{"id":500791,"date":"2022-07-13T02:24:57","date_gmt":"2022-07-13T06:24:57","guid":{"rendered":"https:\/\/gijn.org\/?page_id=500791"},"modified":"2023-06-25T07:31:09","modified_gmt":"2023-06-25T11:31:09","slug":"bincike-mai-zurfi-a-aikin-jarida-yadda-ake-gabatar-da-tayin-labarai","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/gijn.org\/ha\/albari\/bincike-mai-zurfi-a-aikin-jarida-yadda-ake-gabatar-da-tayin-labarai\/","title":{"rendered":"Bincike Mai Zurfi a aikin Jarida: Yadda ake gabatar da tayin labarai"},"content":{"rendered":"<div class=\"elementor-element elementor-element-7cd409eb elementor-widget elementor-widget-heading\" data-id=\"7cd409eb\" data-element_type=\"widget\" data-widget_type=\"heading.default\">\n<div class=\"elementor-widget-container\">\n<h3 class=\"elementor-heading-title elementor-size-default\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"aligncenter wp-image-223911 size-full\" src=\"https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2020\/03\/gijnafricaheader-1.png\" alt=\"\" width=\"770\" height=\"187\" srcset=\"https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2020\/03\/gijnafricaheader-1.png 770w, https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2020\/03\/gijnafricaheader-1-336x82.png 336w, https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2020\/03\/gijnafricaheader-1-768x187.png 768w\" sizes=\"auto, (max-width: 770px) 100vw, 770px\" \/><\/h3>\n<\/div>\n<\/div>\n<div class=\"elementor-element elementor-element-bc591a6 elementor-widget elementor-widget-image\" data-id=\"bc591a6\" data-element_type=\"widget\" data-widget_type=\"image.default\">\n<div class=\"elementor-widget-container\">\n<figure class=\"wp-caption\">\n<p><div id=\"attachment_253621\" style=\"width: 2570px\" class=\"wp-caption aligncenter\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" aria-describedby=\"caption-attachment-253621\" class=\"wp-image-253621 size-full\" src=\"https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2020\/07\/young-female-freelancer-using-laptop-at-home-3808008-scaled.jpg\" alt=\"\" width=\"2560\" height=\"1707\" srcset=\"https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2020\/07\/young-female-freelancer-using-laptop-at-home-3808008-scaled.jpg 2560w, https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2020\/07\/young-female-freelancer-using-laptop-at-home-3808008-336x224.jpg 336w, https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2020\/07\/young-female-freelancer-using-laptop-at-home-3808008-771x514.jpg 771w, https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2020\/07\/young-female-freelancer-using-laptop-at-home-3808008-768x512.jpg 768w, https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2020\/07\/young-female-freelancer-using-laptop-at-home-3808008-1536x1024.jpg 1536w, https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2020\/07\/young-female-freelancer-using-laptop-at-home-3808008-2048x1365.jpg 2048w, https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2020\/07\/young-female-freelancer-using-laptop-at-home-3808008-1170x780.jpg 1170w\" sizes=\"auto, (max-width: 2560px) 100vw, 2560px\" \/><p id=\"caption-attachment-253621\" class=\"wp-caption-text\">Image: Pexels<\/p><\/div><\/figure>\n<\/div>\n<\/div>\n<div class=\"elementor-element elementor-element-73f138ad elementor-widget elementor-widget-text-editor\" data-id=\"73f138ad\" data-element_type=\"widget\" data-widget_type=\"text-editor.default\">\n<div class=\"elementor-widget-container\">\n<p>Tayin rahotannin da babu tabbas ko kuma suna dauke da batutuwa masu sarkakiya sun fi wahala saboda suna bukatar yarda tsakanin bangarorin biyu.