/article\/contract-negotiation-getting-what-you-want-gracefully\">Contract Negotiation: Getting What You Want, Gracefully<\/a><b>,\u00a0<\/b>wanda Jennifer Pirtle ta rubuta a 2006.<\/li>\n<\/ul>\n<ul>\n<li><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.sej.org\/library\/freelance\/overview\">The Society for Enviromental Journalists<\/a>: Mai mazauninta a Washington DCwannan kungiyar \u2018yan jarida masu dauko rahotanni dangane da muhalli yana karin bayani kan kwantiragi<\/li>\n<li><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.cjr.org\/watchdog\/freelance-contracts.php\">Abubuwa uku da ya kamata a sani wajen yin yarjejeniya a cewar lauyoyi<\/a>, a wani labarin da Maya Kroth na the Columbia Journalism Review ta rubuta a 2018<\/li>\n<li><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.freelancevoorwaarden.nl\/\">Freelancevoorwaarden.nl<\/a> \u2013 yana dauke da bayanai har ma da manufofin freelancing kan mawallafa a kasar Holland. Kuna iya karanta <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/ijnet.org\/en\/story\/dutch-website-helps-journalists-better-understand-freelancer-agreements\">wannan labarin<\/a> da Linda A. Thombson ta rubuta ma Kungiyar \u2018Yan Jarida na kasa da kasa a 2019<\/li>\n<\/ul>\n<h4><b>Shawarwari daga kwararru a GIJC2019<\/b><\/h4>\n<p>Wasu kwararru sun yi mahawara lokacin babban taron <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/gijc2019.org\/\">GIJC 2019<\/a> a birnin Hamburg na kasar Jamus, imda suka duba batun kwnatiragi musamman ma wadanda ke bincike mai zurfi<\/p>\n<p>Babban abun dauka: Biya bisa yawan kalmomin da mutun ya rubuta a labari, duk da cewa yadda aka saba ke nan ba zai dace da labaran da bincikensu ke daukan lokaci mai tsawo ba.<\/p>\n<p>A maimakon haka, masu maganan sun shawarcin yin yarjejeniyar da za ta tanadar da biya mako-mako ko wata-wata dan lokacin da aka sauka ana bincike da karin da za\u2019a yi daga baya idan an je wallafa. <a href=\"https:\/\/gijn.org\/2019\/11\/05\/tips-for-freelance-investigators-finding-the-story-maximizing-earnings-and-managing-your-business\/\">A cewar bitan<\/a> da <a href=\"https:\/\/gijn.org\/about\/staff-member\/rowan-philp\/\">Rowan Philip<\/a> na GIJN ya yi dangane da mahawarar.<\/p>\n<p>\u201cKuna iya neman wannan kuna biyanin cewa kudin kasha labarin zai kasance da mahimmanci kuma kuna iya neman sakin layin da zai ba ku hakkin mallaka. A kowani kwantiragi ku tabbatar cewa ba\u2019a sa muku wani nauyin da bai dace ba,\u201d a cewar Philip.<\/p>\n<p>Wasu karin bayanan na da mahimmanci, misali sadda za\u2019a biya: Lokacin da aka amince ku yi rubutun, ko daga baya, idan an wallafa.<\/p>\n<p>Batun biya kafin a fara labarin idan kamar zai dauki dogon lokaci kuma zai bukaci kudi sosai? Dangane da wannan batun, freelancers sun ce ana iya tsara biyan ya kasance bayan an cimma wani buri kamar misali a ce idan an kammala hirarraki, sai a biya wani kudi kafin a cigaba.<\/p>\n<p>Idan wani edita na so ya dakatar da labarin fa? Za\u2019a biya wani kudi? Ku yi tunani sanya bayani irin wannan a cikin kwantiragin:<\/p>\n<\/div>\n<\/div>\n<div class=\"elementor-element elementor-element-08b85bf elementor-blockquote--skin-border elementor-blockquote--button-color-official elementor-widget elementor-widget-blockquote\" data-id=\"08b85bf\" data-element_type=\"widget\" data-widget_type=\"blockquote.default\">\n<div class=\"elementor-widget-container\">\n<blockquote class=\"elementor-blockquote\">\n<p class=\"elementor-blockquote__content\">Idan ba\u2019a amince da labarin bam za\u2019a biya dan jaridan wani kudi, kashi 25 cikin 100 na kudin da dama ya kamata a biya<\/p>\n<\/blockquote>\n<\/div>\n<\/div>\n<div class=\"elementor-element elementor-element-dafffc5 elementor-widget elementor-widget-text-editor\" data-id=\"dafffc5\" data-element_type=\"widget\" data-widget_type=\"text-editor.default\">\n<div class=\"elementor-widget-container\">\n<p>Duba wadannan <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/leavingworkbehind.com\/clauses-your-freelance-writing-contract-should-include\/\">shawarwarin kan kudaden<\/a> da ake biya idan ba\u2019a dauki rahoton ba wanda aka dauka daga labarin da Alexander Cordova ya rubuta a 2017.<\/p>\n<ul>\n<li>Ka da ku sa kudi mai mai yawan gaske a matsayin wanda za\u2019a biya idan ba\u2019a dauki rahoton ba. Wannan zai taimake wajen kyautata dangantaka kada a rabu baram-baram<\/li>\n<li>Ku sa farashin ya danganci yawan aikin da kuka riga ku ka yi a kan shirin.