{"id":462790,"date":"2022-05-02T01:57:49","date_gmt":"2022-05-02T05:57:49","guid":{"rendered":"https:\/\/gijn.org\/?page_id=462790"},"modified":"2025-07-09T11:47:35","modified_gmt":"2025-07-09T15:47:35","slug":"working-with-whistleblowers-aiki-da-masu-fallasa-bayanan-sirri","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/gijn.org\/ha\/albari\/working-with-whistleblowers-aiki-da-masu-fallasa-bayanan-sirri\/","title":{"rendered":"Working with Whistleblowers\/ Aiki da masu fallasa bayanan sirri"},"content":{"rendered":"<p>Whistleblowers ko kuma masu fallasa bayanan sirri \u2013 ma\u2019aikata wadanda ke fallasa haramtattun ayyuka da karbar cin hanci da rashawa \u2013 suna da mahimmanci wajen samo irin bayanan da \u2018yan jarida ke bukata. Daga inda suke aiki cikin gwamnatoci, kamfanoni da sauran kungiyoyi za su iya bayar da hujjoji da irin alamun da ake bukata domin fallasa abubuwa, kama daga zamba da almubazaranci har zuwa miyagun aiyuka, makirci da miyagun laifukan yaki.<\/p>\n<p>Sai dai ya na da mahimmanci \u2018yan jarida su tantance manufar masu fallasar domin su iya tantance bayanan da su ke bayarwa. Haka nan kuma yana da mahimmanci a san yadda za\u2019a kare su a matsayin majiyoyin labarin.<br \/>\nAn yi sa\u2019a akwai bayanai da dama kan fallasa, har da karuwar da aka samu a yawan kungiyoyi masu zaman kansun da ke da kwarewa ta wannan fanin a kasashen duniya.<\/p>\n<p>Domin taimakwa \u2018yan jarida su bi diddigin irin wadannan labaran a yanayi mai kalubalen gaske, GIJN ta kirkiro kundin da ya jera irin wadannan wurare na samun taimako. Idan har akwai wanda kuke ganin ba mu sa ba, rubuto mana ta adireshinmu\u00a0<a href=\"mailto:hello@gijn.org\">hello@gijn.org<\/a>.<\/p>\n<blockquote>\n<h5><strong>Fallasa shi ne idan na miji ko na mace wanda, saboda imanin da ya\/ta yi da kare darajar al\u2019umma, ya\/ta yi watsi da bukatun kamfanin da ya\/ta ke aiki dan ya\/ta fito fil ta tona duk wani abun da kamfanin ya ke yi da ya shafi karbar cin hanci da rashawa, haramtacce, zamba, ko kuma yana iya raunata jama\u2019a.<\/strong><\/h5>\n<h5><em><strong>\u2013 Ralph Nader, Mai bayar da shawara da kuma fafutukar kare hakkin jama\u2019a.<\/strong><\/em><\/h5>\n<\/blockquote>\n<hr \/>\n<h4><strong>Guidance from Experts\/Shawarwari daga kwararru<\/strong><\/h4>\n<p>Idan har masu fallasa sun amince su bayar da bayanai, wajibi ne su sami kulawa ta musamman.<\/p>\n<p>GIJN ta takaita wadansu mahimman sharudda na aiki da masu fallasa daga majiyoyi iri-iri. Rahoton na kunshe da cikakken bayani kuma ya dace a karanta.<\/p>\n<p><strong><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/whistleblowingnetwork.org\/WIN\/media\/pdfs\/Journalism-Sources-INT-Blueprint-2018-Perugia-Principles-for-Journalists.pdf\">The Perugia Principles for Journalists\/ Ka\u2019idoji ma \u2018yan jarida na Perugia<\/a>,<\/strong>\u00a0wanda aka yi wa taken \u201cAiki da Masu Fallasa a zamanin Dijital.\u201d A shekarar 2019 aka fara wallafawa, Julie Posetti, Dr. Suelette Dreyfus da Naomi Colvin suka rubuta. Marubutan sun kirkiro ka\u2019dojin na Perugia lokacin wata tattaunawa ta musamman tare da tallafin wasu \u2018yan jaria na kasa da kasa da kwararru 20. Kungiyar Blueprint for Free Speech, wadda ke fafutukar kare hakkin \u2018yan jarida na fadan albarkacin baki da ke birnin Perugia a Italy ce ta dauki nauyin tattaunawar a watan Afrilun 2018. Bayan nan ne marubutan suka sake ganawa da kwararru a fannin bincike a aikin jarida, lauyoyi da masan illimi domin kwaskware ka\u2019idoji 12 da suka gindaya.<\/p>\n<ol>\n<li style=\"list-style-type: none\">\n<ol>\n<li>Da farko, a kare majiyoyi. Kada a bayyana sunayensu sadda aka tambaya.<\/li>\n<li>Sadda za ku sada a karon farko, idan zai yiwu, ku tabbatar cewa hanyoyin yin hakan nagartattu ne kuma za sub a su kariya.<\/li>\n<li>Ku yi la\u2019akari da hadarin da mai fallasa zai iya fuskanta, dan haka ku sa su su yi tunanin gaba da yadda za su tafiyar da rayuwarsu bayan labarin ya fita.<\/li>\n<li>Ku tantance bayanin kuna bayar da fifiko kan darajar da bayanin ke da shi ga ci-gabar al\u2019umma ba ra\u2019ayinka ba ko kuma halayya ko ra\u2019ayin mai fallasar ba.<\/li>\n<li>Ku dauki nauyin kare kan ku a duniyar yanar gizo ku yi amfani da lambobi masu sarkakiya wadanda ake kira \u201cencryption\u201d a turance. Duk da cewa ba lallai ne encryption ya kare majiyoyinku ba, ya na bayar da kariya a matakin farko.<\/li>\n<li>Ku tantance abubuwan da za su kasance barazana mafi hadari gare ku da majiyoyinku, da kuma irin matakan da ya kamata ku dauka dan kare juna.<\/li>\n<li>Ku bayyana wa majiyarku irin hadarin da ke tattare da bayyana abu a yanar gizo. Idan labarai masu sarkakiya ne ku koya wa majiyoyinku mahimman matakan kare kai a yanar gizo.<\/li>\n<li>Ku wallafa duka bayanan da kuka samu na ainihi idan da hali kuma babu wani hadari, yin hakan na da mahimmanci ga labarai.<\/li>\n<li>Ku yi amfani da amintattun hanyoyi wajen goge bayanan da amsu fallasar suka bayar, idan har an tambaya, domin ku sakaye sunayen mahiyoyin, abin da ya zo daidai da matakan da\u2019a da doka da nauyin da ya rataya a kan mai aiki.<\/li>\n<li>Ku tabbata duk hanyoyin musayar bayanan da aka yi amfani da su a yanar gizo, irin su drop box suna da kariya mai inganci, sa\u2019annan wa bayanan da ke dauke da sirri a tabbatar an sakaya sunayensu.