Accessibility Settings

color options

monochrome muted color dark

reading tools

isolation ruler

Albari

Albari

Topics

Working with Whistleblowers/ Aiki da masu fallasa bayanan sirri

Read this article in

Photo: Flickr

Whistleblowers ko kuma masu fallasa bayanan sirri – ma’aikata wadanda ke fallasa haramtattun ayyuka da karbar cin hanci da rashawa – suna da mahimmanci wajen samo irin bayanan da ‘yan jarida ke bukata. Daga inda suke aiki cikin gwamnatoci, kamfanoni da sauran kungiyoyi za su iya bayar da hujjoji da irin alamun da ake bukata domin fallasa abubuwa, kama daga zamba da almubazaranci har zuwa miyagun aiyuka, makirci da miyagun laifukan yaki.

Sai dai ya na da mahimmanci ‘yan jarida su tantance manufar masu fallasar domin su iya tantance bayanan da su ke bayarwa. Haka nan kuma yana da mahimmanci a san yadda za’a kare su a matsayin majiyoyin labarin.
An yi sa’a akwai bayanai da dama kan fallasa, har da karuwar da aka samu a yawan kungiyoyi masu zaman kansun da ke da kwarewa ta wannan fanin a kasashen duniya.

Domin taimakwa ‘yan jarida su bi diddigin irin wadannan labaran a yanayi mai kalubalen gaske, GIJN ta kirkiro kundin da ya jera irin wadannan wurare na samun taimako. Idan har akwai wanda kuke ganin ba mu sa ba, rubuto mana ta adireshinmu hello@gijn.org.

Fallasa shi ne idan na miji ko na mace wanda, saboda imanin da ya/ta yi da kare darajar al’umma, ya/ta yi watsi da bukatun kamfanin da ya/ta ke aiki dan ya/ta fito fil ta tona duk wani abun da kamfanin ya ke yi da ya shafi karbar cin hanci da rashawa, haramtacce, zamba, ko kuma yana iya raunata jama’a.
– Ralph Nader, Mai bayar da shawara da kuma fafutukar kare hakkin jama’a.

Guidance from Experts/Shawarwari daga kwararru

Idan har masu fallasa sun amince su bayar da bayanai, wajibi ne su sami kulawa ta musamman.

GIJN ta takaita wadansu mahimman sharudda na aiki da masu fallasa daga majiyoyi iri-iri. Rahoton na kunshe da cikakken bayani kuma ya dace a karanta.

The Perugia Principles for Journalists/ Ka’idoji ma ‘yan jarida na Perugia, wanda aka yi wa taken “Aiki da Masu Fallasa a zamanin Dijital.” A shekarar 2019 aka fara wallafawa, Julie Posetti, Dr. Suelette Dreyfus da Naomi Colvin suka rubuta. Marubutan sun kirkiro ka’dojin na Perugia lokacin wata tattaunawa ta musamman tare da tallafin wasu ‘yan jaria na kasa da kasa da kwararru 20. Kungiyar Blueprint for Free Speech, wadda ke fafutukar kare hakkin ‘yan jarida na fadan albarkacin baki da ke birnin Perugia a Italy ce ta dauki nauyin tattaunawar a watan Afrilun 2018. Bayan nan ne marubutan suka sake ganawa da kwararru a fannin bincike a aikin jarida, lauyoyi da masan illimi domin kwaskware ka’idoji 12 da suka gindaya.