<\/li>\n<li>Ku yi tunanin sanya wani dan tazara tsakanin sadda aka sanya hannu kan kwantiragin da lokacin da za\u2019a fara aiki ko da wadanda suka bayar da aikin suna so su fasa.<\/li>\n<\/ul>\n<h4><b>Yarjejeniyar kudi wa manyan labarai<\/b><\/h4>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/www.scottcarney.com\/\">Scott Carney<\/a>, wani dan jarida mai bincike mai zurfi wanda ya rubuta littafi mai suna \u201cQuick and Dirty Guide to Freelance Writing,\u201d wato jagora na rubutu a matsayin mai freelancing ya yarda cewa ana iya tattaunawa a sami kudin da ya wuce wanda ake biya wa manyan labarai.<\/p>\n<p>A <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/psmag.com\/economics\/you-dont\">wata hirar da ya yi<\/a> da jaridar Pacific Standard, Carney ya ce:<\/p>\n<\/div>\n<\/div>\n<div class=\"elementor-element elementor-element-474685e elementor-blockquote--skin-border elementor-blockquote--button-color-official elementor-widget elementor-widget-blockquote\" data-id=\"474685e\" data-element_type=\"widget\" data-widget_type=\"blockquote.default\">\n<div class=\"elementor-widget-container\">\n<blockquote class=\"elementor-blockquote\">\n<p class=\"elementor-blockquote__content\">\u201cwasu marubuta na wa rubutunsu kallon kayan masarufi. A ra\u2019ayi na idan mutun ya fita ya je ya sayar da aikin shi a matsayin aikin gwaninta zai iya samun kudi mai yawan gaske. Gaskiyar ita ce idan ka fita da abin da ake so sosai za ka sami mai saye a farashin da ka ke so. Misali a wani <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/www.rollingstone.com\/politics\/news\/the-runaway-general-20100622\">labarin Roling Stone<\/a> wanda ya sa aka kama General McChrystal. Ya kamata a ce dan jaridan ya sayar da shi wa dubban daloli amma mai yiwuwa ya sayar da shi a kan $2 wa kowace kalma.\u201d<\/p>\n<\/blockquote>\n<\/div>\n<\/div>\n<div class=\"elementor-element elementor-element-c524fe9 elementor-widget elementor-widget-text-editor\" data-id=\"c524fe9\" data-element_type=\"widget\" data-widget_type=\"text-editor.default\">\n<div class=\"elementor-widget-container\">\n<p>Wace shawara Carney ke da shi kan tattaunawa?<\/p>\n<\/div>\n<\/div>\n<div class=\"elementor-element elementor-element-6e57f95 elementor-blockquote--skin-border elementor-blockquote--button-color-official elementor-widget elementor-widget-blockquote\" data-id=\"6e57f95\" data-element_type=\"widget\" data-widget_type=\"blockquote.default\">\n<div class=\"elementor-widget-container\">\n<blockquote class=\"elementor-blockquote\">\n<p class=\"elementor-blockquote__content\">\u201cYa kamata ku yi wa aikinku kallon wani abu mai mahimmancin gaske. Na iya na tattauna kwantiragi. Na iya na samu an maido mun hakkokin mallaka na. Na iya na sami kudade masu yawa wa aiki na bayan da na ki daukan wasu ayyukan. Na kan rubuta labarai daya ko biyu ne a shekara kuma ina iya rayuwa da abin da zan samu. Saboda ina sayar da su wa farashi mai yawa ne. Ina ajiye hakkin mallaka. Ina sake sayar da labarin a kasashen waje. Ana gayyata na in yi magana. Ina kuma sayar da litattafai.\u201d<\/p>\n<\/blockquote>\n<\/div>\n<\/div>\n<div class=\"elementor-element elementor-element-b1b5973 elementor-widget elementor-widget-text-editor\" data-id=\"b1b5973\" data-element_type=\"widget\" data-widget_type=\"text-editor.default\">\n<div class=\"elementor-widget-container\">\n<h5><b>Rike Hakkin Mallaka na da Mahimmanci.<\/b><\/h5>\n<p>Rike hakkin mallakar labari buri ne da kowa ke la\u2019akari da shi, kuma gwawarmaya ne, musamman yadda ya shafi labarai na musamman.<\/p>\n<p>Kwantiragin zai iya fayyaci \u2018yancin da kafar yada labaran ke da shi da wanda ku za ku ajiye. Dokokin sun bambamta a kasashe daban-daban dan haka ku yi naku binciken.<\/p>\n<p>Kafafen yada labarai sun sauya a cewar Jack Davies wanda ya rubuta wani labari a <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.cjr.org\/watchdog\/contract-rights-grab.php\">Columbia Journalism Review a kan \u201ctauye hakkin mallaka\u201d a 2018<\/a>. Davies ya ce ya gano cewa kafafen yada labarai daban-daban su kan karbi duk wani \u2018yancin da dan jarida ke da shi a kan labaransa.