<\/li>\n<li>Ku fahimci kadar, yankin da dokokin kasa da kasa na kare majiyoyin da suka bayar da bayani a boye ko kuma suka yi fallasa.<\/li>\n<li>Ku baiwa masu wallafa jaridu karfin gwiwar aiwatar da nauyin da ya rataya a wuyarsu na tabbatar da tsaro ga bayanan \u2018yan jarida, majiyoyi da bayanan da aka boye tare da irin horaswar da ta dace da kuma manufofin da za su jagoranci \u2018yan jaridar.<\/li>\n<\/ol>\n<\/li>\n<\/ol>\n<p><strong><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/gijc2019.org\/2019\/09\/28\/10-tips-for-journalists-working-with-whistleblowers\/\">10 tips for Journalists working with Whistleblowers\/ Shawarwar 10 ma \u2018yan jaridan da ke aiki da masu fallasa<\/a>.<\/strong>\u00a0Wannan labarin da Rowan Philp ya rubuta a 2019 ya takaita mahimman sakonnin masu gabatarwa a babban taron GIJC, wanda aka yi a 2019 a birnin Hamburg na kasar Jamus.<\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.whistleblower.org\/guide-journalists\/\"><strong>Working with Whistleblowers: A Guide for Journalists\/ Aiki da masu fallasa: Shwarwari ga \u2018yan jarida<\/strong><\/a>\u00a0\u2013 Kungiyoyin Amurka biyu ne suka buga wannan littafin: Shirin sanya ido a kan gwamnati (GAP) daya daga cikin manyan kungiyoyin fallasa masu zaman kansu, da Al\u2019ummar \u2018Yan jarida Kwararru (society of Professional Journalists). A 2017 aka wallafa. \u201cmuna fatan taimakawa \u2018yan jarida su kare masu fallasa a maimakon kyale su, su fuskanci ramuwar gayya,\u201d a cewar gabatarwar takardar mai shafuka 36. Ya kuma kara da wadannan shawarwarin:<\/p>\n<ol>\n<li style=\"list-style-type: none\">\n<ol>\n<li style=\"list-style-type: none\">\n<ul>\n<li>Domin hadarin afkuwar ramuwar gayya a kan masu fallasar yana da yawa kuma dokokin na da sarkakiya, \u2018yan jarida da majiyoyi za su sami tallafi sosai idan suka hada gwiwa da GAP da sauran lauyoyin da suka lakanci dokokin fallasa kafin su yi amfani da bayanan da suka samu daga majiyoyi.<\/li>\n<li>Ka da \u2018yan jarida su sanya kan su a cikin labari; Kai ba mai bayar da shawara ne ko dabaru, kuma kai ba lauya ba ne. Amma ta sa yardar ka da nuna fahimtar cewa akwai matakai na musamman wajen tinkarar labaran da ke da alaka da majiyoyi na fallasa, ka na iya taimakwa a sami rahotanni masu bayanan da ke da darajan gaske ga al\u2019umma, yayin da ake daukan matakan da za su kare majiyarka.<\/li>\n<li>Idan wani ma\u2019aikaci ya tinkare ka da bayanai dangane da kura-kurai masu tsananin gaske, ko da batun ya danganci tauya hakkin dana dam, barazana ga muhakki ko kuma hadari ga tsaron kasa, \u2018yan jarida su yi hankali wajen tattaunawa da ma\u2019aikacin domin su tabbatar da cewa mutumin ya yi la\u2019akari da duk zabubbukan da yake da shi dangane da hanyar da ta fi dacewa ya kai bayanan da ya ke so ya bayar.<\/li>\n<\/ul>\n<\/li>\n<\/ol>\n<\/li>\n<\/ol>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.whistleblower.org\/guide-journalists\/\"><strong>The Whistleblower Project\/ Shirin Masu Fallasa<\/strong><\/a>\u00a0na al\u2019ummar kwararrun \u2018yan jarida a Amurka na da rubuce-rubuce sosai kan wannan batu, har ma da tattaunawar da aka yi kan bukatar a tabbatar da tsaro a duk sadarwar da ta shafi irin wadannan bayanan.<\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/journalistsresource.org\/tip-sheets\/reporting\/whistleblowers-tips-journalists\/\"><strong>Covering Whistleblowers: 6 Tips for Journalists\/ Yin labarai kan masu fallasa: shawarwari 6 wa \u2018yan jarida<\/strong><\/a>\u00a0\u2013 Wannan kasidar da Denise-marie Ordway ta rubuta a 2019 na daga cikin jerin abubuwan da ke tallafawa \u2018yan jarida. Shawarwari shiddan da ke kasidar su ne:<\/p>\n<ol>\n<li style=\"list-style-type: none\">\n<ol>\n<li>Kafin ku bayyana sunan wanda ya yi fallasa, ku duba ku gani ko bayanan da ya bayar ya fi irin hadarin da shi da ma wasu za su fuskanta a sakamakon labarin mahimmanci.<\/li>\n<li>Kada ku mayar da hankali a dalilin da ya sa mai fallasar ya bayar da bayanan<\/li>\n<li>Ku fahimci banbancin da ke tsakanin masu fallasa da wadanda suka fitar da bayanai da gangar.<\/li>\n<li>Ku tabbatar kun sami kyakyawar dabara ta sadarwa<\/li>\n<li>Ku nemi karin illimi kan dokokin da suka danganci kare masu fallasa musamman yadda suka shafi wanda ya kawo muku bayanan.<\/li>\n<li>Ku tabbata kun san irin wuraren da za ku sami taimako wajen fahimtar batutuwan da suka shafi masu fallasa.<\/li>\n<\/ol>\n<\/li>\n<\/ol>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.journalism.co.uk\/news\/the-art-of-working-with-whistleblowers\/s2\/a737581\/\"><strong>The Art of Working with Whistleblowers\/ Salon aiki da masu fallasa<\/strong><\/a><br \/>\nA wannan labarin, jaridar journalism.co.uk ta bayyana darussan Meirion Jones, edita a ofishin aikin bincike na jarida (BIJ) da ke Burtaniya. \u201cdaya daga cikin matakan da ya fi mahimmanci, a cewar Jones she ne kare suna da lafiyar wanda ya kawo labarin. Idan har akwai hadarin cewa hakan ba zai yiwu ba, gara kada a yi amfani da labarin baki daya ko kuma a wallafa kadan daga cikin abubuwan da ba za su tayar da hankali sosai ba,\u201d a cewar labarin.