  1. Da farko, a kare majiyoyi. Kada a bayyana sunayensu sadda aka tambaya.
  2. Sadda za ku sada a karon farko, idan zai yiwu, ku tabbatar cewa hanyoyin yin hakan nagartattu ne kuma za sub a su kariya.
  3. Ku yi la’akari da hadarin da mai fallasa zai iya fuskanta, dan haka ku sa su su yi tunanin gaba da yadda za su tafiyar da rayuwarsu bayan labarin ya fita.
  4. Ku tantance bayanin kuna bayar da fifiko kan darajar da bayanin ke da shi ga ci-gabar al’umma ba ra’ayinka ba ko kuma halayya ko ra’ayin mai fallasar ba.
  5. Ku dauki nauyin kare kan ku a duniyar yanar gizo ku yi amfani da lambobi masu sarkakiya wadanda ake kira “encryption” a turance. Duk da cewa ba lallai ne encryption ya kare majiyoyinku ba, ya na bayar da kariya a matakin farko.
  6. Ku tantance abubuwan da za su kasance barazana mafi hadari gare ku da majiyoyinku, da kuma irin matakan da ya kamata ku dauka dan kare juna.
  7. Ku bayyana wa majiyarku irin hadarin da ke tattare da bayyana abu a yanar gizo. Idan labarai masu sarkakiya ne ku koya wa majiyoyinku mahimman matakan kare kai a yanar gizo.
  8. Ku wallafa duka bayanan da kuka samu na ainihi idan da hali kuma babu wani hadari, yin hakan na da mahimmanci ga labarai.
  9. Ku yi amfani da amintattun hanyoyi wajen goge bayanan da amsu fallasar suka bayar, idan har an tambaya, domin ku sakaye sunayen mahiyoyin, abin da ya zo daidai da matakan da’a da doka da nauyin da ya rataya a kan mai aiki.
  10. Ku tabbata duk hanyoyin musayar bayanan da aka yi amfani da su a yanar gizo, irin su drop box suna da kariya mai inganci, sa’annan wa bayanan da ke dauke da sirri a tabbatar an sakaya sunayensu.
  11. Ku fahimci kadar, yankin da dokokin kasa da kasa na kare majiyoyin da suka bayar da bayani a boye ko kuma suka yi fallasa.
  12. Ku baiwa masu wallafa jaridu karfin gwiwar aiwatar da nauyin da ya rataya a wuyarsu na tabbatar da tsaro ga bayanan ‘yan jarida, majiyoyi da bayanan da aka boye tare da irin horaswar da ta dace da kuma manufofin da za su jagoranci ‘yan jaridar.

10 tips for Journalists working with Whistleblowers/ Shawarwar 10 ma ‘yan jaridan da ke aiki da masu fallasa. Wannan labarin da Rowan Philp ya rubuta a 2019 ya takaita mahimman sakonnin masu gabatarwa a babban taron GIJC, wanda aka yi a 2019 a birnin Hamburg na kasar Jamus.

Working with Whistleblowers: A Guide for Journalists/ Aiki da masu fallasa: Shwarwari ga ‘yan jarida – Kungiyoyin Amurka biyu ne suka buga wannan littafin: Shirin sanya ido a kan gwamnati (GAP) daya daga cikin manyan kungiyoyin fallasa masu zaman kansu, da Al’ummar ‘Yan jarida Kwararru (society of Professional Journalists). A 2017 aka wallafa. “muna fatan taimakawa ‘yan jarida su kare masu fallasa a maimakon kyale su, su fuskanci ramuwar gayya,” a cewar gabatarwar takardar mai shafuka 36. Ya kuma kara da wadannan shawarwarin:

   • Domin hadarin afkuwar ramuwar gayya a kan masu fallasar yana da yawa kuma dokokin na da sarkakiya, ‘yan jarida da majiyoyi za su sami tallafi sosai idan suka hada gwiwa da GAP da sauran lauyoyin da suka lakanci dokokin fallasa kafin su yi amfani da bayanan da suka samu daga majiyoyi.
   • Ka da ‘yan jarida su sanya kan su a cikin labari; Kai ba mai bayar da shawara ne ko dabaru, kuma kai ba lauya ba ne. Amma ta sa yardar ka da nuna fahimtar cewa akwai matakai na musamman wajen tinkarar labaran da ke da alaka da majiyoyi na fallasa, ka na iya taimakwa a sami rahotanni masu bayanan da ke da darajan gaske ga al’umma, yayin da ake daukan matakan da za su kare majiyarka.
   • Idan wani ma’aikaci ya tinkare ka da bayanai dangane da kura-kurai masu tsananin gaske, ko da batun ya danganci tauya hakkin dana dam, barazana ga muhakki ko kuma hadari ga tsaron kasa, ‘yan jarida su yi hankali wajen tattaunawa da ma’aikacin domin su tabbatar da cewa mutumin ya yi la’akari da duk zabubbukan da yake da shi dangane da hanyar da ta fi dacewa ya kai bayanan da ya ke so ya bayar.