\u201d<\/p>\n<p>Su na son kwantiragi \u201cabun da ke hana masu freelancing sama wa ayyukansu lasisi su raba da kafafe daban-daban, su sami riba kan fassara ko ma fim ko littafi, abin da ke barin su da kankanin zabi na wajen da za su sami albashin da zai biya mu su bukatun su,\u201d a cewar Davies.<\/p>\n<p>Wata hanya da za ta taimaka wajen samun \u2018yancin mallaka it ace ku yi tunanin hanyoyin da ku ke so ku sami alfanu. Ga wadansu tambayoyin da za ku yi la\u2019akari da su:<\/p>\n<ul>\n<li>Ya kamata ku mallaki hakki na fina-finai, podcasts da duk wani abun da za\u2019a yi sakamakon aikinku?<\/li>\n<li>Za\u2019a iya sayar da aikinku a wani harshen daban?<\/li>\n<li>Kuna iya wallafa labarin a shafinku na kanku?<\/li>\n<li>Wanda zai sami hakkin mallakar dindindin ne ko na wani tsawon lokaci?<\/li>\n<\/ul>\n<p>Wani gargadin da kowa ya yarda da shi wato \u201cKu ajiye hakkin mallakarku\u201d ya na <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/web.archive.org\/web\/20221015060816\/https:\/\/web.law.columbia.edu\/kernochan\/keep-your-copyrights\/\">shafin<\/a> Columbia Law School ko kuma makarantar shari\u2019a ta Columbia wanda ke bayar da takaitaccen bayani kan dokokin Amurka. Shafin na gargadin cewa:<\/p>\n<\/div>\n<\/div>\n<div class=\"elementor-element elementor-element-017e717 elementor-blockquote--skin-border elementor-blockquote--button-color-official elementor-widget elementor-widget-blockquote\" data-id=\"017e717\" data-element_type=\"widget\" data-widget_type=\"blockquote.default\">\n<div class=\"elementor-widget-container\">\n<blockquote class=\"elementor-blockquote\">\n<p class=\"elementor-blockquote__content\">\u201cIdan kuka zauna baku yi komai ba, zaku kammala rayuwarku na aiki ku ga cewa kun yi abubuwa da yawa da wasu mutane ne suke mallaka ba kai, wadanda watakila ma ba wani abin da ya hada ku.\u201d<\/p>\n<\/blockquote>\n<\/div>\n<\/div>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Kulla yarjejeniya ma bincike mai zurfi a aikin jarida zai yi la\u2019akari da abubuwa da dama wadanda ba su da mahimmanci a misali labarin maguna Akwai mahimman abubuwan da kowani irin labari ke da shi wadanda ya kamata a mayar da hankali a kai wadanda suka hada da: Bayani dangane da suffan aikin da yadda [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":3031153,"featured_media":1050217,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_acf_changed":false,"_price":"","_stock":"","_tribe_ticket_header":"","_tribe_default_ticket_provider":"","_tribe_ticket_capacity":"0","_ticket_start_date":"","_ticket_end_date":"","_tribe_ticket_show_description":"","_tribe_ticket_show_not_going":false,"_tribe_ticket_use_global_stock":"","_tribe_ticket_global_stock_level":"","_global_stock_mode":"","_global_stock_cap":"","_tribe_rsvp_for_event":"","_tribe_ticket_going_count":"","_tribe_ticket_not_going_count":"","_tribe_tickets_list":"[]","_tribe_ticket_has_attendee_info_fields":false,"republication-tracker-tool-hide-widget":false,"footnotes":"","_tec_slr_enabled":"","_tec_slr_layout":""},"categories":[23110],"tags":[],"gijn_topic":[19127],"series":[],"gijn_language":[17798],"gijn_region":[],"class_list":["post-501120","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-albari","gijn_topic-gudanar-da-girgizar-kai","gijn_language-ha-ha"],"acf":[],"ticketed":false,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/501120","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/users\/3031153"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=501120"}],"version-history":[{"count":3,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/501120\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2122620,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/501120\/revisions\/2122620"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/media\/1050217"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=501120"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=501120"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=501120"},{"taxonomy":"gijn_topic","embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/gijn_topic?post=501120"},{"taxonomy":"series","embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/series?post=501120"},{"taxonomy":"gijn_language","embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/gijn_language?post=501120"},{"taxonomy":"gijn_region","embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/gijn_region?post=501120"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}