<\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.whistleblowers.org\/what-journalists-need-to-know-about-whistleblowers\/\"><strong>What Journalists Need to Know About Whistleblowers\/ Abin da ya kamata \u2018yan jarida su sani a kan masu fallasa<\/strong><\/a>\u00a0\u2013 littafi ne <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/www.whistleblowers.org\/index.php\">da cibiyar masu fallasa na kasa a Amurka (US National Whistleblowers Center)<\/a> ta wallafa. Batutuwa biyar aka tattauna: Ku sa dokokin, ku sakaya sunan wanda ya kawo labarin, ku san irin hadarin da ke tattare mai fallasar, \u201cwadanda ke fallasa batutuwan da suka shafi leken asiri suna da nasu dokokin,\u201d da kuma banbancin masu bayar da bayanai da gangar da masu fallasa ko tona asiri.<\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/whistleblowingnetwork.org\/WIN\/media\/pdfs\/Journalism-Sources-EUR-IALS-2017-Protecting-Sources-and-Whistleblowers-in-a-Digital-Age.pdf\"><strong>Protecting Sources and Whistleblowers in the Digital Age\/ Kare majiyoyi da masu fallasa a zamanin kafofin yada labarai na dijital<\/strong><\/a><br \/>\nDokar bayanai da cibiyar manufofin da ke kwalejin karatun shari\u2019a a jami\u2019ar Landan sun fitar da rahoto kan wata tattaunawar da aka yi da wata kungiyar kwararru na mutane 25 masu bincike a aikin jarida, da wakilai daga kungiyoyi masu zaman kansu, da lauyoyin kafafen yada labarai da masu bincike na musamman a watan Satumban 2016. Rahoton ya bayar da shawarar cewa \u2018yan jarida da kafaofin yada labarai su yi abubuwa kamar haka:<\/p>\n<ul>\n<li style=\"list-style-type: none\">\n<ul>\n<li>Karfafa manufofi kan fasaha mai karko, kulawa ma majiyoyi da kariya.<\/li>\n<li>Bita kan irin ma\u2019amalar da suke yi da majiyoyin da su ka bukaci a sakaya sunayensu<\/li>\n<li>Horaswa kan yadda ya kamata a kare majiya<\/li>\n<\/ul>\n<\/li>\n<\/ul>\n<p><strong>UNESCO\u2019S <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/unesdoc.unesco.org\/ark:\/48223\/pf0000248054\">Protecting Journalism Sources in the Digital Age\/ Kare majiyoyin \u2018yan jarida a zamanin dijital na UNESCO<\/a><\/strong>\u00a0littafi ne da ya kunshi shawarwar da bayanai kan hanyoyin kare majiyoyi a kasashe 120.<\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.ibanet.org\/Default.aspx\"><strong>International Bar Association\/ Kungiyar kwararrun lauyoyi na kasa da kasa IBA<\/strong><\/a><br \/>\nA shekarar 2018 IBA ta wallafa \u201cWhistleblower protections: A Guide,\u201d wanda ya duba dokoki har ma da shafin da ya kunshi bayanai da dokokin kasa. Ku je shafin IBA ku nemi labarin kuna amfani da Kalmar \u201cwhistleblowers\u201d<\/p>\n<h4><strong>Kungiyoyin kasa da kasa (International Organisations)<\/strong><\/h4>\n<p><strong><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignright wp-image-3823 size-medium\" src=\"https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2014\/09\/win1-336x143.png\" alt=\"\" width=\"336\" height=\"143\" srcset=\"https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2014\/09\/win1-336x143.png 336w, https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2014\/09\/win1.png 418w\" sizes=\"auto, (max-width: 336px) 100vw, 336px\" \/><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/whistleblowingnetwork.org\/\">Hadakar kungiyoyin kasa da kasa na masu fallasa WIN (Whistleblowing International Network)<\/a><\/strong>\u00a0Wannan hadin gwiwar kungiyoyi masu zaman kansu da na fararen hulan da ke aiki a fannin tabbatar da kariya wa masu fallasa. Kungiyar da ke da shlkwatarta a Scotland na bai wa mambobi damar musayar illiminsu da kwarewa a fannin shari\u2019a da aiki masu fallasa, ta yadda za su lalubo martanoni na dimokiradiyya ga batun fallasar a matakin cikin gida da na kasa da kasa, su kuma kara tallafawa wadanda ke aiki wajen kare masu fallasar a duniya baki daya. WIN na bayar da shawarwari, kayayyakin aiki, da kwarewarta ga kungiyoyin fararen hular da ke karewa da ma tallafawa masu fallasa a duniya. <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/euwhistleblowingmeter.polimeter.org\/\">Mitar auna fallasa ta Tarayyar Turai (The EU Whistleblowing Meter)<\/a> na bin diddigin yunkurin kasashen Tarayyar Turai wajen aiwatar da umurnin da tarayyar ta bayar a shekarar 2019 dan ganin ya zama doka.<\/p>\n<p><strong><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignleft wp-image-358807 size-thumbnail\" src=\"https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2021\/07\/NWC-140x72.jpeg\" alt=\"\" width=\"140\" height=\"72\" \/><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/www.whistleblowers.org\/index.php\">Cibiyar masu fallasa ta kasa (National Whistleblower Center)<\/a><\/strong>\u00a0kungiya ce mai zaman kanta wadda shelkwatarta ke Washington, D.C. Kungiyar na dauakar nauyin shawarwari, illimi da shirye-shirye, a ciki har da kundin bayanai na database da ya bayyana dokoki da wuraren samaun tallafi wa masu fallasa a kowace kasa. NWC tana kuma da wata karamar shiri ta kasa da kasa da ke aiki da \u2018ya jarida, masu rajin kare \u2018yancin fadan albarkacin baki, lauyoyi da jami\u2019an gwamnati. Akwai kuma littafi mai suna <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.whistleblowers.org\/resources\/the-whistleblowers-handbook\">The New Whistleblower\u2019s Handbook<\/a> da aka wallafa a shekarar 2019. NWC tana kuma da taskar blog inda ta kan rubuta sharhuna.