<\/p>\n<p>Bugu da kari, kudin da za\u2019a kashe wajen yin irin binciken na da yawa, kuma ba lallai ne kwalliya ta biya kudin sabulu ba. Yana da wahala a iya kimanta lokaci da yawan aikin da za\u2019a yi, dan haka da wuya a tantance ko yin binciken zai zama da wani amfani.<\/p>\n<p>Daga karshe yana da hadari. \u2018Yan jarida masu zaman kansu su kan fuskanci kalubale na musamman idan suna aiki kan labarai masu sarkakiya, akwai kuma hadaruka na lafiya da shari\u2019a da kafar yada labaran ba za ta iya daukar nauyi ba.<\/p>\n<p>Duk da haka, bincike mai zurfi a aikin jarida tsakanin \u2018yan jarida masu zaman kansu na da karfi sosai. Ganin cewa suna da \u2018yancin kansu da walwalar zaben labarin da suke so da inda suke so a buga, \u2018yan jarida masu zaman kansu suna samun alheri sosai. Wasu sukan kulla dangantaka da editocin kafofin yada labarai wasu kuma su kan dauki kananan ayyuka a gefe dan toshe wasu kafofin, domin su bunkasa yawan aiki da albashi a matsayin marubuta, malamai ko kuma masu bayar da shawara.<\/p>\n<p>GIJN ta duba irin kalubalen da ake fuskanta wajen sayar da labaran da aka yi mu su bincike mai zurfi ga kuma wadansu daga cikin shawarwarin da suka samu daga kwararru.<\/p>\n<p>Zamu mayar da hankali a kan:<\/p>\n<ul>\n<li>Neman kafafen tarayya<\/li>\n<li>Gabatar da tayi mai kwari<\/li>\n<li>Kare ra\u2019ayoyi<\/li>\n<li>Tantance kasafin kudin<\/li>\n<\/ul>\n<p>Baya da wannan GIJN ta kuma hada wani jadawali na shawarwari da dabarun da za su taimkawa \u2018<a href=\"https:\/\/gijn.org\/tips-and-strategies-freelancing-during-the-covid-19-pandemic\/\">yan jarida masu zaman kansu lokacin\u00a0COVID-19<\/a>.<\/p>\n<h4><b>Samun Kafofi<\/b><\/h4>\n<p>Akwai bukatar aminci da yarda tsakanin kafafen yada labarai da \u2018yan jarida masu bincike mai zurfi dan haka ne ma yawanci ke son hulda da wanda suka riga suka sani.<\/p>\n<p>Kulla dangantaka da labarai na yau da kullun daga farko ya fi domin farawa da irin labaran da ke bukatar bincike mai zurfi zai yi wahala,<\/p>\n<p>Wata shawara kuma ita ce haduwa da editocin da ku ka san za su so labarin a irin manyan tarukan \u2018yan jarida ko kuma taron karawa juna sani.<\/p>\n<p><b>Yin Bincike<\/b><\/p>\n<p>Lokacin bincike ka da ku duba kafofin da ke wallafa rahotannin bincike mai zurfi kadai, ku duba har da kafofin da ke da sha\u2019awar batun da ku ke so ku rubuta a kai. Da wannan a hannu, kuna iya cigaba da binciken:<\/p>\n<ul>\n<li>Karanta abin da suka taba rubutuwa dangane da batun a baya da ma sauran batutuwan da su ka yi rubutu a kai<\/li>\n<li>Fahimci salon rubutunsu da irin matsayin da su ke dauka<\/li>\n<li>Ku lakanci kudurinsu\/manfofinsu<\/li>\n<li>Duba manyan editocinsu<\/li>\n<li>Tambaya ko ku kan ku ko wani da ku ka sani ya san wani a wurin ta yadda zai bude muku kofar shiga<\/li>\n<\/ul>\n<p>Ku duba kasuwanni da dama dan sayar da labarin \u201cku yi amfani da duk wata dabara da kuka sani na neman labarai\u201d kamar yadda Rowan Philip na GIJN ya kwatanta a kasidar da ya\u00a0<a href=\"https:\/\/gijn.org\/2019\/11\/05\/tips-for-freelance-investigators-finding-the-story-maximizing-earnings-and-managing-your-business\/\">gabatar a GIJN 2019<\/a>\u00a0mahawarar da aka yi kan freelancing.