The Whistleblower Project/ Shirin Masu Fallasa na al’ummar kwararrun ‘yan jarida a Amurka na da rubuce-rubuce sosai kan wannan batu, har ma da tattaunawar da aka yi kan bukatar a tabbatar da tsaro a duk sadarwar da ta shafi irin wadannan bayanan.

Covering Whistleblowers: 6 Tips for Journalists/ Yin labarai kan masu fallasa: shawarwari 6 wa ‘yan jarida – Wannan kasidar da Denise-marie Ordway ta rubuta a 2019 na daga cikin jerin abubuwan da ke tallafawa ‘yan jarida. Shawarwari shiddan da ke kasidar su ne:

  1. Kafin ku bayyana sunan wanda ya yi fallasa, ku duba ku gani ko bayanan da ya bayar ya fi irin hadarin da shi da ma wasu za su fuskanta a sakamakon labarin mahimmanci.
  2. Kada ku mayar da hankali a dalilin da ya sa mai fallasar ya bayar da bayanan
  3. Ku fahimci banbancin da ke tsakanin masu fallasa da wadanda suka fitar da bayanai da gangar.
  4. Ku tabbatar kun sami kyakyawar dabara ta sadarwa
  5. Ku nemi karin illimi kan dokokin da suka danganci kare masu fallasa musamman yadda suka shafi wanda ya kawo muku bayanan.
  6. Ku tabbata kun san irin wuraren da za ku sami taimako wajen fahimtar batutuwan da suka shafi masu fallasa.

The Art of Working with Whistleblowers/ Salon aiki da masu fallasa
A wannan labarin, jaridar journalism.co.uk ta bayyana darussan Meirion Jones, edita a ofishin aikin bincike na jarida (BIJ) da ke Burtaniya. “daya daga cikin matakan da ya fi mahimmanci, a cewar Jones she ne kare suna da lafiyar wanda ya kawo labarin. Idan har akwai hadarin cewa hakan ba zai yiwu ba, gara kada a yi amfani da labarin baki daya ko kuma a wallafa kadan daga cikin abubuwan da ba za su tayar da hankali sosai ba,” a cewar labarin.

What Journalists Need to Know About Whistleblowers/ Abin da ya kamata ‘yan jarida su sani a kan masu fallasa – littafi ne da cibiyar masu fallasa na kasa a Amurka (US National Whistleblowers Center) ta wallafa. Batutuwa biyar aka tattauna: Ku sa dokokin, ku sakaya sunan wanda ya kawo labarin, ku san irin hadarin da ke tattare mai fallasar, “wadanda ke fallasa batutuwan da suka shafi leken asiri suna da nasu dokokin,” da kuma banbancin masu bayar da bayanai da gangar da masu fallasa ko tona asiri.

Protecting Sources and Whistleblowers in the Digital Age/ Kare majiyoyi da masu fallasa a zamanin kafofin yada labarai na dijital
Dokar bayanai da cibiyar manufofin da ke kwalejin karatun shari’a a jami’ar Landan sun fitar da rahoto kan wata tattaunawar da aka yi da wata kungiyar kwararru na mutane 25 masu bincike a aikin jarida, da wakilai daga kungiyoyi masu zaman kansu, da lauyoyin kafafen yada labarai da masu bincike na musamman a watan Satumban 2016. Rahoton ya bayar da shawarar cewa ‘yan jarida da kafaofin yada labarai su yi abubuwa kamar haka:

  • Karfafa manufofi kan fasaha mai karko, kulawa ma majiyoyi da kariya.
  • Bita kan irin ma’amalar da suke yi da majiyoyin da su ka bukaci a sakaya sunayensu
  • Horaswa kan yadda ya kamata a kare majiya

UNESCO’S Protecting Journalism Sources in the Digital Age/ Kare majiyoyin ‘yan jarida a zamanin dijital na UNESCO littafi ne da ya kunshi shawarwar da bayanai kan hanyoyin kare majiyoyi a kasashe 120.