<\/p>\n<p><strong><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignright wp-image-358808 size-thumbnail\" src=\"https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2021\/07\/GAP-140x49.png\" alt=\"\" width=\"140\" height=\"49\" \/><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/www.transparency.org\/\">Shirin Sanya Ido kan Gwamnati (The Government Accountability Project)<\/a><\/strong><br \/>\nMai mazaunin shi a Washington D.C. ya ce manufar shi ya kunshi \u201cinganta matakan sanya ido kan manyan kamfanoni da gwamnatoci ta hanyar kare masu fallasa, da wanzuwar \u2018yancin fadan albarkacin baki a wuraren aiki da kuma bai wa \u2018yan kasa masu fafutuka karfin gwiwa.\u201d Ya wallafa litattafai na shawara da yadda masu fallasa za su tsira. Tun 1977, GAP ya taimaka ma mutane fiye da 8,000 a fannonin gwamnati da \u2018yan kasuwa. Daga nan ne ya wallafa wani littafi mai suna <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.whistleblower.org\/caught-conscience-career-clean\/\">Caught Between Conscience &amp; Career: Expose Abuse Without Exposing Identity<\/a>, wato Tsakanin Imani da Aikin yi: fallasa batanci ba tare da bayyana kai ba, wanda ake gani shawarwarin kare kai ne wa duk masu fallasa.<\/p>\n<p><strong><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignleft size-thumbnail wp-image-358809\" src=\"https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2021\/07\/ti-logo-140x140-1-140x140.jpeg\" alt=\"\" width=\"140\" height=\"140\" srcset=\"https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2021\/07\/ti-logo-140x140-1.jpeg 140w, https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2021\/07\/ti-logo-140x140-1-60x60.jpeg 60w\" sizes=\"auto, (max-width: 140px) 100vw, 140px\" \/><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/www.transparency.org\/\">Transparency International<\/a><\/strong>\u00a0na aiki da gwamnati, \u2018yan kasuwa da kungiyoyin fararen hula wajen dakatar da cin hanci da rashawa dan inganta matakan yin ayyuka a bayyane, da sa ido, kuma cikin mutunci. TI na da rassa fiye da 100 a kasashen duniya kuma babban ofishinta na kasa da kasa na birnin Berlin. Akwai ofisoshi uku da ke da kwarewa a fallasa: <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/accion-ciudadana.org\/\">Accion Ciudadana<\/a> a Guatemala, <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/transparency.ie\/\">Transparency International Ireland<\/a> da <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/transparency.org.ru\/\">Tranparency International Russia<\/a>.<\/p>\n<p><strong><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"wp-image-358810 size-medium alignright\" src=\"https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2021\/07\/digital-whistleblowing-fund-336x151.png\" alt=\"\" width=\"336\" height=\"151\" srcset=\"https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2021\/07\/digital-whistleblowing-fund-336x151.png 336w, https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2021\/07\/digital-whistleblowing-fund.png 629w\" sizes=\"auto, (max-width: 336px) 100vw, 336px\" \/><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.whistleblowingfund.org\/\">Digital Whistleblowing Fund<\/a><\/strong>\u00a0wani karamin shiri ne na tallafi da ke karkashin jagorancin Cibiyar Hermes da Gidauniyar Renewable Freedom \u201cwanda ke taimakawa kungiyoyin masu bincike a aikin jarida, da kare hakkin dan adam da kungiyoyin talakawa wajen samun tallafin kudi da aiki, da dabarun tabbatar ingancin tsaro a shirin fallasar da suke da shi a yanar gizo ko kuma dijital. Wannan ya kasance daya daga cikin burukansu na zamantakewa.\u201d Shirin bincike a aikin jarida na Italiya (IRPI) na daya daga cikin wadanda suka sami irin wannan tallafi, kuma sun yi amfani da shi wajen gina ingantaccen shafin da masu fallasa za su iya tura bayanai.<\/p>\n<p><strong><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignleft wp-image-3936 size-full\" src=\"https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2014\/09\/IACC.png\" alt=\"\" width=\"195\" height=\"129\" \/><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/iaccseries.org\/\">Babban taron yaki da cin hanci da rashawa na kasa da kasa. (The International Anti-Corruption Conference)<\/a><\/strong>\u00a0dandali ne na kasashen duniya, da ke tattara wakilan gwamnatoci, kungiyoyin fararen hula, da \u2018yan kasuwa masu zaman kansu domin su tattauna kalubalen cin hanci da rashawa. Babban taron ya fi mayar da hankali ne kan masu fallasa da batutuwan da suka danganci hakan. Yana karkashin jagorancin kungiyar IACC wadda ke Transparency Internationl. Ana gudanar da babban taron bayan kowane shekaru biyu.<\/p>\n<h4><strong>Kayyakin Aiki (Tools)<\/strong><\/h4>\n<p><strong><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignright size-thumbnail wp-image-358816\" src=\"https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2021\/07\/securedrop_logo-336x311-1-140x140.png\" alt=\"\" width=\"140\" height=\"140\" srcset=\"https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2021\/07\/securedrop_logo-336x311-1-140x140.png 140w, https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2021\/07\/securedrop_logo-336x311-1-60x60.png 60w\" sizes=\"auto, (max-width: 140px) 100vw, 140px\" \/><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/securedrop.org\/\">Secure Drop<\/a><\/strong>\u00a0wannan wani tsari ne da ya tanadi duk masu fallasa su tura bayanan su, wanda ke karkashin jagorancin gidauniyar \u2018yancin kafofin yada labarai a Amurka, kuma duk kafofin yada labarai na iya amfani da bayanan ba tare da an bayyana wanda ya tur aba. Gidauniyar na da ofishinta a San Francisco ne kuma tana taimakwa wajen horas da duk mutanen da ke amfani da Secure Drop.