<\/p>\n<p>\u201cYa kamata \u2019yan jarida masu zaman kansu wadanda ke bincike mai zurfi su rika samun kafofi da yawa na sayar da labaransu ma kowani labari da za su rubuta, idan har aikinsu zai dore,\u201d ya rubuta, Rowan shi kan shi ya dade yana freelancing.<\/p>\n<p>Wadanda suka kasance a mahawaran sun kwatanta kafofi da dama, a ciki har da Jarida, hotuna, da rediyo wanda zai kara yawan kudaden shiga.<\/p>\n<p><b>Gabatar da tayin<\/b><\/p>\n<\/div>\n<\/div>\n<div class=\"elementor-element elementor-element-d3e3c33 elementor-widget elementor-widget-image\" data-id=\"d3e3c33\" data-element_type=\"widget\" data-widget_type=\"image.default\">\n<div class=\"elementor-widget-container\">\n<figure class=\"wp-caption\">\n<p><div style=\"width: 778px\" class=\"wp-caption alignnone\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"attachment-medium_large\" src=\"https:\/\/thecjid.org\/wp-content\/uploads\/2022\/04\/Freelance-graphic-771x645-1-768x642.png\" alt=\"\" width=\"768\" height=\"642\" \/><p class=\"wp-caption-text\">Image: <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/undraw.co\/\">unDraw<\/a><\/p><\/div><figcaption class=\"widget-image-caption wp-caption-text\"><span style=\"font-size: 19.55px\"><span style=\"font-size: 19.55px\"><span style=\"font-size: 19.55px\">Da zarar kun tantance wuraren da ku ke so ku wallafa rahotanninku sai ku shirya tayi.<\/span><\/span><\/span>Yawancin hanyoyin da aka saba sayar da labaran yau da kullun ne ake amfani da su a labarin da zai bukaci bincike mai zurfi. Ya kamata tayin ya zama takaitacce kuma mai jan hankali.\u00a0<\/figcaption><\/figure>\n<\/div>\n<\/div>\n<div class=\"elementor-element elementor-element-d8f8e61 elementor-widget elementor-widget-text-editor\" data-id=\"d8f8e61\" data-element_type=\"widget\" data-widget_type=\"text-editor.default\">\n<div class=\"elementor-widget-container\">\n<p>\u201cYa kamata ku ja ra\u2019ayin edita ko duk wanda ke sauraro cewa ku ne ku ka dace ku yi wannan labarin saboda kuna da msaniya, majiyoyi da kwarewar da ake bukata da sauransu, ko kuma ka sami wasu takardun da ba kowa ke sane da sub a,\u201d a cewar\u00a0<a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/twitter.com\/clobo_guerrero?lang=en\">Catalina Lobi-Guerrero<\/a>, wata \u2018yar jarida mai zaman kanta a Columbia kuma tsohuwar editan GIJN wadda ke da shekaru sama da 10 na gogewa.<\/p>\n<p><b>Shawarwari daga editoci<\/b><\/p>\n<p>Editan jaridan The Atlantic\u00a0<a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/twitter.com\/SStossel?ref_src=twsrc%5Egoogle%7Ctwcamp%5Eserp%7Ctwgr%5Eauthor\">Scott Stossel<\/a>\u00a0ya bayar da manyan shawarwarin shi a wata hirar da\u00a0<a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.banffcentre.ca\/articles\/how-write-good-pitch-tips-editor-atlantic\">ya yi a 2017<\/a>:<\/p>\n<ul>\n<li>Ku dan fara rahoton ku tabbatar cewa kun yi tunanin yadda zai kasance<\/li>\n<li>Ku cike duk wani gibi. Ku gano wadanda abin ya shafa, abubuwan da wadanne irin hadurruka za\u2019a fuskanta kuma me ya sa labarin ke da mahimmanci<\/li>\n<li>Ku nuna kwarewarku a rubutu. Tayin kan shi ya kasance kamar labari kuma ya gabatar da wata kusurwar da za\u2019a fayyace.