International Bar Association/ Kungiyar kwararrun lauyoyi na kasa da kasa IBA
A shekarar 2018 IBA ta wallafa “Whistleblower protections: A Guide,” wanda ya duba dokoki har ma da shafin da ya kunshi bayanai da dokokin kasa. Ku je shafin IBA ku nemi labarin kuna amfani da Kalmar “whistleblowers”

Kungiyoyin kasa da kasa (International Organisations)

Hadakar kungiyoyin kasa da kasa na masu fallasa WIN (Whistleblowing International Network) Wannan hadin gwiwar kungiyoyi masu zaman kansu da na fararen hulan da ke aiki a fannin tabbatar da kariya wa masu fallasa. Kungiyar da ke da shlkwatarta a Scotland na bai wa mambobi damar musayar illiminsu da kwarewa a fannin shari’a da aiki masu fallasa, ta yadda za su lalubo martanoni na dimokiradiyya ga batun fallasar a matakin cikin gida da na kasa da kasa, su kuma kara tallafawa wadanda ke aiki wajen kare masu fallasar a duniya baki daya. WIN na bayar da shawarwari, kayayyakin aiki, da kwarewarta ga kungiyoyin fararen hular da ke karewa da ma tallafawa masu fallasa a duniya. Mitar auna fallasa ta Tarayyar Turai (The EU Whistleblowing Meter) na bin diddigin yunkurin kasashen Tarayyar Turai wajen aiwatar da umurnin da tarayyar ta bayar a shekarar 2019 dan ganin ya zama doka.

Cibiyar masu fallasa ta kasa (National Whistleblower Center) kungiya ce mai zaman kanta wadda shelkwatarta ke Washington, D.C. Kungiyar na dauakar nauyin shawarwari, illimi da shirye-shirye, a ciki har da kundin bayanai na database da ya bayyana dokoki da wuraren samaun tallafi wa masu fallasa a kowace kasa. NWC tana kuma da wata karamar shiri ta kasa da kasa da ke aiki da ‘ya jarida, masu rajin kare ‘yancin fadan albarkacin baki, lauyoyi da jami’an gwamnati. Akwai kuma littafi mai suna The New Whistleblower’s Handbook da aka wallafa a shekarar 2019. NWC tana kuma da taskar blog inda ta kan rubuta sharhuna.

Shirin Sanya Ido kan Gwamnati (The Government Accountability Project)
Mai mazaunin shi a Washington D.C. ya ce manufar shi ya kunshi “inganta matakan sanya ido kan manyan kamfanoni da gwamnatoci ta hanyar kare masu fallasa, da wanzuwar ‘yancin fadan albarkacin baki a wuraren aiki da kuma bai wa ‘yan kasa masu fafutuka karfin gwiwa.” Ya wallafa litattafai na shawara da yadda masu fallasa za su tsira. Tun 1977, GAP ya taimaka ma mutane fiye da 8,000 a fannonin gwamnati da ‘yan kasuwa. Daga nan ne ya wallafa wani littafi mai suna Caught Between Conscience & Career: Expose Abuse Without Exposing Identity, wato Tsakanin Imani da Aikin yi: fallasa batanci ba tare da bayyana kai ba, wanda ake gani shawarwarin kare kai ne wa duk masu fallasa.

Transparency International na aiki da gwamnati, ‘yan kasuwa da kungiyoyin fararen hula wajen dakatar da cin hanci da rashawa dan inganta matakan yin ayyuka a bayyane, da sa ido, kuma cikin mutunci. TI na da rassa fiye da 100 a kasashen duniya kuma babban ofishinta na kasa da kasa na birnin Berlin. Akwai ofisoshi uku da ke da kwarewa a fallasa: Accion Ciudadana a Guatemala, Transparency International Ireland da Tranparency International Russia.