<\/p>\n<p><strong><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"size-thumbnail wp-image-3828 alignright\" src=\"https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2014\/09\/global-leaks-140x140.png\" alt=\"\" width=\"140\" height=\"140\" srcset=\"https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2014\/09\/global-leaks-140x140.png 140w, https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2014\/09\/global-leaks-60x60.png 60w\" sizes=\"auto, (max-width: 140px) 100vw, 140px\" \/><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/globaleaks.org\/\">GlobalLeaks<\/a><\/strong>\u00a0na tanadar da software, ko kuma fasahar da ake amfani da shi wajen aiki da komfuta. Wannan na taimakawa wajen tabbatar da tsaro a kan shafukan ta yadda ba kowa ne zai iya gani ba amma masu fallasa, \u2018yan jarida da ma wasu majiyoyi na iya gani har ma su yi ma\u2019amala da juna. Wannan tsarin na iya taimakawa kafofin yada labarai, kungiyoyin masu rajin kare hakkin dana dam, hukumomin gwamnati da manyan kamfanoni. Yana karkashin jagorancin Cibiyar tabbatar da gaskiya da kare hakkin bil adama na Hermes da ke Milan. GlobaLeaks na bayar da kayayykin aikin na software domin tallafawa ayyukan fallasa.<\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/wereschagin.com\/encryption\"><strong>Kayan aiki na masu fallasa (Tools for Whistleblowers)<\/strong><\/a><br \/>\nMichael Wereschagin dan jarida mai zaman kan shi wanda ke bincike kuma mawallafi daga birnin Pittsburgh a jihar Pennsylvania ne ya hada wannan. Wereschagin ya jera sunayen irin tsare-tsaren da kafofin yada labarai da \u2018yan jarida masu zaman kansu ke amfani da su.<\/p>\n<h4><strong>Kungiyoyi a jere ta sunayen kasashe (Organisations by Country)<\/strong><\/h4>\n<p><em>Kungiyoyin da ke kasa sun kunshi kungiyoyi masu zaman kansu wadanda ke tallafawa masu fallasa suna kuma samar musu da damammakin yin hakan. Gaba daya, ba mu sanya ma\u2019akatan shari\u2019an da ke ayyukan fallasa ba ko manyan kamfanonin da ke bayar da software, ko da shi ke wasu daga cikin shafukansu na yanar gizo na da bayanai masu mahimmanci. Muna maraba da shawarwari, ku tuntube mu a adireshinmu na\u00a0<a href=\"mailto:hello@gijn.org\">hello@gijn.org<\/a><\/em><\/p>\n<h4><strong>Africa<\/strong><\/h4>\n<p><strong>Baki daya (General)<\/strong><\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.afrileaks.org\/\"><strong>AfriLeaks<\/strong><\/a>\u00a0na karkashin jagorancin hadakar kafafen yada labaran Afirkan da ke amfani da wata amintacciyar hanyarsamun bayanai na dropbox. Mutane na iya tura sakonni sa\u2019annan su zabi mambar kungiyar da suke so ta gudanat da binciken. Wannan shirin hadin gwiwa ne tsakanin Kawancen Cibiyoyin Bincike na aikin Jarida a Afirka da Cibiyar Tabbatar da Gaskiya da Kare Hakkin Dan Adam a Yanar Gizo na Hermes.<\/p>\n<p><strong><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.pplaaf.org\/\">Dandalin kare masu fallasa a Afirka (Platform to Protect Whistleblowers in Africa)<\/a><\/strong> \u2013 wanda ke birnin Paris kungiya ce mai bayar da shawarwari da taimako a fannin shari\u2019a, wadda a shekarar 2020 ta baiwa wata hadakar kungiyoyin kasa da kasa na \u2018yan jarida masu bincike bayanan da suka kasance tushen binciken da aka kaddamar kan Isabel dos Santos, biloniyar nan wadda mahaifinta shi ne tsohon shugaban kasar Angola.<\/p>\n<p><strong>Afirka ta Kudu (South Africa)<\/strong><\/p>\n<p><strong><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.opendemocracy.net\/en\/\">Cibiyar shawarwari ta dimokiradiyya mai gaskiya (Open Democracy Advice Center)<\/a><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.opendemocracy.net\/en\/\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignright wp-image-358819 size-full\" src=\"https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2021\/07\/ODAClogo2014-336x164-1.jpeg\" alt=\"\" width=\"336\" height=\"164\" \/><\/a><\/strong> burinta ita ce inganta dimokiradiyya mai gaskiya, da renon al\u2019adar sanya ido kan manyan kamfanoni da gwamnatoci, ta kuma illimantar da \u2018yan kasa kan hakkin dan adam. Cibiyar na inganta nuna gaskiya, da damar samun bayanai kuma yana tallafawa masu fallasa.<\/p>\n<h4><strong>Turai (Europe\/Eurasia)<\/strong><\/h4>\n<p><strong>Baki daya (General)<\/strong><\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.whistleblower-rights.org\/\"><strong>Cibiyar kare hakkin masu fallasa na tarayyar Turai mai<\/strong><\/a>\u00a0ofishi a Berlin, ta na taimakawa masu fallasa kuma ita ma tana taimakawa da manufofi da shari\u2019a. A bazarar 2019 ta wallafa kasidarta na farko wanda ke fitowa kwane wata uku.