<\/li>\n<li>Ku sami wani dan wasan kwaikwayo. A fayyace wasan kwaikwayon sosai a tayin<\/li>\n<li>Fahimci mahimmancin labarin. Ku tabbata kun danganta shi da abin da ke faruwa a labarai<\/li>\n<li>Ka da ya kasance tsohon labari<\/li>\n<\/ul>\n<p>Bisa bayanan <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/www.investigative-manual.org\/\">takardar jagorar bincike mai zurfi a aikin jarida<\/a>, daya daga cikin shirye-shiryen Kafafen yada labarai na duniya na gidauniyar Konrad Adenauer. Duk wani tayi ya kasance yana da.<\/p>\n<ul>\n<li>Takaitaccen labarin<\/li>\n<li>Abin da ya sa labarin ya dace da jaridar ko wadanda ke karantawa<\/li>\n<li>Gajeren bayani kan yadda za\u2019a sami labarin da irin matakan da za\u2019a dauka<\/li>\n<li>Tsawonlokacin da zai dauka<\/li>\n<li>Kasafin kudi<\/li>\n<\/ul>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/twitter.com\/sarahblustain?lang=en\">Sarah Blustain<\/a>, babban editan Type Investigations ta shirya wata <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.typeinvestigations.org\/wp-content\/uploads\/2017\/09\/How-to-write-a-strong-story-proposal-tipsheet.pdf\">takardar shawarwari<\/a> kan rubuta tayin da ke jaddada cewa ya kasance \u201ctakaitacce,\u201d \u201ckai tsaye,\u201d \u201csa\u2019annan ku baiwa editoci abin da su ke bukata su kai labarinku kan tsanin labaran kafofinsu,\u201d a cewar ta yawanci ta na bayar da shawarar cewa tayin ya kunshi sakin layi hudu da mahimman abubuwa guda hudu:<\/p>\n<ul>\n<li>Mene ne labarin<\/li>\n<li>Me ya sa ya ke da mahimmanci \u2013 me ya sa ya ke da mahimmanci yanzu.<\/li>\n<li>Me bincike ke nunawa<\/li>\n<li>Me ya sa ku za ku rubuta<\/li>\n<\/ul>\n<p>Mother Jones, wata kasidar Amurka da ke wallafa labaran bincike mai zurfi ta jaddada wadannan shawarwari a littafin da ake kira\u00a0<a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.motherjones.com\/contribute\/writer-guidelines\/\">Freelance Writer Guidelines<\/a>:<\/p>\n<p>\u201cFada mana a sakin layi \u2018yan kalilan abin da za ku rubuta a labarin, abin da ya sa ya ke da mahimmanci ko ban sha\u2019awa, da kuma yadda za ku yi labarin. Ya kamata tayin ya nuna matsayin da za ku dauka, murya da salo. Ya kuma kamata ya amsa wadannan tambayoyin: Wani kwarewa ku ke da shi ku rubuta wannan labarin? Yaya dangantakarku ta ke da majiyoyin ku? Idan an riga an yi wasu labarai dangane da wannan batun, me zai banbanta na ku \u2013 ya inganta shi??<\/p>\n<p>Ku rubuta kadan game da ku da biyu ko uku na ayyukan da ke ka taba yi.<\/p>\n<p>Wannan labarin na kafar yada labaran Nieman ne da aka wallafa a 2018 \u2013\u00a0<a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/niemanstoryboard.org\/stories\/the-pitch-at-the-guardians-long-read-no-rigid-formula-or-geographic-limits\/\">The Pitch: At the Guardian\u2019s Long Read, No rigid formula or Greographic Limits<\/a>\u00a0\u2013 Ba kan bincike mai zurfi ne kadai ba kuma yana fadan gaskiya kan irin wahalar da ake sha. \u201cShawarar edita: Ku yi nazarin abun da aka wallafa a baya. Ku kwatanta cewa kun san abin da ku yi, ku kuma ja hankali.\u201d<\/p>\n<p>Duk da cewa an rubuta da burin neman tallafin kudi ne, wannan kasidar da<a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/twitter.com\/EricKarstens\">\u00a0Eric Karsten<\/a>\u00a0ya rubuta a 2016 mai taken<a href=\"https:\/\/gijn.org\/2018\/05\/16\/how-not-to-win-a-journalism-grant\/\">\u00a0How Not to Win Jornalism Grant<\/a>, wato Yadda Bai Kamata a Sami Tallafin Aikin Jarida Ba, wanda GIJN ta sake wallafawa a 2018 na da shawarwari masu kyau.