Digital Whistleblowing Fund wani karamin shiri ne na tallafi da ke karkashin jagorancin Cibiyar Hermes da Gidauniyar Renewable Freedom “wanda ke taimakawa kungiyoyin masu bincike a aikin jarida, da kare hakkin dan adam da kungiyoyin talakawa wajen samun tallafin kudi da aiki, da dabarun tabbatar ingancin tsaro a shirin fallasar da suke da shi a yanar gizo ko kuma dijital. Wannan ya kasance daya daga cikin burukansu na zamantakewa.” Shirin bincike a aikin jarida na Italiya (IRPI) na daya daga cikin wadanda suka sami irin wannan tallafi, kuma sun yi amfani da shi wajen gina ingantaccen shafin da masu fallasa za su iya tura bayanai.

Babban taron yaki da cin hanci da rashawa na kasa da kasa. (The International Anti-Corruption Conference) dandali ne na kasashen duniya, da ke tattara wakilan gwamnatoci, kungiyoyin fararen hula, da ‘yan kasuwa masu zaman kansu domin su tattauna kalubalen cin hanci da rashawa. Babban taron ya fi mayar da hankali ne kan masu fallasa da batutuwan da suka danganci hakan. Yana karkashin jagorancin kungiyar IACC wadda ke Transparency Internationl. Ana gudanar da babban taron bayan kowane shekaru biyu.

Kayyakin Aiki (Tools)

Secure Drop wannan wani tsari ne da ya tanadi duk masu fallasa su tura bayanan su, wanda ke karkashin jagorancin gidauniyar ‘yancin kafofin yada labarai a Amurka, kuma duk kafofin yada labarai na iya amfani da bayanan ba tare da an bayyana wanda ya tur aba. Gidauniyar na da ofishinta a San Francisco ne kuma tana taimakwa wajen horas da duk mutanen da ke amfani da Secure Drop.

GlobalLeaks na tanadar da software, ko kuma fasahar da ake amfani da shi wajen aiki da komfuta. Wannan na taimakawa wajen tabbatar da tsaro a kan shafukan ta yadda ba kowa ne zai iya gani ba amma masu fallasa, ‘yan jarida da ma wasu majiyoyi na iya gani har ma su yi ma’amala da juna. Wannan tsarin na iya taimakawa kafofin yada labarai, kungiyoyin masu rajin kare hakkin dana dam, hukumomin gwamnati da manyan kamfanoni. Yana karkashin jagorancin Cibiyar tabbatar da gaskiya da kare hakkin bil adama na Hermes da ke Milan. GlobaLeaks na bayar da kayayykin aikin na software domin tallafawa ayyukan fallasa.

Kayan aiki na masu fallasa (Tools for Whistleblowers)
Michael Wereschagin dan jarida mai zaman kan shi wanda ke bincike kuma mawallafi daga birnin Pittsburgh a jihar Pennsylvania ne ya hada wannan. Wereschagin ya jera sunayen irin tsare-tsaren da kafofin yada labarai da ‘yan jarida masu zaman kansu ke amfani da su.

Kungiyoyi a jere ta sunayen kasashe (Organisations by Country)

Kungiyoyin da ke kasa sun kunshi kungiyoyi masu zaman kansu wadanda ke tallafawa masu fallasa suna kuma samar musu da damammakin yin hakan. Gaba daya, ba mu sanya ma’akatan shari’an da ke ayyukan fallasa ba ko manyan kamfanonin da ke bayar da software, ko da shi ke wasu daga cikin shafukansu na yanar gizo na da bayanai masu mahimmanci. Muna maraba da shawarwari, ku tuntube mu a adireshinmu na hello@gijn.org

Africa

Baki daya (General)

AfriLeaks na karkashin jagorancin hadakar kafafen yada labaran Afirkan da ke amfani da wata amintacciyar hanyarsamun bayanai na dropbox. Mutane na iya tura sakonni sa’annan su zabi mambar kungiyar da suke so ta gudanat da binciken. Wannan shirin hadin gwiwa ne tsakanin Kawancen Cibiyoyin Bincike na aikin Jarida a Afirka da Cibiyar Tabbatar da Gaskiya da Kare Hakkin Dan Adam a Yanar Gizo na Hermes.