<\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/see-whistleblowing.org\/\"><strong>Hadin gwiwar kasashen yankin kudu maso gabashin Turai<\/strong><\/a>\u00a0dan kare masu fallasa (The Southeast Europe Coalition on Whistleblower Protection) Hadaka ce ta kungiyoyi daga kasashe 12<\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/fishyleaks.eu\/en\/\"><strong>FishyLeaks<\/strong><\/a>\u00a0\u2013 shi ma shafi ne na samun bayanai da wata kungiya mai suna <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/our.fish\/\">Our Fish<\/a> ta kirkiro yayin da ta ke gangamin na wayar da kan jama\u2019a dangane da yawan kamun kifin da ake yi a teku, wanda kasancewa barazana ga muhalli. FishyLeaks na samun tallafi daga <a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/fundingfish.eu\/\">Funding Fish<\/a> ko gidauniyar kifaye da burin samun jama\u2019an da za su rika kawo musu rahotannin haramtattun abubuwan da suka gani a ruwayen Turai.<\/p>\n<p><strong>Albaniya<\/strong><\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/csdgalbania.org\/governance-program-2\/\"><strong>Cibiyar Nazarin Dimokiradiyya da Mulki (The center for the Study of Democracy and Governance)<\/strong><\/a>\u00a0Ya wallafa littafin shawarwari wa masu fallasa wadanda ke fallasa a Albaniya<\/p>\n<p><strong>Austria<\/strong><\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/whistleblowing.at\/\"><strong>Fallasa a kasar Austriya (Whistleblowing in Austria)<\/strong><\/a>\u00a0an kirkiro ta ne a 2011 a matsayin kungiyar da za ta taimaka wa \u2018yan kasa su dauki matakin bayyana zalunci da rashin gaskiya.<\/p>\n<p><strong>Faransa (France)<\/strong><\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/transparency-france.org\/#\/\"><strong>Transparency International Faransa<\/strong><\/a>\u00a0na da shafin da ke taimakwa masu fallasa wajen tsegunta batutuwan da suka shafi cin hanci da rashawa<\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/mlalerte.org\/\"><strong>La Maison des Lanceurs d\u2019Alerte<\/strong><\/a>\u00a0kungiya ce ta Faransa wadda ke bayar da taimako a fannin shari\u2019a, lafiyar kwakwalwa da kafofin yada labarai da ma tallafin kudi wa masu fallasar da ke bukata. Ta na kuma bayar da irin abubuwan da ake bukata a yanar gizo kamar su lambobin tuntuba, shawarwari da bayanai dangane da shari\u2019a.<\/p>\n<p><strong>Jamus (Germany)<\/strong><\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/www.whistleblower-net.de\/\"><strong>Hadakar Kungiyoyin masu fallasa (Whistleblower Network)<\/strong><\/a>\u00a0Mambobin kungiyar \u2018yan sa-kai ne, \u2018yan jarida da masu fallasar suka kirkiro kungiyar a shekarar 2006. Kungiyar na bayar da shawarwari sa\u2019annan yana aiki da masu fallasa, masu bincike da \u2018yan jarida a lokacin da ya dace. Shafin dandali ne na bayanai dangane da masu fallasa. A kowace rana akwai labarai na taskar blog da ke dauke da halin da ake ciki ko inda aka kwana a batun na fallasa.<\/p>\n<p><strong>Hungary<\/strong><\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/k-monitor.hu\/fooldal\"><strong>K Monitor mai sanya ido kan kudaden al\u2019umma\u00a0(K Monitor Watchdog for Public Funds)<\/strong><\/a>\u00a0an kafa shi a shekarar 2007 a matsayin wata hanya na sanya batutuwan da suka shafi matsalar cin hanci da rashawa a kasar Hungary da ma kasa da kasa a cikin labarai. Kungiyar na kokarin wanzar da ra\u2019ayin samar da bayanan da al\u2019umma ke bukata ta yin amfani da bincike mai zurfi a aikin jarida, kuma shafin yana da database inda \u2018yan jarida da ma masu fallasa za su iya samun bayanan da suke bukata.<\/p>\n<p><strong>Ireland<\/strong><\/p>\n<div id=\"attachment_358820\" style=\"width: 346px\" class=\"wp-caption alignright\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" aria-describedby=\"caption-attachment-358820\" class=\"wp-image-358820 size-full\" src=\"https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2021\/07\/1571588031_b901164a77_z-336x246-1.jpeg\" alt=\"\" width=\"336\" height=\"246\" \/><p id=\"caption-attachment-358820\" class=\"wp-caption-text\">Creative Commons photo c \/ o Ollie Brown, Flickr<\/p><\/div>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/transparency.ie\/helpline\"><strong>Transparency International Ireland<\/strong><\/a><br \/>\nA shekarar 2004 aka kafa ta kuma tana aiki ne ta tabbatar cewa an bi ma kowa hakkin shi, ko da mutun ya kasasnce a bangaren gwamnati ko na \u2018yan kasuwa masu zaman kansu. Burinta shi ne a samar ma jama\u2019a hanyoyin dogaro-da-kai ta amfani da illimi, da bayanai da kuma bincike. Littafin ta mai suna Speak Up Safely Guide (sauke a nan) na da burin taimakawa ma\u2019aikata a Ireland su fahimci dokokin fallasa a kasar Ireland.<\/p>\n<p><strong>Italiya (Italy)<\/strong><\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/irpi.eu\/iniziative\/\"><strong>IrpiLeaks<\/strong><\/a> dandalin fallasar kungiyar IRPI, wato cibiyar bincike a aikin jarida na Italiya. Ta fi mayar da hankali kan bayanan kungiyoyin mafia a Burtaniya<\/p>\n<p><strong>Holland (The Netherlands)<\/strong><\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/huisvoorklokkenluiders.nl\/\"><strong>Gidan masu fallasa (House of Whistleblowers)<\/strong><\/a>\u00a0na bayar da shawarwari ta tallafi wajen lura da lafiyan kwakwalwa da yanayin zamantakewa, ta na kuma gudanar da bincike kan yadda ake kula da lafiyar masu fallasar da kuma cin zarafin da sukan fiskanta a al\u2019umma. Haka nan kuma, tana taimakwa wajen kare su daga yanayin da zai sa bata musu mutuncin su, sa\u2019annan tana bayar da bayanai dangane da masu fallasan.