<\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/thewholestory.solutionsjournalism.org\/what-editors-are-looking-for-in-solutions-pitches-f45b4d3e3b22\"><b>Abin da Editoci Ke Nema a Tayi <\/b><\/a>Kashi na biyu na jerin rubuce-rubuce a kan gabatar da tayi wa kungiyar hadin-kan Journalim Solutions a 2018, Julia Hotz ra fadada wadannan batutuwan guda takwas:<\/p>\n<ol>\n<li>Amsa mai gamsarwa dangane da tambayar \u201cMe ya sa masu sauraro\/karatu za su damu?\u201d<\/li>\n<li>Alamar cewa kun yi bayar da labari kuma akwai labarin bayarwa<\/li>\n<li>Hujjoji \u2013 masu yawo ko masu inganci \u2013 dangane da tasirin da labarin zai yi<\/li>\n<li>La\u2019akari da koma bayan da tasirin da kuma yadda za\u2019a sanya ido a kai<\/li>\n<li>Takaitaccen bayani na yadda labarin zai fara da yadda komai zai tafi daga baya<\/li>\n<li>Bayanin kan yadda ka ku rawaito labarin da dalilin ya sa ku ne ku ka dace ku yi rahoton<\/li>\n<li>Kanun da zai talata mahimmancin labarin ya kuma nuna cewa labarin ba zai tsufa ba<\/li>\n<li>Fahimtar abin da kafar watsa labaran ke yi (da wanda ba ya yi)<\/li>\n<\/ol>\n<p>Kashin farko na labarin na <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/thewholestory.solutionsjournalism.org\/how-to-prepare-a-solutions-pitch-10-tips-from-journalists-in-our-network-2912de9b2e20\">hade da wani labarin ne (companion piece)<\/a> wanda ya tsokaci kan matakan farko na rubuta tayi, yayin da kashin karshe shi kuma ya kawo misalan taye-tayen da suka yi nasara.<\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.niemanlab.org\/2018\/10\/how-to-successfully-pitch-the-new-york-times-or-well-anyone-else\/\">Yadda ake nasarar yin tayi ga jaridar New York Times (ko wani<\/a>) wanda Tim Herrera ya rubuta yana kunshe kurarai ukun da \u2018yan jarida suka cika maimaitawa,\u201d farawa da \u201cBa ku san mene ne labarin ku ba.\u201d<\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/writingcooperative.com\/why-your-pitch-was-turned-down-from-the-editors-themselves-d6a3350ec007\">Abin Da Ya Hana Daukar Tayin Ku \u2013 Daga Bakin Editocin Da Kansu<\/a>\u00a0\u2013 Shawarwari daga editocin manyan jaridu wadanda Ben Sledge ya yi hira da su.<\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.spj.org\/freelance-pitching-resources.asp\">One good list<\/a>\u00a0shawarwari ne na kafafen yada labarai dangane da irin abubuwan da suke so masu tayin rahotanni su kula da su,wanda kungiyar \u2018yan jarida kwararru na Amurka ta wallafa.<\/p>\n<p><b>Kafofin yada labaran da suka kunshi bincike mai zurfi na bukatar da yawa daga wurin dan jarida<\/b><\/p>\n<p>Sjafukan kafafen yada bincike mai zurfi su kan bayyana irin abubuwan da su ke nema. Duk da cewa kusan ko wanne na da abin da ya ke so, akwai wasu batutuwan da su ka zo daya.<\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.revealnews.org\/pitching-reveal\/\">Reveal<\/a>, gidan rediyon bincike mai zurfi na Amurka wanda ke karkashin jagorancin Cibiyar Labaran Bincike Mai Zurfi kan bukaci bayanai da yawa kuma su kan yi tambayoyi masu wuyan amsawa.<\/p>\n<p>Takardar cikawa dan neman aikin da su ya fara kamar kowanne, yana fadawa \u2018yan jarida cewa cikin kalmomi 500 su rubuta \u201ckadan daga cikin abin da labarin zai kunsa da kuma tambayar da zai amsa.\u201d<\/p>\n<p>Akwai kuma wasu karin tambayoyin da suka hada da:<\/p>\n<ul>\n<li>Su wa abin ya shafa?