Dandalin kare masu fallasa a Afirka (Platform to Protect Whistleblowers in Africa) – wanda ke birnin Paris kungiya ce mai bayar da shawarwari da taimako a fannin shari’a, wadda a shekarar 2020 ta baiwa wata hadakar kungiyoyin kasa da kasa na ‘yan jarida masu bincike bayanan da suka kasance tushen binciken da aka kaddamar kan Isabel dos Santos, biloniyar nan wadda mahaifinta shi ne tsohon shugaban kasar Angola.

Afirka ta Kudu (South Africa)

Cibiyar shawarwari ta dimokiradiyya mai gaskiya (Open Democracy Advice Center) burinta ita ce inganta dimokiradiyya mai gaskiya, da renon al’adar sanya ido kan manyan kamfanoni da gwamnatoci, ta kuma illimantar da ‘yan kasa kan hakkin dan adam. Cibiyar na inganta nuna gaskiya, da damar samun bayanai kuma yana tallafawa masu fallasa.

Turai (Europe/Eurasia)

Baki daya (General)

Cibiyar kare hakkin masu fallasa na tarayyar Turai mai ofishi a Berlin, ta na taimakawa masu fallasa kuma ita ma tana taimakawa da manufofi da shari’a. A bazarar 2019 ta wallafa kasidarta na farko wanda ke fitowa kwane wata uku.

Hadin gwiwar kasashen yankin kudu maso gabashin Turai dan kare masu fallasa (The Southeast Europe Coalition on Whistleblower Protection) Hadaka ce ta kungiyoyi daga kasashe 12

FishyLeaks – shi ma shafi ne na samun bayanai da wata kungiya mai suna Our Fish ta kirkiro yayin da ta ke gangamin na wayar da kan jama’a dangane da yawan kamun kifin da ake yi a teku, wanda kasancewa barazana ga muhalli. FishyLeaks na samun tallafi daga Funding Fish ko gidauniyar kifaye da burin samun jama’an da za su rika kawo musu rahotannin haramtattun abubuwan da suka gani a ruwayen Turai.

Albaniya

Cibiyar Nazarin Dimokiradiyya da Mulki (The center for the Study of Democracy and Governance) Ya wallafa littafin shawarwari wa masu fallasa wadanda ke fallasa a Albaniya

Austria

Fallasa a kasar Austriya (Whistleblowing in Austria) an kirkiro ta ne a 2011 a matsayin kungiyar da za ta taimaka wa ‘yan kasa su dauki matakin bayyana zalunci da rashin gaskiya.

Faransa (France)

Transparency International Faransa na da shafin da ke taimakwa masu fallasa wajen tsegunta batutuwan da suka shafi cin hanci da rashawa

La Maison des Lanceurs d’Alerte kungiya ce ta Faransa wadda ke bayar da taimako a fannin shari’a, lafiyar kwakwalwa da kafofin yada labarai da ma tallafin kudi wa masu fallasar da ke bukata. Ta na kuma bayar da irin abubuwan da ake bukata a yanar gizo kamar su lambobin tuntuba, shawarwari da bayanai dangane da shari’a.

Jamus (Germany)

Hadakar Kungiyoyin masu fallasa (Whistleblower Network) Mambobin kungiyar ‘yan sa-kai ne, ‘yan jarida da masu fallasar suka kirkiro kungiyar a shekarar 2006. Kungiyar na bayar da shawarwari sa’annan yana aiki da masu fallasa, masu bincike da ‘yan jarida a lokacin da ya dace. Shafin dandali ne na bayanai dangane da masu fallasa. A kowace rana akwai labarai na taskar blog da ke dauke da halin da ake ciki ko inda aka kwana a batun na fallasa.