<\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.publeaks.nl\/press.html\"><strong>PubLeaks<\/strong><\/a> Shafi ne mai kwakwarar tsaro wanda ke samun goyon bayan kafofin yada labaran Holland fiye da 40. A shekarar 2013 aka kafa ta yin amfani da fasahar software na GlobaLeaks wanda cibiyar Hermes ta sarrafa.<\/p>\n<p><strong>Poland<\/strong><\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/www.batory.org.pl\/\"><strong>Gidauniyar Stefan Batory (Stefan Batory Foundation)<\/strong><\/a> gidauniya ce mai zaman kanta a Poland wadda aka samar a 1988 da burin samar da al\u2019umma mai gaskiya, mai samun bayanai kuma mai bin turbar dimokiradiyya.<\/p>\n<p><strong>Rasha (Russia)<\/strong><\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/transparency.org.ru\/\"><strong>Transparency International Russia<\/strong><\/a>, an kafa shi a 1999 kuma yana tattara kungiyoyin fararen hula har da kafofin yada labarai su yi yaki da cin hanci da rashawa su kuma yi aiki wajen halatta ka\u2019idojin gaskiya da ci-gaba a fannonin gwamnati da na \u2018Yan kasuwa masu zaman kansu.<\/p>\n<p><strong>Serbiya (Serbia)<\/strong><\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/pistaljka.rs\/\"><strong>Pistaljka<\/strong><\/a>\u00a0ko kuma \u201cusur\u201d da harshen serbiyanci, na gudanar da bincike, kuma yana da shafin da ke karbar bayanai daga masu fallasa sa\u2019annan su taimaka musu da batutuwan da suka shafi shari\u2019a.<\/p>\n<p><strong>Spain<\/strong><\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/xnet-x.net\/en\/quienes-somos\/\"><strong>XNET<\/strong><\/a>\u00a0ta na fafutukar ganin cewa masu fallasa sun sami kariya. Kuma ta na da wani tsarin da ke kula da masu fallasar da ta ajiye a boye ta yin amfani da fasaha mai sarkakiya na encryption.<\/p>\n<p><strong>Ukraine<\/strong><\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/initziativa11.org\/\"><strong>Initiative 11<\/strong><\/a>\u00a0gamayya ce ta kungiyoyin fararen hulan da ke fafutukar tabbarar da kariya wa masu fallasa a Ukraine.<\/p>\n<p><strong>Burtaniya (United Kingdom)<\/strong><\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/protect-advice.org.uk\/\"><strong>Kariya, (wadda a baya aka san ta da Aikin Damuwar Jama\u2019a) (Protect, formerly known as Public Concern at Work)<\/strong><\/a>\u00a0an fara kungiyar a 1993 kuma burin ta shi ne ta tabbatar aikin fallasa ya dore saboda a kauce wa hadurruka da ke barazana dagula al\u2019umma, kuma ko da ba\u2019a kai ga cimma wannan buri ba, akalla a dago miyagun abubuwan kafin su yi lahani. PCW na da layin kyauta inda take bayar da shawarwari, kuma tana tallafawa kungiyoyin da ke aiki irin na ta. Ta na gudanar da ayyukan da suka shafi manufofin ci-gaba da illimantar da al\u2019umma.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignleft size-medium wp-image-4104\" src=\"https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2014\/09\/Screen-Shot-2014-10-20-at-1.33.19-PM-336x71.png\" alt=\"\" width=\"336\" height=\"71\" srcset=\"https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2014\/09\/Screen-Shot-2014-10-20-at-1.33.19-PM-336x71.png 336w, https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2014\/09\/Screen-Shot-2014-10-20-at-1.33.19-PM-771x164.png 771w, https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2014\/09\/Screen-Shot-2014-10-20-at-1.33.19-PM-1170x249.png 1170w, https:\/\/gijn.org\/wp-content\/uploads\/2014\/09\/Screen-Shot-2014-10-20-at-1.33.19-PM.png 1370w\" sizes=\"auto, (max-width: 336px) 100vw, 336px\" \/><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/www.thewhistler.org\/\"><strong>The Whistler<\/strong><\/a>: Hadaka ce da ta kawo kungiyoyin Campassion and Care (Tausayi da kulawa) da (Cibiyar bincike a aikin jarida) Centre for Investigative Journalism the nufin kare duk wadanda suke aikin fallasa gaskiya ba tare da la\u2019akati da banbancin kabila, addini ko manufoi na siyasa ba. Masu aikin fallasan ne suka hada, domin kansu da sauran \u2018yan uwansu masu fallasan kuma suna taimaka musu da kwararru da shawarwari da kuma taimako a fanin shari\u2019a, da kudi.<\/p>\n<h4><strong>Kudancin Amirka da yankin Carribbean (Latin America\/Carribbean)<\/strong><\/h4>\n<p><strong>Guatemala<\/strong><\/p>\n<p><strong><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/accion-ciudadana.org\/\">Accion Ciudadana<\/a>:<\/strong>\u00a0A shekarar 1996 aka kafa ta kuma daga shekarar 2006 ta fara kasancewa daya daga cikin rassan kungiyar Tranparency International. Kungiyar fararen hula ne da ke aiki da kungiyoyin Transparency da Integrity a Guatemala.<\/p>\n<p><strong>Mexico<\/strong><\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/mexicoleaks.mx\/\"><strong>MexicoLeaks<\/strong><\/a>\u00a0dandali ne da ke samun goyon bayan kungiyoyin Mexico guda takwas wadanda suka hada da Animal Politico, emeequis, M\u00e1sde131, Periodistas de a Pie, Poder, Proceso, R3D, da Arestegui Noticias.