<\/li>\n<li>Me ke sa labarin kasancewa abin da ya shafi kasa baki daya?<\/li>\n<li>Me ya mayar da shi labari mai kayatarwa irin wanda za\u2019a sa a rediyo?<\/li>\n<\/ul>\n<p>Sai su kuma editocin na Reveal su ka cigaba da zurfafa tambayoyin su ka kara wasu guda tara wadanda su ka hada da:<\/p>\n<ul>\n<li>Bayyana bayanai biyar da ku ka riga kuka samu ko kuma ku ke aikin samowa<\/li>\n<li>Yi mana bayani kan wadanda abin ya shafa da irin wuraren da ku ke sa ran nadan bayanansu<\/li>\n<li>Su wa suka taba yin wannan labarin (bamu adiresoshin intanet ko wata hujja) ta yaya na ku zai banbanta?<\/li>\n<\/ul>\n<h5><b>Fuskantar rashin tabbas<\/b><\/h5>\n<p>A kan iya fuskantar rashin tabbas idan labari bai kasance yadda aka zata ba tun farko, amma wannan bai kamata ya zama koma baya ba.<\/p>\n<p>Lobo Guerrero ta ce: \u201cWata kila daya daga cikin hanyoyin yin tayin labarin bincike mai zurfi shi ne a bayyana cewa: Ga abin da na ke fatan samu, idan har na iya cimma wannan buri, amma ko ma ban samu ba, zai iya zama labari domin \u2026\u2026 (ku bayana abin da ku ka shirya dama) ko abin da editoci ke kira karamin labari da babban labari.\u201d<\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.osce.org\/albania\/201276?download=true\">Wannan jagoran na<\/a> 2015 Kungiyar Yan Jarida Masu Bincike Mai Zurfi a Yankin Balkan (BIRN) na da wasu sassa masu dimbin amfani wajen tantance labari da kwatanta abin da zai iya zama babban labari da wanda zai iya zama karami. Yana rubuce ne a turanci.<\/p>\n<h5><b>Abin da Ya Kamata a Cire?<\/b><\/h5>\n<p>Akwai matsala duk sadda mutun yake da babban labarin da ya ke so ya saida. Ta yaya mutun zai bayyana labarin cikin kariya ba tare da ya bayar da komai ba? Dole ne tayin ya kasance kai tsaye, amma kuma bai kamata a fadi abubuwa da yawa ta yadda za\u2019a iya amfani da bangaren labarin a wani wuri ba.<\/p>\n<p>Blustain na bayar da shawarar cewa: \u201cBai kamata ku rubuta abubuwa da yawa dangane da binciken da ku ka yi ku baiwa wata kafar da za ta iya baiwa na ta mai daukan rahotannin ya je ya yi labarin ba.\u201d Ta yi gargadi sosai kan bayar da majiyoyi.<\/p>\n<p>Idan har kun ga kamar kuna iya yarda da kafar ku sa a yi muku yarjejeniyar cewa ba za su fadawa kowa ba (NDA Non-disclosure agreement) ba dole ne sai an yi shi cikin wani babban turanci ba.<\/p>\n<p>\u201cKafa (X) ta amince ba za ta wallafa binciken da ke kunshe a tayin da marubuci (X) ya yi ba tare da masaniyar shi ba.\u201d<\/p>\n<p>Samantha Sunne ce ta tsara wannan turancin. Sunne \u2018yar jarida ce mai zaman kanta New Orleans, Louisiana, wadda ke wallafa wata wasikar labarai da ake kira Tools for Reporters.<\/p>\n<p>\u201cWatakila NDA ya yi yawa, ya danganci aikin,\u201d ta ce a wani rubutun da ta yi a 2018. \u201cBa zan ce a yi haka wa kowani labari ba saboda na gwada da wani editan da ban taba aiki da shi ba, sai ya ki daukan labarin kawai.\u201d Yanzu Sunne ta fadawa GIJN cewa tana aiki da mutanen da take ganin ba sai an kai ga neman irin wannan yardar ba.<\/p>\n<p>Kwararru a wannan fanin sun ce abin da ko daya bai kamata ku bayyana ba su ne majiyoyi da bayanan da kuke da shi.<\/p>\n<p>Sunne ta bayar da shawarar cewa hanyar sauki na samun tabbacin cewa ba za\u2019a yi muku satar bayanai ba shi ne a ce su rubuta a email.