Hungary

K Monitor mai sanya ido kan kudaden al’umma (K Monitor Watchdog for Public Funds) an kafa shi a shekarar 2007 a matsayin wata hanya na sanya batutuwan da suka shafi matsalar cin hanci da rashawa a kasar Hungary da ma kasa da kasa a cikin labarai. Kungiyar na kokarin wanzar da ra’ayin samar da bayanan da al’umma ke bukata ta yin amfani da bincike mai zurfi a aikin jarida, kuma shafin yana da database inda ‘yan jarida da ma masu fallasa za su iya samun bayanan da suke bukata.

Ireland

Creative Commons photo c / o Ollie Brown, Flickr

Transparency International Ireland
A shekarar 2004 aka kafa ta kuma tana aiki ne ta tabbatar cewa an bi ma kowa hakkin shi, ko da mutun ya kasasnce a bangaren gwamnati ko na ‘yan kasuwa masu zaman kansu. Burinta shi ne a samar ma jama’a hanyoyin dogaro-da-kai ta amfani da illimi, da bayanai da kuma bincike. Littafin ta mai suna Speak Up Safely Guide (sauke a nan) na da burin taimakawa ma’aikata a Ireland su fahimci dokokin fallasa a kasar Ireland.

Italiya (Italy)

IrpiLeaks dandalin fallasar kungiyar IRPI, wato cibiyar bincike a aikin jarida na Italiya. Ta fi mayar da hankali kan bayanan kungiyoyin mafia a Burtaniya

Holland (The Netherlands)

Gidan masu fallasa (House of Whistleblowers) na bayar da shawarwari ta tallafi wajen lura da lafiyan kwakwalwa da yanayin zamantakewa, ta na kuma gudanar da bincike kan yadda ake kula da lafiyar masu fallasar da kuma cin zarafin da sukan fiskanta a al’umma. Haka nan kuma, tana taimakwa wajen kare su daga yanayin da zai sa bata musu mutuncin su, sa’annan tana bayar da bayanai dangane da masu fallasan.

PubLeaks Shafi ne mai kwakwarar tsaro wanda ke samun goyon bayan kafofin yada labaran Holland fiye da 40. A shekarar 2013 aka kafa ta yin amfani da fasahar software na GlobaLeaks wanda cibiyar Hermes ta sarrafa.

Poland

Gidauniyar Stefan Batory (Stefan Batory Foundation) gidauniya ce mai zaman kanta a Poland wadda aka samar a 1988 da burin samar da al’umma mai gaskiya, mai samun bayanai kuma mai bin turbar dimokiradiyya.

Rasha (Russia)

Transparency International Russia, an kafa shi a 1999 kuma yana tattara kungiyoyin fararen hula har da kafofin yada labarai su yi yaki da cin hanci da rashawa su kuma yi aiki wajen halatta ka’idojin gaskiya da ci-gaba a fannonin gwamnati da na ‘Yan kasuwa masu zaman kansu.

Serbiya (Serbia)

Pistaljka ko kuma “usur” da harshen serbiyanci, na gudanar da bincike, kuma yana da shafin da ke karbar bayanai daga masu fallasa sa’annan su taimaka musu da batutuwan da suka shafi shari’a.

Spain

XNET ta na fafutukar ganin cewa masu fallasa sun sami kariya. Kuma ta na da wani tsarin da ke kula da masu fallasar da ta ajiye a boye ta yin amfani da fasaha mai sarkakiya na encryption.

Ukraine

Initiative 11 gamayya ce ta kungiyoyin fararen hulan da ke fafutukar tabbarar da kariya wa masu fallasa a Ukraine.

Burtaniya (United Kingdom)

Kariya, (wadda a baya aka san ta da Aikin Damuwar Jama’a) (Protect, formerly known as Public Concern at Work) an fara kungiyar a 1993 kuma burin ta shi ne ta tabbatar aikin fallasa ya dore saboda a kauce wa hadurruka da ke barazana dagula al’umma, kuma ko da ba’a kai ga cimma wannan buri ba, akalla a dago miyagun abubuwan kafin su yi lahani. PCW na da layin kyauta inda take bayar da shawarwari, kuma tana tallafawa kungiyoyin da ke aiki irin na ta. Ta na gudanar da ayyukan da suka shafi manufofin ci-gaba da illimantar da al’umma.