<\/p>\n<p><strong>Yankin Arewacin Amirka (North America)<\/strong><\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/acacanada.ca\/\"><strong>Yaki da cin hanci da rashawa da sa ido, Canada (Anti-corruption and Accountability Canada)<\/strong><\/a>\u00a0na taimkawa masu yin aikin fallasa, kuma suna bayar da shawara kyauta<\/p>\n<p><strong>Amurka<\/strong><\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/www.whistleblower.org\/\"><strong>Governmant Accountability Project (GAP)<\/strong><\/a>\u00a0kungiya mai zaman kanta ne a Washington, da ke goyon bayan aikin da masu fallasa ke yi.<\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/www.pogo.org\/\"><strong>Project on Government Oversight (POGO)<\/strong><\/a>\u00a0kungiya ce mai zaman kanta wadda ke aiki da masu fallasa da \u2018yan jarida da jami\u2019an gwamnati domin su tabbatar da sauye-sauye masu kyau a gwamnati.<\/p>\n<p><strong><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/www.whistleblowers.org\/index.php\">National Whistleblower center<\/a>&#8211;<\/strong>\u00a0kungiya mai zaman kanta ne a Washington wadda ke tallafawa shirye-shiryen fadakarwa, illimi da shirye-shiryen da suka shafi fallasa.<\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/whistlebloweraid.org\/\"><strong>Whistleblower Aid<\/strong><\/a>\u00a0kungiya mai zaman kanta, wadda ke kula da harkokin shari\u2019a kuma tana da mazaunin ta a Washington, D.C. \u201cMuna goyon bayan duk wadanda suka bi doka suka kai karan gwamnati da manyan kamfanoni da zarar sun karya doka.\u201d<\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"http:\/\/whistleblowing.us\/\"><strong>The Whistlerblower Support Fund<\/strong><\/a>\u00a0kungiya mai zaman kanta da ke \u201cbayar da shawarwari da taimako a fanin aiki da kwararru, da lauyoyi. da ma\u2019akatan zamantakewa, da masu bayar da shawara kan aikin yi ko\/da \u2018yan jarida, sa\u2019annan ta na kuma taimaka ma wadanda ke aikin fallasa.<\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.kkc.com\/blog\/\"><strong>The Whistleblower Blog<\/strong><\/a>\u00a0\u201cKamfanin yada labarai ne mai zaman kan shi,\u201d wanda ke zaman gudunmawa na kyauta ga al\u2019umma daga kamfanin Kohn, Kohn &amp; Colapinto, LPP<\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.councilofnonprofits.org\/tools-resources\/whistleblower-protections-nonprofits\"><strong>The National Council of Nonprofits<\/strong><\/a>\u00a0\u2013 Ya jera abubuwan da suka dace a sani game da manufofin aikin fallasa da ma mahimmancinsu ga kungiyoyi masu zaman kance.<\/p>\n<p><strong>ASIYA (ASIA)<\/strong><\/p>\n<p><a rel=\"noopener\" target=\"_blank\" href=\"https:\/\/www.indonesialeaks.id\/\"><strong>IndonesiaLeaks<\/strong><\/a>\u00a0\u2013 Yana tanadar da wurin da masu bayar da bayanan za su iya su tsegunta ba tare da kowa ya sani ba. Daga nan sai \u2018yan jarida su bi sahun labarin<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Whistleblowers ko kuma masu fallasa bayanan sirri \u2013 ma\u2019aikata wadanda ke fallasa haramtattun ayyuka da karbar cin hanci da rashawa \u2013 suna da mahimmanci wajen samo irin bayanan da \u2018yan jarida ke bukata. Daga inda suke aiki cikin gwamnatoci, kamfanoni da sauran kungiyoyi za su iya bayar da hujjoji da irin alamun da ake bukata [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":3031153,"featured_media":843854,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_acf_changed":false,"_price":"","_stock":"","_tribe_ticket_header":"","_tribe_default_ticket_provider":"","_tribe_ticket_capacity":"0","_ticket_start_date":"","_ticket_end_date":"","_tribe_ticket_show_description":"","_tribe_ticket_show_not_going":false,"_tribe_ticket_use_global_stock":"","_tribe_ticket_global_stock_level":"","_global_stock_mode":"","_global_stock_cap":"","_tribe_rsvp_for_event":"","_tribe_ticket_going_count":"","_tribe_ticket_not_going_count":"","_tribe_tickets_list":"[]","_tribe_ticket_has_attendee_info_fields":false,"republication-tracker-tool-hide-widget":false,"footnotes":"","_tec_slr_enabled":"","_tec_slr_layout":""},"categories":[23110],"tags":[],"gijn_topic":[19124],"series":[],"gijn_language":[17798],"gijn_region":[],"class_list":["post-462790","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-albari","gijn_topic-lambobin-kira-hanyoyin-sadarwa","gijn_language-ha-ha"],"acf":[],"ticketed":false,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/462790","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/users\/3031153"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=462790"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/462790\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2369462,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/462790\/revisions\/2369462"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/media\/843854"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=462790"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=462790"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=462790"},{"taxonomy":"gijn_topic","embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/gijn_topic?post=462790"},{"taxonomy":"series","embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/series?post=462790"},{"taxonomy":"gijn_language","embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/gijn_language?post=462790"},{"taxonomy":"gijn_region","embeddable":true,"href":"https:\/\/gijn.org\/ha\/wp-json\/wp\/v2\/gijn_region?post=462790"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}