<\/p>\n<p>Ga \u2018Yan Jarida masu zaman kansu da dama, yadda ce komai. Wadanda suka dade suna aiki da juna, ko daya ba suwa damuwa. Wadansu kafafen kuma suna bayar da mahimmanci ga kare hakkokin marubuta.<\/p>\n<p>Type Investigations, misali, yana daukar matsayi na sirri:<\/p>\n<p>\u201cMun dauki hakin kare labaranku da gaske; Ba zamu baiwa wani banda editocinmu da suka riga suka gani ba. Mun kuma fahimci cewa watakila labarinku na da batutuwa masu sarkakiya. Idan kuna shakkan tura manan bayanan ta email ku sanar da mu domin mu shirya hanyar ta daban dan karbar labarin cikin kariya.\u201d<\/p>\n<h5><b>Calculating Costs<\/b><\/h5>\n<\/div>\n<\/div>\n<div class=\"elementor-element elementor-element-120fb27 elementor-widget elementor-widget-image\" data-id=\"120fb27\" data-element_type=\"widget\" data-widget_type=\"image.default\">\n<div class=\"elementor-widget-container\">\n<figure class=\"wp-caption\">\n<p><div style=\"width: 778px\" class=\"wp-caption alignnone\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"attachment-medium_large\" src=\"https:\/\/thecjid.org\/wp-content\/uploads\/2022\/04\/Spreadsheet-771x508-1-768x506.png\" alt=\"\" width=\"768\" height=\"506\" \/><p class=\"wp-caption-text\">Image: <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/undraw.co\/\">UnDraw<\/a><\/p><\/div><figcaption class=\"widget-image-caption wp-caption-text\"><span style=\"font-size: 19.55px\">Shirya kasafin kudi na da mahimmanci wajen tabbatar da yin riba a aikin jarida na sa kai.<\/span><\/figcaption><\/figure>\n<\/div>\n<\/div>\n<div class=\"elementor-element elementor-element-c43ecc2 elementor-widget elementor-widget-text-editor\" data-id=\"c43ecc2\" data-element_type=\"widget\" data-widget_type=\"text-editor.default\">\n<div class=\"elementor-widget-container\">\n<p>Idan mutun ya riga ya san abubuwan da zai kashe wa kudi zai iya sanin farashin da zai sanya wa aiki ya kuma san sadda zai ce ba zai dauki aiki ba idan kudin da ake tayawa ya yi kankanta sosai.<\/p>\n<p>\u201cBayan da na yi \u2018yan shekaru ina yin bincike mai zurfi a matsayi na na \u2018yar jarida mai zaman kanta, sai na kirkiro da salon da na ke kira \u2018tiers\u2019\u201d a <a href=\"https:\/\/gijn.org\/2018\/11\/21\/a-tiered-approach-to-researching-and-pitching-investigative-stories-for-freelance-writers\/\">cewar<\/a> Sunne.<\/p>\n<p>Ma kowane tier, ta kwatanta irin himmar da za ta sanya wajen nemo ra\u2019ayoyi; \u201cDalilin yin hakan na da sauku: ban so in yi komai da komai \u2013 Hira, samo bayani, kasha kudin tafiya \u2013 Idan har ba abin da zan samu. Idan har ban sami yarjejeniya ba ko kuma ba editan da ya dauki labarin zan ajiye.<\/p>\n<p>Sauran \u2018yan jaridan masu zaman kansu sun yarda: Ku zauna cikin shirin kin karbar ayyukan da ba su da riba.<\/p>\n<p>Wani dalili na yin kasafin kudi kuma shi ne dan a iya sanin wuraren da za\u2019a kashe kudin a kan kari kada a shiga matsala daga baya.<\/p>\n<p>Emmanuel Freudenthal kwararren dan jarida mai zaman kan shi ya rubuta <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.instagram.com\/p\/B28yTH9nM-n\/\">shawarwari 6<\/a> na yadda \u2018yan jarida masu zaman kansu za su iya rayuwa lokacin babban taron <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/gijc2019.org\/tipsheets\/\">GIJN na 11<\/a>.