The Whistler: Hadaka ce da ta kawo kungiyoyin Campassion and Care (Tausayi da kulawa) da (Cibiyar bincike a aikin jarida) Centre for Investigative Journalism the nufin kare duk wadanda suke aikin fallasa gaskiya ba tare da la’akati da banbancin kabila, addini ko manufoi na siyasa ba. Masu aikin fallasan ne suka hada, domin kansu da sauran ‘yan uwansu masu fallasan kuma suna taimaka musu da kwararru da shawarwari da kuma taimako a fanin shari’a, da kudi.

Kudancin Amirka da yankin Carribbean (Latin America/Carribbean)

Guatemala

Accion Ciudadana: A shekarar 1996 aka kafa ta kuma daga shekarar 2006 ta fara kasancewa daya daga cikin rassan kungiyar Tranparency International. Kungiyar fararen hula ne da ke aiki da kungiyoyin Transparency da Integrity a Guatemala.

Mexico

MexicoLeaks dandali ne da ke samun goyon bayan kungiyoyin Mexico guda takwas wadanda suka hada da Animal Politico, emeequis, Másde131, Periodistas de a Pie, Poder, Proceso, R3D, da Arestegui Noticias.

Yankin Arewacin Amirka (North America)

Yaki da cin hanci da rashawa da sa ido, Canada (Anti-corruption and Accountability Canada) na taimkawa masu yin aikin fallasa, kuma suna bayar da shawara kyauta

Amurka

Governmant Accountability Project (GAP) kungiya mai zaman kanta ne a Washington, da ke goyon bayan aikin da masu fallasa ke yi.

Project on Government Oversight (POGO) kungiya ce mai zaman kanta wadda ke aiki da masu fallasa da ‘yan jarida da jami’an gwamnati domin su tabbatar da sauye-sauye masu kyau a gwamnati.

National Whistleblower center kungiya mai zaman kanta ne a Washington wadda ke tallafawa shirye-shiryen fadakarwa, illimi da shirye-shiryen da suka shafi fallasa.

Whistleblower Aid kungiya mai zaman kanta, wadda ke kula da harkokin shari’a kuma tana da mazaunin ta a Washington, D.C. “Muna goyon bayan duk wadanda suka bi doka suka kai karan gwamnati da manyan kamfanoni da zarar sun karya doka.”

The Whistlerblower Support Fund kungiya mai zaman kanta da ke “bayar da shawarwari da taimako a fanin aiki da kwararru, da lauyoyi. da ma’akatan zamantakewa, da masu bayar da shawara kan aikin yi ko/da ‘yan jarida, sa’annan ta na kuma taimaka ma wadanda ke aikin fallasa.

The Whistleblower Blog “Kamfanin yada labarai ne mai zaman kan shi,” wanda ke zaman gudunmawa na kyauta ga al’umma daga kamfanin Kohn, Kohn & Colapinto, LPP

The National Council of Nonprofits – Ya jera abubuwan da suka dace a sani game da manufofin aikin fallasa da ma mahimmancinsu ga kungiyoyi masu zaman kance.

ASIYA (ASIA)

IndonesiaLeaks – Yana tanadar da wurin da masu bayar da bayanan za su iya su tsegunta ba tare da kowa ya sani ba. Daga nan sai ‘yan jarida su bi sahun labarin

Republish our articles for free, online or in print, under a Creative Commons license.

Republish this article


Material from GIJN’s website is generally available for republication under a Creative Commons Attribution-NonCommercial 4.0 International license. Images usually are published under a different license, so we advise you to use alternatives or contact us regarding permission. Here are our full terms for republication. You must credit the author, link to the original story, and name GIJN as the first publisher. For any queries or to send us a courtesy republication note, write to hello@gijn.org.