<\/p>\n<hr \/>\n<p><strong><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/twitter.com\/tobyjmcintosh\"><i><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignleft size-thumbnail wp-image-256609\" src=\"https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2020\/07\/Toby-McIntosh-140x140-1-1-140x140.jpg\" alt=\"\" width=\"140\" height=\"140\" srcset=\"https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2020\/07\/Toby-McIntosh-140x140-1-1.jpg 140w, https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2020\/07\/Toby-McIntosh-140x140-1-1-60x60.jpg 60w\" sizes=\"auto, (max-width: 140px) 100vw, 140px\" \/>Toby McIntosh<\/i><\/a><\/strong><i><strong>\u00a0<\/strong>mai bayar da shawara ne a GIJN. Ya yi aiki a <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.bna.com\/\">Bloomberg BNA<\/a> a Washington na tsawon shekaru 39. Tsohon edita ne na <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/freedominfo.org\/\">freedominfo.org<\/a> (2010-2017) inda ya rubuta manufofin FOI a duniya baki daya. Yana rubutu a taskar blog mai suna <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/eyeonglobaltransparency.net\/\">eyeonglobaltransparency.net<\/a><\/i><\/p>\n<\/div>\n<\/div>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Tayin rahotannin da babu tabbas ko kuma suna dauke da batutuwa masu sarkakiya sun fi wahala saboda suna bukatar yarda tsakanin bangarorin biyu. Bugu da kari, kudin da za\u2019a kashe wajen yin irin binciken na da yawa, kuma ba lallai ne kwalliya ta biya kudin sabulu ba. Yana da wahala a iya kimanta lokaci da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":3031153,"featured_media":0,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_acf_changed":false,"_price":"","_stock":"","_tribe_ticket_header":"","_tribe_default_ticket_provider":"","_tribe_ticket_capacity":"0","_ticket_start_date":"","_ticket_end_date":"","_tribe_ticket_show_description":"","_tribe_ticket_show_not_going":false,"_tribe_ticket_use_global_stock":"","_tribe_ticket_global_stock_level":"","_global_stock_mode":"","_global_stock_cap":"","_tribe_rsvp_for_event":"","_tribe_ticket_going_count":"","_tribe_ticket_not_going_count":"","_tribe_tickets_list":"[]","_tribe_ticket_has_attendee_info_fields":false,"republication-tracker-tool-hide-widget":false,"footnotes":"","_tec_slr_enabled":"","_tec_slr_layout":""},"categories":[23110],"tags":[],"gijn_topic":[19127],"series":[],"gijn_language":[17798],"gijn_region":[],"class_list":["post-500791","post","type-post","status-publish","format-standard","hentry","category-albari","gijn_topic-gudanar-da-girgizar-kai","gijn_language-ha-ha"],"acf":[],"ticketed":false,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/500791","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/users\/3031153"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=500791"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/500791\/revisions"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=500791"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=500791"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=500791"},{"taxonomy":"gijn_topic","embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/gijn_topic?post=500791"},{"taxonomy":"series","embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/series?post=500791"},{"taxonomy":"gijn_language","embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/gijn_language?post=500791"},{"taxonomy":"gijn_region","embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/gijn_region?post=500791"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}